SANADIN LABARINA 40


 


                  Page (40)


***Kunsan sha biyu na rana tana zaune jigum har lokacin be dawo ba, abincin da tayi masa da safe ma sai Godiya ta bawa ta kai gate wajn masu gadi, sannan ta kara musu da wanda aunty ta kawo, taci ta zubawa Godiyan ta zauna tana kallon wani American movie har dai aka gama. Mikewa tayi a saman kujerar da nufin yin bacci taji an shigo gidan, da sauri ta tashi ta leka sai taga motar shi ce, tana tsaye jikin curtains din tana jiran fitowar sa sai taga Yaya ta fito tana magana tana kallon gidan, da sauri ta bud'e kofar ta fita, tayi tsalle ta rungume Yayan tana dariya


"Yaya sannu da zuwa." Ta sake ta bayan ta tureta tana dariya 


"Bansan yaushe zaki hankali ba Jidda, karki zama kamar sauran shashasun chan mana." Tace 


"Murnar ganin ki ce fa Yaya, wallahi duk na gaji ni kadai kamar mayya a zaune."


"Aure kenan yarinya, tukunna ma, akwai ciki da goyo."


"Innalillahi Yaya."


"Toh ai gwara ki sani, wuce ki kaini ciki kin barni a tsaye haka."


"Laa na manta wallahi." Tace tana kama hannun ta


"Dole ki manta, kai kuma idan ka gama zaman motar sai ka shigo ko?"


Waigawa Jiddah tayi da sauri, yana zaune a motar ya zuro kafafun sa waje yana kallon su, kallon ta yayi daga kasa har sama haushin a yadda ta fito na tirnike shi, shiyasa yaki cewa komai dan kamar ma tunda ta fito bata ma lura dashi ba. Da sauri taja hannun Yayan suka shige ciki, gajeren tsaki yaja ya fito daga motar ya rufe yabi bayan su. Be shiryawa surutun Yaya ba, gashi ba zai iya hanata biyo shi ba da tace zata zo, so yayi ma ya kwanta ya danyi bacci kafin la'asar amma yasan honourable Yaya ba zata taba barin sa ba.

   A tsakiyar falon ya tarar dasu Yayan ta zauna tana bayanin gidan da abinda be mata ba, ita dai jidda dariya kawai take taje ta kawo mata juice da ruwa ta zuba mata dan tasan minti kad'an aka kara Yayan zatayi complain. Zama yayi a daya daga cikin kujerun falon, ya bude hannunsa sosai yayi relaxing yana kallon TV


"Muje ciki Yaya, sai kin fi sakewa."


"Wa? Ni Allah ya raba ni da shiga dakin mijinki, naje nayi ubanme toh? Haram ba dani ba."


"Kai Yaya, bafa nan ba."


"Ko Ina ne ba zani ba wallahi, dakin ku zanje nayo me toh? A wanne dalilin ma? Kul naga kina kwasar mutane kina kaisu, baki ga yadda baban ku yake ba shi da yake da girma aka ma."


Turo baki tayi duk kunya ta rufe ta, ita matsalar Yaya bata shiru sai kayi niyyar mata gwanin ta sai ta gwasale ka, yana jin su be tanka ba, yayi biris kamar baya wajen sai da Yaya ta gama sababin ta sannan ya dago ya zauna sosai yana kallon Jiddan, kallon kinyi min laifi, sauke kanta k'asa tayi yace


"Yaya? Menene hukuncin mace ta dinga fita ba hijabi wajen wadanda ma Muharraman ta ba?"


"Haramun ne, babu kyau ai." 


"Good." Ya fada har lokacin idon sa na kanta,kin dagowa tayi sarai ta gane da ita yake da kuma dalilin yin maganar.


"Yo mu a zamanin mu ma ina muka isa? Kaya ne za'a yi maka su zani da riga da mayafi duk na atamfa, dinkin manya-manya haka muke sasu kuma."


"Bari na kunna miki kallo Yaya." 


Tace tana son dauke maganar, tayi saurin chanja channel din zuwa arewa24 aka ci sa'a kuwa ana favourite film din Yayan, sai ta maida hankalin ta kan kallon ta manta da batun da ake magana akai. 

