SANADIN LABARINA 39


 Page (39)


***Cikin yanayin bacin rai Baba ya rufe ta da fada, ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, sosai ran sa ya baci akan abinda Maman tayi, shiyasa ya ki bari a kira Jiddan yace kuma Tariq ya dauki matar sa su wuce gida, ya kuma kafa masa sharadin duk abinda ya faru da ita sai ya basu mamaki shida mahaifiyar sa.

   Ranta a bace yake matuka bayan ta dawo ciki dan da Tariq din ya fita bin bayan sa tayi, ta tambaye shi dalilin da zai wulakanta ta haka har ya dauki Jiddan ba tare da sanin ta ba, hakuri kawai ya bata dan be san me zai ce ba, bata sake magana ba ganin Jiddan ta nufo su, sai kawai ta koma ciki in da ta tarar da Baban na yiwa Safiyya da Umaima nasiha. Tana shiga yace su tashi su tafi Allah yayi musu albarka, sai kawai tabi bayan su, suka fito yayi kwafa yana cike da haushin Maman, dan ta kaishi makura a yau zai kuma nuna mata shi yake da iko da ita da Tariq din, ba zai tsaya ta zubar masa da girma akan son zuciyar ta ba.

   Tafiya akayi dasu kowacce a nan Abujan zata zauna, duk da bacin ran da Maman ke ciki haka ta daure har aka tafi dasu, sannan tunanin ta ya dawo kan abinda ya faru, da irin maganganun da Baban ya gaggasa mata a gaban yaran. 

    A daki suka sameta bayan sun dawo daga kai amaren, Aunty Nafi ta zauna a kubin ta, tana kallon yanayin ta


"Wai Yaya me ya faru ne? Ko duk tafiyar yaran ce?"


"Rai na ne a bace Nafi, wallahi."


"Me ya faru?"


"Kinsan wai ashe Tariq tun jiya ya dauki yarinyar nan suka wuce gidan sa?"


Zaro ido tayi


"Ba dai Jidda ba?"


"Ita, ace ya kasa fada min sai yau zanji a wajen ubansu, tsakani da Allah me Tariq yake so ya zama ne?"


"Gaskiya ba haka aka bar shi ba, Tariq din da muka sani daban wannan Tariq din daban, gaskiya an samu matsala, kema Yaya kin yi sanyi da yawa har kika bari haka ta faru, yanzu suna ina?"


"Sun tafi."


"Kika bar su kuma?"


"Ya zan? Baban su yace wallahi komai zai iya faruwa idan nace zan wani abu."


"Tab! Amma gaskiya da matsala, shikenan haka zamu zuba ido kishiya ta mallake miki babban d'a?"


"Ba zai yiwu ba ai, wallahi ba zan amince ba, duk tsoratarwa kawai yake shima, dole na tashi a tsaye."


"Gaskiya dai, ai ba zai yiwu ba."


"Menene shawararki?"


"Eh toh, tunda dai a yanzu ran Honourable ya baci sosai, zai iya aikata komai, ta karkashin kasa zamu biyo musu, tunda dai ke bakya son dan tainakon nan na wajen malamai."


"A ah bana so, wani abun dai daban."


"Yaushe Baban zai yi tafiya?"


"Jibin nan zasu tafi tare da Halima."


"Wannan karon kuma? Ah lallai kinyi sake wallahi."


"Ni duk wannan baya gaba na, ta d'ana nake."


"Toh kawai mu tura musu Salma da Amira gidan, tunda dama hutu suke dukkansu, sauran aikin sai mu barwa Salma tasan me zatayi duk zan dora ta akan komai."


"Kina ganin hakan zai yi? Amira fa bata da aminiya irin ta."


"Duk wannan ba matsala bace ai, ke dai ki bar komai a hannu na."


