DAUDAR GORA 35

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      




  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)




            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



*_35_*



........Hadiman sashin gaba ɗaya kamshin turaren da sukaji ya sakasu tunanin Tajwar Eshaan da bai jima da shigowa ba daga fada ne ya sake fitowa. Sai kuma sukaga saɓanin haka lokacin da Iffah ke ƙarasowa cikin katafaren falon mai ɗauke da duk wani nau'in kayan more rayuwa irin na wanda suka isa. A kujerar da ko ba'a faɗaba tsarin zubinta ya isa tabbatar ma mai kallo Shahan-shan ne kawai ke zamanta ta kai zaune da bismillah a bakinta. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta harɗe fiye da salon sarauniyar Ingila tana kallonsu. Cikin rawar harshe dajin kwarjininta ya cike falon tsaf suka shiga zubewa suna gaisheta. Yatsu biyu ta ɗaga musu cike da ƙasaita batare data amsa ba dan haka kawai yanayin da ta tashi da shi taji bata buƙatar magana. Basu iya sun motsa ba har ta gama zuƙar iska da fesarwa tamkar mai lissafin kaɗawarta sannan ta dubesu, sai kuma ta maida ga tarin abincin da aka shirya yanzu akan wata lallausar darduma saɓanin na ɗazun akan teburin cin abinci. Akan farin tambulan na gilashi mai ɗauke da madara fara ƙal-ƙal ta sauke idanun nata (mafarkina ya zama gaskiya kenan ko saɓaninsa) zuciyarta ta ayyana har lokacin idanunta tsaye akan tambulan ɗin..

   Hadiman da basu fahimci ma'anar kallon da takema kayan abincinba cike da girmamawa a gareta ɗaya ke faɗin, “Ya Zawjata-almilk abincine daga saken mai babban ɗaki, an shiryashi ne matsayin liyafa gareki ke da shugaba”. A hankali Iffah ta janye idanunta daga wajen ta maida kan hadimar na tsahon wasu sakkani, acan ƙasan zuciyarta kuwa nanata sunan Malikat Haseenat take tamkar mai bitar karatun hadda. Batare da tace komai ba kuma sai ta kaɗa kanta. Shiru ya sake biyo baya kafin Iffah ta katseshi da duban hadiman da har yanzu dai ke tsaye da alama zaman jiransu sukeyi kenan, dan ta fahimci idan zaici abinci haka suke zagayesa. Kanta ta kauda da faɗin,

    “Maleek fa?”.

Kai tsaye duk suka fahimci wa take nufi, tunda dai duk sun san minene ma'anar kalmar Malik ɗin. Cikin tsantsan da kai ɗaya daga ciki ta amsa mata da “Yanzu ya shigo daga fada”. Bata amsa ba, sai ɗan jimm da tai na tunani akan ambatar fada da hadimar tayi, amma a zahiri ta basar abinta.


   

       ★Kasancewar saƙon haɗa liyafar cin abincin na Malikat Haseenat da tai akan iya shi da wadda ake kira matar tasa ya riskesa tunma kafin Iffah, dan kusan shine ma yay sanadin barowarsa fada duk da Aaminsa Miran Jasim (Aami. Kawunsa)ya buƙaci zaman tattaunawa da shi. Badan son ransa ba ya kimtsa ya fito cikin shiga mai sauƙi ta zaman gida. Kamshinsa da takun sawayensa dake tabbatar da girman ikonsa tuni ya iso a kunne da hancin Iffah dama hadiman dake zagaye da ita. Tuni hadiman duk sun zube bisa gwiwunsu kawuna a ƙasa dan kallon shugaban nasu kai tsaye haramunne garesu bisa al'adar masarautar, idanma hakan ta faru gaban Ghazi zaka iya fuskantar tsatstsauran hukunci a dalilin hakan. Akanta dake harɗe kan kujerar da bayan shi babu wani mahaluki daya iya kwatanta zama kanta ya fara sauke ƙasaittun idanunsa. Dai-dai itama ta ɗago nata sakamakon jin takun sawayensa da zubewar hadiman. Cikin ido suka kalla juna, hakan yay matuƙar tsikarar zuciyar Iffah da abinda take faman hasashe da neman tabbaci a kwanakin nan ya tabbata ɗin yau a idanunta. Dan tabbas shigar jikinsa ta yanzu ta sake tabbatar mata da waccan fuskar... Shine ya fara janye nasa kausasan idanun batare data iya tsinto komai a cikinsu ba. Kamewa da gagara fassara abinda ke kan fuskarsa kuma ya taka rawar gani wajen ɓoye ainahinsa. Sai ma kallonsa da ya maida kan ƙaton agogon dake kafe a falon cike da basarwa kai kace bai ganta bane. Ita madai basar da shi ɗin tayi kamar ma bata san da fitowar tasa ba, sai zuciyarta dake faman kai kawo a ƙirjinta cikin sauri-sauri. So take ta gaskata shi ɗinne kota ƙaryata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kan karkata akan ko ɗaya a cikinsu. Sai ma neman jefata a ruɗani takeyi......

