SANADIN LABARINA 5


  Free Page ( 5)©®Hafsat Rano


****Duk da karancin shekarun ta amma maganar sa tayi mata zafi, kuma tsakanin sa da Allah yake maganar, kamar ya kushe halittar ta ne ko wani abu, amma kuma da ta sake kallon kanta sai taga kuma akwai kamshin gaskiya a maganar sa, tabbas tana da rama ta ban mamaki, dan ita kanta wani lokacin sai ta dinga jin kamar zata karye.


"Haka Tariq yake, yanzu akan wannan maganar asibitin ko yaje sai ya sake kira ya jaddada min, da gaske yake daukar ire-iren wadannan abubuwan musamman da ba wani saka baki ya cika yi a abu ba, amma duk abinda kuma ya damu dashi toh fa baya hakura sai ya cim masa."


Shiru tayi bata ce komai ba har Antyn ta gama bayanin da ta lura so take ta wanke shi, tashi tayi kawai ta soma gyara falon ita kuma Anty ta nufi kitchen dan sama musu dan abinda zasu ci kafin hajiyar gidan ta kirasu zuwa karin kumallo dan duk ranar girkin ta sai an sha yunwa a gidan musamman yanzu da Baba zai fita da asubah ba dashi za'a karya ba dan yace daga airport din ma wani wajen zai yi suna da meeting na majlisun su a masallaci.


***Safiyya ce kawai ta fito da zai tafi ita da Mama suka rakashi har mota, dan su Amira ce musu yayi su zauna kar wadda ta fito baya son ire-iren wadannan abubuwan, last da zai tafi suka sha kukan su yana kallon su shi abun ma mamaki ya bashi, shiyasa wannan karon yace kar su fito, har ya shiga mota ya tuna da Yaya, shi shaf ya ma manta da ita, ya kuma san idan har ya tafi be mata sallama ba ya shiga uku, dan maganar ba zata taba karewa ba ta dinga mita kenan, fitowa yayi daga motar ya nufi bangaren ta yana fatan ya sameta ta koma bacci, yana tura kofar falon ya ganta tana shirin fitowa, da sauri yayi baya ta kalle shi


"Na zata ai tafiya zakayi baka zo ba."


"Ban tafi ba." Yace


"Na zata ai nace, wajen ka nake shirin zuwa yanzu haka ma, zauna muyi magana."


Tace tana zama, kamar kar ya zauna sai kuma ya zauna


"Kana ji, nayi magana da wani malamin mu na chan kauye, yace zaa kawo maka rubutu kasha idan abun be sauki ba sai ayi maka rukiyya, bansan yau zaka tafi ba, ba wanda ya fada min sai da babanku ya dawo yake fada min, yanzu sai ku fara biyawa ku karba sai ku wuce."


"Ina?"


"Ban sani ba."


"Allah ya baki hakuri, zamu biya mu karba."


Yace ya mike


"Karka fa tafi baka karba ba, ka kira su ayapot din kace su jira ka."


"Toh, zan kira."


"Yawwa, Allah ya baka lafiya kaji."


"Amin."


Ya amsa yayi saurin ficewa, ya san rigimar Yaya shiyasa shi duk abinda tace toh yake ce mata,in ba haka ba yaushe mutumin da zai yi tafiya, a jirgi ma ba a mota ba ace wai ya kira yace a jira shi, rigimar ta yawa ne da ita shi takamaimai ba me san rashin lafiyar me yake ba da har za'a ce ya sha magani. Yana zuwa ya fada mota, Baba ya fito suka tafi.


*** Bayan tayi wanka suna zaune da Muhammad da Usman suna bata labarin ball Anty tace ta taso suje ta gaida Yaya, tashi tayi rike da hannun yaran suka fita zuwa bangaren Yayan da yake daga gefen gidan, tana dan madaidacin tsakar gidan ta, a zaune Abu na shanya mata kaya suna hira suka shigo. Da ido Yayan ta kafe Jiddan har suka karaso ta durkusa kasa ta gaishe ta, ta amsa a sake kafin ta dora


"Ina kika samo yar fillo Halima?"


"Yar gidan Yaya ce fa, Hauwa'u."


"Allah sarki, itace ta girma haka."


"Itace."


"Lallai, amma dai ya bar miki ko? Dan banga amfanin zaman zankadediyar yarinya kamar wannan a hannun makirar matar nan ba Lami."


Dariya tayi


"Eh ya bar min."  Tace a kunyace


"Kai madallah madallah, zumunci kenan, ya kyauta ke kuma Allah ya baki ikon rike ta da amana, ya baki ikon tarbiyarta."