"Shikenan, dan Allah ayi duk yadda za'a yi, kafin ma a samu matsala wani abu ya shiga tsakanin su, yazo shima ya tattara ya tafi dan inaga a karshen satin nan zai koma Canada, dan naji Baban yana maganar suna ta masa mail ya ma kara sati,."


"Toh kinga in da aikin ki zai shigo, ki masa lamfo-lamfo ki nuna masa komai ya wuce zaki kula da ita ko baya nan, daga nan ita kuma sai mu nuna mata shege."


"Shikenan zan daure, yanzu ke yaushe zaki koma?"


"Ai ban ga ta tafiya ba, sai naga yadda aka yi, ba a barki ke kadai ba, amfanin dan uwan kenan."


"Toh kar mu bar Mimi taji maganar nan, zata bata komai."


"Wa?* Ta kama bakinta


"Ba zata ji komai ba, uwar iyayi sai ta hau fada mana magaana, kyaleta kice wani taro zan rakaki."


"Shikenan, Nagode sosai, sai kuyi magana da Salman, shi kuma Tariq din nasan yadda zan masa, Dan ba karamin aikin sa bane suna zuwa ya koro su wallahi."


"Zai aikata, musamman yanzu da baya ganin kowa sai figaggiiyar yarinyar nan, me zubin yunwa."


"Wallahi ko ganin ta kusa dashi bana son yi, dan dai yaran yanzu ne, baka isa dasu ba."


"Ba a hayyacin sa yake bane aj."


"Toh Allah yasa ya dawo hayyacin nasa, kar a samu matsala kiji ana amai an samu juna biyu."


"In sha Allah hakan ba zata faru ba, ina Allah ma ya kiyaye."


"Toh Amin." Tace a sanyaye



***Tunda suka dauki hanyar babu wanda yace uffan, shi gaba daya hankalin sa na kan abinda ya faru da yake ta gudu tsakanin iyayen sa, gashi be san yadda Mama zata dauki abinda ya farun ba, gashi shi kansa be san dalilin da yasa ya kafe ba har yake ganin Baban yafi ta gaskiya. Be so hakan ta faru ba, yafi so duk su fahimci juna tunda an riga an daura auren. Yana parking ya fice daga motar be ko kalli in da take ba, a hankalin ta bud'e kofar ta fito, jikin ta da yayi matukar yin sanyi taja zuwa cikin gidan tana ayyana abinda ya sashi a cikin yanayin da yake ciki. A tunanin ta zata ganshi a falo, sai taga wayam alamun ya shige ciki, mayafin jikinta, ta ajiye a saman kujerar ta nufi kitchen tana kallon hanyar dakin nasa, ta leka store taga an kawo musu kusan komai an lode, kayan abinci na ban mamaki dan kar tayi karya da sai tace babu ce kawai babu a ciki. Wucewa still idon ta na kan bedroom din nasa, ta bud'e nata ta shiga, ta ajiye komai a mazaunin sa sannan ta sauya kayan jikin ta zuwa riga 3 quarter da dogon wando wanda ya dan tsuke daga sama ya bud'e daga kasa, headband ta dora akan ta fito zuwa kitchen dan sama musu abinda zasu ci, tayi kuma amfani da damar wajen zuwa ta gano halin da yake ciki dan ko motsin sa babu.

    Dankali ta dauko ta feraye ta soya ta hada da fresh chopped tomatoes, peppers, carrot da onions, tayi mixing tayi seasoning nasa sannan ta dama masa oat dan taga alamun yana so sosai. A tray ta dora komai ta nufi dakin nasa, har taje kofar zata yi knocking sai tayi wani tunani, fasawa tayi ta wuce nata dakin ta ajiye tray din a gefe ta dauki turare ta feshe jikin ta dashi sannan ta yafa matsakaicin mayafi a kan kayan jikin ta, sannan ta dauki tray din ta nufi dakin nasa. 

