ELHAJJ 5

 


🤎🤎🤎🤎

                    *ELHAJJ*

                                  🤎🤎🤎🤎


Free page 5

    

   Written by

        Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387



*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃



*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*



*LOCATION KANO*


08062073990


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


   Dago kai yai ya kallo table din da mamaki ya bude baki sai kuma ya kalli kofa ganin bai ga jarkar rubutun da Malam ya ajiye masa ba, shi dai yasan bai dauke ba kuma yana toilet bai ji alamun an bude kofa ba balle yace an shigo ma.


Da tsananin Mamaki yake dudduba office din amma bai gani ba, wannan shine karo na hudu kenan da Malam yake kawo masa rubutu yasha amma kafin yasha sai ya ne me shi ya rasa.


Lumshe ido kawai yai ya fita daga office din zuwa masallaci....


Bayan sun fito har zai wuce yaga wani kamar Baba Auwalu kamar yadda suke kiran sa bai man ce shi ba tsohon ma'aikacin sa ne da a old site yake daga baya da aka bude new site yasa sunan shi a jerin wadan da zasu dawo New site din.


Kara sa wa gun sa yai ganin yana ciki cikin mikewa da alama zame wa yayi a gun, taimaka masa yai ya mike cike da kulawa yace "Baba Auwalu kana lafia dai".


Washe baki Baba yai yace "Alhamdulillah MD, dan zame wa nai, ina wuni".


Gajeran murmushi yai yana shafa sajen sa yace "Allah ya kiyaye gaba, ai ni ya kamata na gaishe Ka Baba Auwalu".


Dariya Baba yai yace "A'a MD ai gaba kake dani a fannin aiki da matsayi, ai kamar kasan jiya yarinya ta take cewa tana so tazo ta ganka ta gaishe Ka wai in zata samu aiki ko na goge goge ne tana so tayi ita dai a biyata albashi kawai ko 5k nace bata da hankali waye zai dauke ta aiki haka".


Fuskar sa dauke da murmushi yace "in ta shirya ko yaushe zaka iya kawo ta a cikin satin nan ina neman mai share min office dina".


Dan shiru yai sai kuma yace "ina son na samu mace dama da zata na gyara min office sosai fatan dai zata iya koh".


Da Mamaki Baba yace "wai Ka dauke ta aiki knn, zata iya zuwa ko gobe ne tana fa zuwa makaranta da safe rigimar tace kawai fah".


Cikin rashin damuwa Elhajj yace "zata iya zuwa duk lokacin data tashi daga school din wannan ba damuwa, bane in tazo zamuyi magana akan albashin ta".


Baki bude Baba yake kallon sa har ya wuce, shifa fada masa kawai yai ganin ya samu damar magana da MD yau a sauwake, lallai kuwa in haka ne baxai yi Wasa da wannan damar ba ya san tabbas za'a biyata albashi mai tsoka daga nan sai ya dinga tara kudin in auren ta ya tashi ai barkan sa.


Cikin nishadi ya koma bakin aikin sa ransa fess....



*******


Dambe muke kamar me, na danne ruwan cikin Amal class mate dinmu sai naushi nake, ihu ake a kan mu ba wanda yayi kokarin zuwa ya raba mu ba yau na fara dambe ba duk Wanda yazo da niyar raba mu kansa nake koma wa.


Daka min tsaya Uncle Mustapha yai discipline teacher, da sauri na daga Amal din ina kunkuni.


Gyada kai yai yace "ku biyo ni office ynxu nan".


Duban inda Amal take nai naga sai kuka take tana gogewa da Hijab dinta, kwafa nai nayi gaba bayan na sabi jakata.


A office dinsa muka sa me sa yana zaune ga bulala nan ya ajiye akan table.


Hadiyar yawu nai cike da tsoro nace "Uncle zan fara bayanin abinda ya faru".


Bai bani amsa ba sai kallon Amal yai yace "mai ya hada ku?".


Kuka ta Kara fashewa dashi cikin kuka tace "Uncle kawai don Hajjo ta zo tana bamu labari cewa yau Maman Dije ce ta mata wanka sbd tsabar kazantar ta shine ta kama ni ta ke duka kuma bayan bani kadai bace nake tsokanar ta muna da yawa".