  Mikewa yayi hannun sa zube a aljihun sa, yace ta kawo masa abincin sa daki ya shige ciki, kallon Yaya tayi taga itama kallon ta take, a hankali murya k'asa k'asa tace


"Sai kin koyi jan aji fa, kina kai masa ki dawo nan."


"Toh Yaya." 


"Yawwa yi maza, dan naga kanki rawa yake ke dadi miji, masu irin halin Malam baa musu irin wannan rawar kan "


Jidda na jinta ita dai tayi gaba zuwa kitchen ta hado abinda zata hado ta zo ta wuce ta shiga ciki, baya dakin ta dai ji motsin ruwa a toilet sai kawai ta ajiye masa ta fice kafin ya fito ya tsaida ta har Yaya taga ta dade. Tana komawa Yaya ta kalle ta


"A kofa kika ajiye masa abincin Hala?"


"A ah na kai har ciki."


"Amma ko sakwan biyu fa bana jin kinyi."


"Ba kince kar na dade ba."


"Eh amma ai ba ina nufin kina shiga ki fito ba."


"Hajiya Yaya, bari na koma toh."


"Ban ce ba, karo min naman nan."


"Toh." Ta kara mata ta zauna suna hira, tana fada mata yadda take so tayi bata son rawar kai, dariya kawai jiddah take dan tasan halin Yaya anjima k'adan sai ta chanja zance shiyasa ma take biye mata a duk yadda tazo.

  Bayan la'asar driver yazo daukar ta, har lokacin Tariq ko lekowa be sake ba, shiga Jidda tayi dan ta fada masa, ta same shi yana bacci, baccin la'asar da bashi da amfani, har gaban gadon ta karasa tana kallon fuskar sa, dan jim tayi a tsaye kafin ta juya da nufin barin dakin ya riko hannun ta, ta juyo da sauri still idanun sa na rufe har lokacin, 


"Mene kike kallo na." 


"Na'am? Ni?"


"Am dama Yaya ce zata tafi shine nazo zan fada maka naga kana bacci shine zan fita."


Fuzgo ta yayi ta fado kan gadon, ya gyara mata kusa dashi yana kallon fuskar ta, runtse idon ta tayi taki yarda ta bud'e, murmushi yayi ya matse mata hannun da ya rike tayi saurin bud'e idon ta, 


"Yanzu ma a hakan zaki sake fita wajen?" 


Ya rike gefen rigar jikin ta, da sauri ta girgiza kanta


"Ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri Yaya na jira na."


"Ba zaki fita ba toh." Waro ido tayi da sauri


"Dan Allah kayi hakuri, wallahi tace kar na dade."


"Ni kuma mijinki nace ba zaki fita ba, itama in banda abinda menene na zuwa gidan newly weds, idan ta gaji zata tafi gobe ba zata dawo ba."


"Na shiga uku, ka rufa min asiri dan Allah."


"I'm serious, ba in da zaki." 


"Na shiga uku, Amma..." Hannu yasa ya rufe mata bakin ta, tayi tsit tana zaro ido, shafa lips dinta ya shiga yi a hankali yana zagaya hannun sa akan dan karamin bakin nata. 


"Kina sake magana I ll kiss you."


Rufe idon ta, tayi kirjin ta na bugawa da sauri da sauri, ta rasa dalilin da yasa yake mata haka, kallon ta ya cigaba da yi bashi da niyyar  kyale ta, kuma yana sane sarai yasan shikenan sun tabo Yaya, zai so yaga yadda drama zata kare dan yau sai ta kusan kasa bacci akan hakan. Shiru ne ya biyo bayan maganar da yayi, ta dan bud'e idon ta kad'an taga ya rufo da kansa saman fuskar ta, so close da ko yaya ta sake motsawa fuskar ta zata taba tasa, juyar da kanta tayi dayan barin da nufin tayi magana


"Dan Allah..." Ai bata karasa ba ya tallafo fuskar ta da hannayen sa biyu ya juyo da fuskar ta yana hade bakin su waje daya.