        

    

       *_BARRISTER_*


     Duk yanda Barrister yaso sanin suwaye su? Mi kuma yay musu basu saurareshi ba suka turasa cikin jibgegiyar baƙar motarsu, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya shiga motar Barrister ɗin ya fiddo komai na ciki a cikin wata ƙatuwar jakka suka bar wajen.. Suna ɗan matsawa a wajen wani abu mai masifar ƙara ya ziyarci kunnuwan kowa. A take aka fara gudun ceton rai dan duk wanda yasan bomb yasan shine a yanzun ma.

    “Innalillahi wa inna'illaihirraji'un”. Barrister ya faɗa idonsa nabin motarsa da tai sama ta shiga dawowa pieces ƙasa alamar dai bomb ɗin daga cikinta ya tashi. Duk da ya firgita da mutanen yay jarumtar dubansu fuska a dake. “Ku su waye? Miyasa kuka aikata min haka?”.

        Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, kamarma basu jisa ba sukayi. Hakan sai ya ƙara tada hankalin Barrister, dan ya fahimci ya shiga hannun mugayen mutanen nan kenan. Yunƙurowa yayi da nufin ƙara magana suka jefa masa handkherciff a fuska, daga haka bai sake sanin inda yake ba sai buɗe idanu yay ya gansa a wani ɗaki da bai san inane ba...


      Gaba ɗaya jihar Hubab da ƙasar Ruman a rikice ake akan tashin wannan bomb, dan abune da bai taɓa faruwa da su ba. Jami'an tsaro sun iso akan lokaci, sai dai Alhamdullah ba'a samu asarar rai ko ɗaya ba daga mutanen gari, amma ana tunanin harda drivern motar al'amarin ya rutsa saboda babu wanda ya lura da sanda mutanen nan suka ƙwamushe Barrister ɗin kasancewar komai sun yisa ne cikin ƙwarewa...

      Jami'an tsaro da ƴan jarida tuni sun iso wajen akan lokaci, hakama jama'ar gari masu jarumta sun zagaye wajen domin ganema idanunsu. Babu gawar direban motar a duk iya bincike da jami'an tsaro sukayi, dan basu ga wani alamar sassan jikin mutum ba ko ɗan yatsa, hakan sai ya ɗaure musu kai dan mutanen da abun ya faru a idonsu sun tabbatar sunga lokacin da mai motar ya ajiye ta a wajen ya shiga masallaci, koda aka fito kuma mutane da yawa sun tabbatar sunga lokacin daya nufi motar wasu ma sunce har ya shiga. Wannan zance ya sake ɗaukar hankalin jama'a kowa yana faɗar albarkacin bakinsa akan al'amarin...


      Isowar wasu samari wajen kusan dai-dai da tashin bomb ɗin, kallon juna sukai da sakin dariya a tare suna tafawa. Sai da sukai mai isarsu drivern dake jan motar ya ɗauka waya. Nuni yay musu da suyi shiru. Take motar tai tsit kuwa. Ya ɗan rissina cike da girmamawa tamkar yana a gabansa ne yana kwasar gaisuwa, bai damu da a yanda aka amsa masa a daƙile ba ya cigaba da faɗin, “An rufe babinsa ranka ya daɗe”. Murmushi yayi alamar an amsasa da magana mai daɗi daga can. Sai kuma ya sauke wayar da juyawa yana kallon ƴan uwansa ya kashe musu ido. Dariya suka shiga kwasa a yanzun ma, bayan sanyi wadda suka gamsu sun wadata sannan suka fita suma suma shige cikin taron mutanen dake wajen dan jin mi'ake tattaunawa.....


    ★★★.....  MASARAUTA  ★.....


      Sai da ya kai zaune a inda aka shirya tarin abincin da kusan minti biyu sannan ta motsa itama dalilin maganar da Hadimai sukai mata. Bata musa ba ta miƙe zuwa inda yaken cikin takunta na nutsuwa da wasu ke ɗauka yanga ko makamancin hakan. Zama tai irin nasa na ƙasaita sai dai da alama ita kanta bata fahimci tayi hakan ba ma. Tsaurin idonta ya sakashi dubanta ta gefen ido batare da alamar hakan ta bayyana a yanayinsa ba. Tuni hadiman suka ƙaraso domin shirya abincin garesu. Iffah batai yunƙurin hanasu ba, dan a ganinta dole ta nutsu ta fara fahimtar yanda ake masa komai kafin ta karɓa wannan tsarin shima. Ta ɗan bi madarar da hadimar ta ɗauka, har yanzu zuciyarta na mata wasiwasi akan madarar batare data san dalili ba...