Da sauri nace "Uncle karya take wallahi, ita ce nan har Kida take min wai ga Dije kazamiya ni kuwa naga baxan dauki iskancin banxa ba nace wace kazamiyar ta kalli idona tace ke Dije shine nake kilar ta fah"


Kallon mu Uncle yai yace dukan ku kuna da laifi, "ke Amal bai kamata ki dinga kiran ta da kazama ba sannan ba ruwanki ko Maman tace ke mata wanka kullum ai mahaifiyar tace koh?".


Daga kai Amal tai tana kuka don fa ta bugu ba karya.


Kallona yai yaga sai cika nake ina batsewa murmushi yai kawai yace "Khadija ban haka ki fada ba, kina mace amma baki da aiki sai fada ehe".


Turo baki nai cike da Shagwabar da nake yiwa kowa nace "Uncle tsokana ta suke yifa, ai in ba Wanda ya tsokane ni bana fada".


Murmushi yai yace "ki dinga hakuri dai kinji, ynxu ku bawa juna hakuri bana son fadan nan daga yau".


Kallon ta nai nace "kiyi hakuri fah Amal kin sanni bana daukar iskanci amma za'a kiyaye".


Dauke kan ta tai tace "kiyi hakuri kema".


Watsa hannu baya nai nace "mafi mishkila".


Murmushi Uncle Mustapha yai yace "ku tafi Maza an dade da tashi".


Fita mukai a tare sai harara ta Amal keyi ina kula da ita nai Mata banxa don bana son wani fitinar kuma ynxu na gaji yunwa nake ji.


Bayan fitar su mikewa Uncle Mustapha yai yana murmushi, shidai Allah ya zuba masa kaunar Dije a ransa tun tana ajin farko yake sonta jira yake ta shiga ajin karshe ya fada mata abinda ya dade yana jira kuma yana fatan insha Allah Dijen gala tasa ce.....


Ina isa gida abinci na fara ci ina ci ina bawa Mama labarin fadan da nai a makaranta, itadai ko kula ni batai ba sai sakar rigar sanyin da takeyi kawai.


Ina gama cin abincin na wanko hannuna na dawo daki, kayan makarantar na cire na zira Riga da skirt ban sa hula ba don bana son hula na fito Palour.


Kwanciya nai akan kujera nace "Mama ki bani tsakar na karasa Miki, naga dai rigar nan ni kike yiwa toh ki bani kawai na karasa kayata kinji".


Ganin taki min magana na tashi zaune ina turo baki, kamar zanyi kuka nace wai Mama don Allah kina ji sai na dinga magana amma ki min banxa kamar baki ji ba.


Ba tare data kalle niba tace "ah toh meye zan tsaya ina biye miki bayan maganar ba mai muhimmanci bace ba, ai da mai muhimmanci ce sai na tsaya ina saurara har na baki amsa ma".


Turo baki nai ina komawa na kwanta bana son naji ina magana amma a ki biye min kawai a share ni shiyasa nayi shiru abuna.


Ganin na daina magana kuma da alama ba bacci nai ba tace "mai kike yi ne Dije? Ko bacci kike".


Ina daga kwancen a hankali nace "na gaji ne kawai".


Murmushi Mama tai tasan fushi take shiyasa tace haka, ita dai bata sake Mata magana ba sai da akai la'asar ta tashe ta.


Yinin yau gaba daya ban zauna a tsakar gidan ba ina daki a kwance alwala ce kawai ke tayar dani.


Ina kwance bayan sallar Isha'i Baba ya shigo palourn.


Mike wa nai nace "Baba ina wuni".


Murmushi kwance a fuskar sa yana Zama a gefe na yace "lafia qalau Mamana, yau ban ganki ba kin zo mini sannu da zuwa".


Turo baki nai ina juyar da kai na gefe.


Mama dake zaune tace "fushi take wai Malam haka ai, tun dazu nima taki min magana".


Kallona Baba yai yace "mai aka yiwa Mamana ne ehh".


Tabe baki Mama tai tace "mai kuwa za'a mata Malam, shirme tazo tan fada min don na Mata banxa shine take fushi".


Murmushi Baba yai yace "toh tashi nazo miki da albishir".


Juyar da kaina nayi ina turo baki nace "tsokana ta Baba kawai kake yi".


Girgiza kai yai yace "dazu nake yiwa MD magana kince kina son aiki ko share share ne, shine yace dama yana neman wacce xata dinga gyara masa office duk lokacin da kika shirya muje tare".