Shiru shiru babu jiddah babu alamar ta, dan daga murya Yayan tayi ta kira sunan ta amma shiru, kama baki tayi cike da mamakin Jiddan, wato itama A ce tana mata kallon sum-sum ashe munafuka ce irin Tariq din, kwafa tayi ta fita fice tun a mota ta fara yiwa Isyaku da Sam mita, su dai jin ta kawai suke Isyaku yana bata hakuri ya samu suka kaita gida sannan ta kyale su. A compound din suka hadu da Fauwaz aikuwa ta fara fada masa wulakancin da Jidda da Tariq sukayi mata dan taje gidan su


"Ashe Jiddan ma munafuka ce ban sani ba? Ta koyi halin mijin nata ni zasu wulakanta?"


"Ai kema Yaya ban da abinki, ai ba'a zuwa gidan sabon aure yanzu, ba irin Malam dinki bane na zamanin dah, dan ma Ya Tariq din ne idan nine da police dog zan hada ki su rarakamin ke."


"Sai dai su raraka ubanka bani ba, bakin mugu."


"Allah kuwa, zuwa zaki ki hana mu shan soyayyar mu."


"Idan kunga dama ku cinye juna tsabar soyayya, kuma ba gidan Tariq ba ma babu wanda zai sake zuwa gidan sa a cikin ku bare ku cimin mutunci, ba dai akwai ciki da goyo ba, muna nan zaku zo har in da nake."


"Allah ma kar yasa muzo rokon abu wajen ki Yaya, wallahi dan zaki wulakanci ba dan kad'an ba."


"Zaka maimaita wannan maganar, kuma ko kafarka na sake gani a gida na sai ka gane baka da wayo."


Tayi gaba shi kuma ya cigaba da kyalkyala dariyar da yake, sosai ta shaki abinda Fauwaz din yai mata ga mamakin Jiddah, duk sai ta kasa zaune ta kasa tsaye ta dinga mita ita kadai. 


***Sakin ta yayi bayan yaji tashin motar su Yayan, juyar da fuskar ta tayi haushin kanta da kunyar Yaya na kamata, toh da wanne ido ma zata kalli Yaya yanzu? Me yasa duk abinda ya fada akanta ta kasa dake masa a duk sanda irin haka ta faru sai ta bada kai bori ya hau, daga baya kuma tazo tana jin haushin kanta. Da kunnenta taji yana cewa ita ba spec dinshi bace ba, amma kuma why? Maganganun da ya fada ranar da ya fara dawowa, da wanda ya maimaita daga baya ne suka shiga dawo mata daki -daki, mikewa tayi tana bata fuskar ta, ya bita da kallo ganin yadda ta sauya lokaci daya


"Menene?" Yace yana zuro kafafun sa ya sakko daga gadon 


"Ka bari idan ka samu spec dinka sai kayi yadda kake so,ni ba type dinka bace ba."


"Jidda?" Yace yana mikewa, sake bata fuskar ta tayi sosai dan ma kar ya samu dama akanta, 


"Me kike son cewa?" 


"Nace ni Jidda ba type dinka bace, ka samo daidai da kai ni nayi maka siranta da yawa, kuma maganar aure ba zata taba yiwuwa a tsakanin mu ba."


"Subhallah, me ya faru? Why are you saying all this?"


"Abinda kace kawai nake maimaitawa, please ka kyale ni ka samu daidai da kai."


Kallon cikin idon ta yayi, be hango komai ba sai iya gaskiyar ta akan maganar da take yi, yana tsaye ya rasa abinda zai ce dan be yi tunanin taji duk abinda yace wa Fauwaz ba, be rikice ba a zahiri sai dai a badini wani irin tsoro ne ya shige shi, ya shiga takowa zuwa in da take a tsaye, da sauri ta tura kanta ta fice daga dakin, ta nufi dakin ta ta shige ta rufe da mukulli. Tsayawa yayi a falon yana kallon kofar da ta shiga, ya dade a tsaye sai ya juya ya samu kujera ya zauna yana jiran fitowar ta.  Dama wajen goshin magriba ba ne, saboda haka yayi alwala a toilet din falon ya sake tsayawa ko zata bud'e amma har akayi kiran sallah bata bude ba, masallaci ya wuce ana idar da sallar ya sake dawowa amma still dakin a rufe yake, gashi be san ta in da zai fara yi mata knocking yace ta bud'e ba.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links