"Amin Yaya."


"Kinga shikenan nima na samu yar daki, dan da alama zatafi zabiyoyin chan hankali. (Su Maryam)."


Dariya kawai tayi, ita kuma Jidda tana rakube a gefen tabarmar tun shigowar su, su usman suka koma. Antyn ma cewa tayi tana zuwa ta fice ta barta a wajen Yayan dan bata so tace ta taso, tana fada  Yaya zata hau sababi, shiyasa ma kawai tace mata kawai tana zuwa.


   Suna zaune Yaya na ta faman bata labari, labarin rayuwar ta da dah, wani tayi dariya wani kuma sai tayi shiru musamman idan Yayan ta baro wani zancen da bata gane ba. Cikin hirar ne ta sako maganar Tariq, ta rage murya sosai sannan tace


"Aljanu ne dashi fa, ina kyautata zaton aljanun kakansu ne suka dawo kansa, halin su daya da Maigidan nan, gashi naga alamun har so yake yafi Malam bakin hali (Mijinta)..." Sai ta dora tana sake rage murya


"Kinsan fa tsabar bakin halin Malam, duk sanda na haihu sai ya tattara ya koma dakin zaure, ko dan ba zai gani ba, har sai mun yi arba'in, idan bako ya  shigo gidan ba zai taba sanin yana nan ba, ko tarin sa ba zaki ji ba, kum bakin sa ko wari baya masa."


"Allah sarki, yanayin sa ne a haka.""Ba wani ke, bakin hali ne kawai."


Shiru tayi kawai dan bata san me kuma zata sake cewa Yayan ba,sauya labarin tayi zuwa wani daban sai ga Fauwaz ya shigo, ya kalli Yayan ya kalli Jidda sai kuma yayi murmushi


"Yaya bakuwa kikayi ne?"


"Toh baki abun magana an hallaro (wai Yaya ce take cewa wani baki abun magana)"


"Bakuwa kikayi ne Hajiya Yaya?"


"Ba bakuwa bace, kwanan ta nawa a gidan nan baku hadu ba?"


"A ah, kinsan mu idan ba abu ba, ba kasafai muke shiga cikin gidan ba."


"Toh gata nan, kanwar kace dan ta zama yar gidan nan itama, yar Yayan Halima ce."


"Toh Masha Allah, sannun ki."


"Ina wuni?" Tace tana mikewa


"Lafiya lou, kina lafiya?"


Shiru tayi tana wasa da hannun ta


"Zaka korar min ita daga zuwa, Jidda yi zamanki mu cigaba da hirar mu."


"Ah hira kuke? Jidda zauna ayi dani nima."


Sai ya zauna a wajen da ta tashi yana tankwashe kafarsa, 


"Zan je na taya Anty aiki."


"Kin jiki, yar kumamar nan dake wane aiki zaki iya?" Yaya tace tana kallon ta


Murmushi ta yi, Fauwaz yace


"Ai ba anan take ba Yaya, sai tafi yaran chan aiki."


"Tunda dama su ba uwar da suke tsinanawa ba, ayi magana ace boko, bokon banza bokon wofi."


Dariya sukayi shi da Jiddan, Yayan ta cigaba da sababi akan bokon, sai ga su sun shigo part din, Amira ce ta ja hannun Jiddan ta zaunar da ita a gefen Ya Fauwaz, maryam ta tsaya daga tsaye tace


"Tun muna daki muke jiyo maganar ki Yaya."


"Ko kice daga bangon duniya ba."


"A'ah dakin dai, kina magana ko hadiyar yawu bakya yi Yaya, ki dinga hutawa."


"Tunda ki kike ci dani kike sha dani, ai sai ki gindaya min sharadi, mutum da bakin sa an isa a hana shi magana ne."


"Allah ya huci zuciyarki gimbiya Yaya, ba abin fada bane."


Tace tana zama a kusa da Amira, suka saka Yayan a tsakiya, wani iri Jiddah take ji, musamman da bata taba experiencing irin wannan rayuwar ba, sai take jin wata nutsuwa na saukar mata, a kalla zatayi rayuwa irin wadda mutane da yawa suke yi, a kalla zata san dadin zama cikin mutane tayi gogagya dasu cikin rayuwa.