Mikewa nai da sauri nace "don Allah Baba da gaske kake".


Dan hade rai yai yace "karya zan miki toh".


Ihu nasa ina rungume Mama nace "Mama na samu aikin da zan dinga samo miki kudi, kinga sai mu dinga cin kayan dadin mu koh".


Ture ni Mama tai ta kalli Baba tace "ban fahimce Kaba Malam mai kake nufi ne wai".


Gyara zama Baba yai yace "jiya take cemin ko zan nema Mata aiki a companyn da nake, toh Allah cikin ikonsa yau na samu magana da MD din companyn a saukake kuma ya dauke tama".


Da mamaki tace "ina Dijen ce zatai aiki wai a companyn da kake".


Daga kai Baba yai cikin tabbatar wa yace "insha Allah kuwa".


Hade rai sosai Mama tai tace "ban yadda ba Malam, yarinyar da take zuwa makaranta Ss 1 fa take shine za'a ce zata je tana aikin share share, baxai yi ba haba Malam Ka duba Ka gani, mai ta rasa ci ko sha?".


A Dan hasale Baba yace "toh ai ita tace tana so kuma na nema Mata, sannan da kike maganar wata makaranta ai nasan da makarantar kuma sai da na fada masa yace bakomai in ta tashi sai tana zuwa tunda tana son aikin".


Girgiza kai Mama tai tace "baxan taba yar da ba Malam, yarinyar da hankali bai wani gama shigar taba kake so ta dinga gyara wa gardi office baxai yibu wallahi".


Mikewa Baba yai a fusace yace "sai kiyi tayi kuma dama ai taimaka miki nai, in tana aikin albashin ai ya isa a dinga Tarawa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mata miji tayi aure, kinga kin samu kudin da zaki rage wasu abubuwan, amma kiyi tunani dai wannan damar in ke baxa ki yadda ba zan fadawa Umma nasan da gudu zata bar Hajjo taje".


Kuka nasa da karfi ina girgiza Mama nace "don Allah kiyi hakuri ki bar ni naje Wallahi ina so Mama".


Tsaki Mama tai ta ture ni tace "sai kiyi tayi dai amma ba inda zaki je wacce bata san ciwon kanba kawai".


Zama nai a Palourn ina dora kaina akan gwiwa ta ina kuka, Allah ya sani ina son wannan aikin kodan In an min albashi na dinga siyo wa Mama kayan dadi tana ci da kuma su Omo tunda bata Sana'ar komai, duk abinda ta fara siyarwa sai Umma ko Inna fure su fara irin Sana'ar shi yasa kawai ta daina komai....



***********


 Idonsa akan Saudat da take masa list din abubuwan da take bukata na bikin kawarta.


Lumshe ido yai a hankali ya bude bakinsa yace "uhm ina ji"


Gyara zama tai tana Kallonsa tace "yauwa Elhajj ankon guda biyu ne ba tsada sosai 300k ne kuma kaga kudin dinki da kudin veil da bag duka dai in Ka bani 500k ya isa sai gudunmawar da zan bayar 100k kaga bikin Kanwar Nabila ne fah".


Kallon ta kawai yake har ynxu yana mamakin irin kudin da take tambayar sa lokaci lokaci masu nauyi haka kuma sai tace wai ba yawa, tabe karamin bakin sa yai yace "yaushe zaki tafi Lagos din".


Murmushi tai tasan tunda yace haka ya yadda zai bata kudin in tayi sa'a ma ya kara Mata, fari tayi da idon ta tace "next week za'a fara amma in son samu ne na tafi ko Sunday ne zamuyi shirye shirye fa kasan nice babbar kawar Nabila".


Mikewa yai cikin rashin damuwa yace "xan Miki transfer din kudin gobe insha Allah, har da Wanda zakiyi booking flight din".


Cikin farin ciki tayi hugging dinsa tace "bara naje na fara hada kayana".


Bin ta yai da kallo kawai har ta sauka, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin wai zaman aure ma suke yine shida saudat, tabbas yana Jin wani abu ba dai-dai ba amma bai San ta ina zai fara ba...


Ganin in ya fara tunanin hakan zai sa mishi ciwon kai karshe ya hana shi bacci kawai ya shiga dakinsa ya kwanta bayan yayi addu'ar kwanciya bacci....



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300  KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


09066728387




Comments Nd share plz




Mrs A.M🥰

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links