      “Bar nan”.

Ta faɗa dai-dai Hadimar na yunƙurin zuba madarar a ƙaramin cup na glass daya gama haɗuwa. Cikin mamaki hadimar ta sake risinar da kai domin girmamawa ga Iffah tana faɗin, “Ya Zawjata-almilk madara na ɗaya daga cikin abinda shugaba yafi buƙatar amfani da shi a irin wannan lokacin”.

         Kai tsaye babu ko ɗar tattare da Iffah tace, “Na yau dai bazai sha ba. A ɗaukesa anan”.

    Tsoro ne ya bayyana sosai a fuskar hadimar, gashi bata da damar ko satar kallon sashin da Tajwar ɗin yake balle ta fahimci karatun tasa fuskar. A ɗan ɗar-ɗar na rashin madafa ta ajiye tambulan ɗin a gefe ta ƙarasa aikinta. Duk da abinda ake yi a gaban Tajwar Eshaan ne, yanaji kuma yana gani. amma tsabar miskilanci da ƙarfin iko irin na masu ƙasa a hannu bai ko motsa ba balle bada wata alama akan abinda Iffah tayi ya bashi mamaki, ko ya ɗimautashi, koya birgesa, koya bashi haushi. Ko ɗaya babu mai iya tsinta a yanayinsa. Iffah ma dai bata yarda ta dubesa ba balle ta tsinta komai a tattare da shi ɗin. Sai ma wani kallon da taima hadiman ya tabbatar musu bata bukatarsu a wajen. Dan haka tuni suka ɓace tamkar ƙyaftawar ido.      

      Ya ɗan ja wasu mintuna zaune batare da ya taɓa komai ba, Iffah ta ɗan laɓe baki, acan ƙasan maƙoshi ta furta

     “Ranka ya daɗe barka da wannan lokaci”. 

   A hankali ya ɗago ya zuba mata idanunsa, a mamakinsa bashi take kalloba ma. Kuma ya tabbatar itace tai maganar ba wani ba dai. Sake tsukewar fuskarsa mai cike da gizago da motsa hanunsa dake kan spoon ya tilasta Iffah ɗan ɗagowa garesa. Sai kuma ta tsaya cak tare da ɗago birkitattun idanunta da ƙyau. Cikin nasa dake kallonta suka shige tamkar ya tsara hakan da gayya. Muƙut ta haɗiye yawu da ƙoƙarin kame rauninta dake neman bayyana a fili ta kauda kai gefe.. Shima nasan ya janye a ƙasaitance ya fara cakulal abincin kamar mai cin magani batare da ya amsa mata gaisuwar tata ba. Hakan da yay ya sosa zuciyar Iffah, dan haka ta kumbura fuska lips ɗinta suka shiga motsawa alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa...

      

       ★★.... ★....


       Tun bayan tabbatar da madarar ta shiga jerin abincin liyafar da aka shiryawa Shahan-shan da Zawjata-almilk ta kasa zaune ta kasa tsaye, bukatarta kawai taji sakamakon da take buƙata ga amintacciyar hadimarta akan lokaci. Sai dai kuma shiru kakeji wai malam yaci shirwa har lokacin da labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya iso cikin masarautar. Ba wannan ne a gabanta ba, dan haka cikin jan tsaki ta kashe television ɗin a harzuƙe. Idanunta ta sake maidawa kan agogon falon tanaji kamar tai tsalle ta ganta a sashen Tajwar Eshaan ɗin ayita ta ƙare. Dan yanzu a duniyar nan gani take bata da babban maƙiyya sama da yarinyar nan datai mugun shige mata hanci amma ta gagara fyatota ta huta a dalilin gargaɗin Uwa data kasa gane manufarsa har yanzu. Sai dai yarda da Uwa ɗin ya tilasta mata bin komai ɗin a sannu. Zata iya rantsuwa tunda ta san kanta bata taɓa cin karo da abinda ya kiɗima zuciyarta ba irin saƙon Zawjata-almilk na raye bayan ta kwana a turakar Shahan-shan kuma. Ba ita kawai ba, hatta Uwa hakan ya kiɗimata da sake tabbatar da yaƙine na gaske tsakaninsu da wannan yarinyar kenan. Dan haka batai wani magana mai tsaho da Ta-kurya ba bayan bata umarnin a isar da madarar data bata ga Iffah ta ɓace cikin tsanani ɓacin rai daya ƙara birkita dukkan tunanin Ta-kurya ɗin a yanzu har ta kasa zaune ta kasa tsaye sakamakon hakan........✍️

     

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links