   Sun dade a wajen Yayan har sai da Mama ta aiko su zo kitchen lokacin girkin rana yayi, bata bi su kitchen din ba, ta wuce ciki ta samu Anty tana bacci ita da Usman , sai ta shige daki ta kwanta kawai tayi lamo akan gadon rayuwar ta na dawo mata daki -daki, mataki-mataki. Bata san daga nan wanne mataki zata taka ba, Amma ko ma wanne iri ne zatayi kokari wajen kula da rayuwar ta da kanta, dan ba zata so ta sake maimaita rayuwar ta, ta baya ba.

    Washegari litinin suka tashi da shirin zuwa makaranta, tun asubah kowa na gidan ya mike aka hau shirin shiryawa, tana shara Anty tace ta ajiye taje tayi wanka dan tare da ita zaa tafi makarantar, fuskarta ce ta fadada da fara'ah, tayi saurin karasa sharar yayi wanka a gurguje dadi na kamata, kaya ta tarar akan gadon da skirt underwear sai half vest da kayan da Antyn ta bayar aka dinka mata, underwears din kuma Abu ta bawa ta siyo mata a kasuwa. Dauka tayi ta saka, ta shafa mai sannan ta zura sabon Hijab din da yake gefen kayan, tamkar ba ita ba, ta sauya sosai kayan sun mata kyau yar fuskar ta fayau ta sake fitowa. Hijab din da ya kasance mint green ya karbi fatarta sosai kasancewar ta fara sosai. Tana ta kallon kanta a mudubi Anty ta shigo tace ta fito su yi breakfast,  sai ta tsaya tana kallon ta baki bude


"Masha Allah Jidda, kin yi kyau tabarakallah Masha Allah. Kin ganki kuwa? Lallai zaa yi kallon yan matacci anan."


Murmushi tayi ta sunne kanta cike da kunyar yabon da Antyn tayi mata, tabi bayanta, ta bata tea da bread anan falon ta, tana sha Amira ta leko tace ta fito, ta tashi da sauri bata gama ba ta ajiye kofin, ta saka takalmin da Antyn ta bata, tace


"Zamu tafi.."


"Toh Jidda, Allah ya bada sa'a, kiyi karatu sosai kinji? Shine gatanki."


Da kai ta amsa, ta nufi kofar ta biyo ta suka fito harabar gidan, Safiyya na tsaye rike da hannun Usman da Muhammad, ita tayi candy wannan shekarar, ta kalli Jiddan da suke fitowa tare da Amira rike da hannun juna, kauda kai tayi kawai bata ce komai ba, ta taimakawa yaran suke shiga motar, Maryam na ciki a zaune da Umaima, sai ga Fauwaz ya fito daga wajen su yana gyara hular da ya dora akan manyan kayan da ya saka, ya gaida Antyn sannan ya shiga gaba gefen me zaman banza. Zama Amira tayi bayan ta matsawa Jiddan itama ta zauna, driver da Baban ya samo musu saboda zuwa makaranta ya tada motar, suka fita daga gidan. Sai a sannan Safiyya ta gaida Antyn a gajarce ta shige ciki da sauri. Duk cikin yaran gidan Safiyya ce kawai bata sakewa da ita, ta kuma san dalilin yanayin da mahaifiyarta ta karbe ta ne, tana kokarin taya mahaifiyar ta kishi, shiyasa ma bata taba damuwa da yanayin yarinyar ba, sau tari tana ganin ta amma kallon kirki bata isheta ba bare ta samu matsayin gaisuwa. Tana shigowa falon sukayi kicibis da Mama, wadda ta cika tayi fam daga gani a cikin bacin rai take.


"Ina kwana Maman Fauwaz?"


"Bana son abinda kike min gaskiya, yanzu tsakani da Allah aure min mijin da kikayi be isheki ba, sai kin kakaba masa rike miki yar dan uwan da ya kasa rike amanar da Allah ya bashi, ba zaki duba shi nauyin da yake kansa ba na yaran sa."


"Me ya faru?" Tace kamar bata san maganar da Maman take yi ba


"Makarantar yaran nan da kika saka babansu ya kai yarinyar da kika dauko."


"Wai Jidda?"


Shiru tayi ranta idan yayi dubu ya baci


"Ayya kiyi hakuri, shi da kansa yayi niyya yace zai saka ta bani na nema ba, sannan naga ai d'a na kowa ne Maman Fauwaz, ba'a san wanda zai more shi ba."


Tana fadan haka ta shige ciki da sauri dan tasan tsaf yadda ran Maman yake a bace za'a iya yin batacciya. Bata san tashin hankali ko kadan shiyasa duk yadda taso suyi rigima taki bata kofa, idan ta fara ma sai tayi shigewarta daki ta barta.


❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯❤‍πŸ”₯


*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*


*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*


*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*


πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links