   Yana zaune akan sofa be cire ko takalmin dake kafarsa ba, gaba daya tunanin sa ya kare ya rasa me yakamata yayi, wa kuma ya kamata dole yayi wa biyayya ya farantawa a cikin su, kowanne a cikin su idan yayi masa ya bar daya be kyauta ba, zai kuma saka kansa a matsala ne, gefe daya kuma baya jin zai iya rabuwa da ita kamar yadda Maman take da bukata ba, sosai yake jin ta a ilahirin gaba daya zuciyar da ruhin sa, kamar idan ya rasa ta yayi wani babban rashi me girma a cikin rayuwar sa, sai yake jin kamar ta dade da shiga rayuwar tasa sani ne be yi ba sai yanzu. 

   Idanun sa akan kofar sanda ta kwankwasa, ya kasa motsawa ballantana ya bud'e baki yace a shigo, sake knocking din tayi a hankali kaamar me tsoron taba kofar, cikin muryar sa da ta shige chan ciki yace


"Shigo."


A hankali ta murda handle din sannan ta turo kofar ta shigo rike da tray din, idanun su suka sarke waje daya, ita tayi saurin janye nata dan hango wani irin abu kwance a cikin kwayar idon nasa, wadda ta kasa fassara yaren da yake kwance a cikin ta. A gabansa ta durkusa ta ajiye abun hannun ta, sannan ta mike zata juya yayi saurin riko hannun ta.


"Ina zaki?" Yace yana mata kallon k'asa-k'asa


"Kitchen, na manta ruwa da lemo."


"Akwai ruwa a wannan fridge din."


"Toh juice din fa?"


"Bana bukata, sai dai idan zakiyi wani abun."


"Eh zanyi." 


Tace da sauri, cikata yayi ya zamo kasa gaban tray din, ya bud'e plate din ita kuma ta juya ta bar dakin da tunanin ko zai dakatar da ita, amma sai taji be ce mata komai ba. Falon ta koma ta dinga zagaye haka kawai ta rasa me zatayi, daga karshe ta hakura ta wuce dakin ta, idon ta akan nasa dakin. 

   Sai da ya gama cin dankalin da yayi masa dadi sosai, yasha oat dinsa ya wanke bakin sa da mouth freshner me dadin kamshi kamar mint, sannan ya jawo cable din system dinsa ya jona a chargy ya shiga kan mails din da akayi masa yayi replying wanda zai iya sannan ya duba available flight na karshen satin wanda zai bi, ya dade yana dudduba abubuwan da tsare-tsaren abinda ya kamata yayi kafin ya ajiye komai yaje yayi alwala yayi shafa'i da wutri, sannan ya cire kayan jikin sa ya rage dashi shi sai boxer da farar singlet ya nufi dakin nata. Rashin ganin haske a dakin ya sa ya gane tayi bacci kenan. Time ya kalla a wayar sa yaga sha daya har da mintuna, be san ya dau lokaci haka ba. A kanta ya tsaya ya dan haska fuskar ta da hasken wayar sa, bacci take tsakanin ta da Allah, gashin kanta da yazo har kusan rabin fuskar ta, yasa hannu ya gyara mata, ya durkusa a gaban ta yana kallon yar karamar fuskar ta gaba daya, so yake ya dan ja baya kad'an har ya samu amsar abinda yake so ya samu, ya kuma samu hanyar da Mama zata yarda ta amince da bukatar sa, baya so ya sabar mata da kanshi azo a samu matsala shiyasa yake son ya bi abun daki-daki. Saman kanta yayi kissing sannan ya gyara mata pillow da ke kanta a hankali yadda ba zai tashi ta ba, sannan ya mike ya fita daga dakin ya ja mata kofar.

   Da safe ta farka a tunanin ta zata ganshi a dakin, sai taga babu alamun ya shigo dakin ma kwata-kwata, tashi tayi jiki a sanyaye tayi abinda zatayi ta fito falon, tana fitowa yana shigowa sanye da kayan motsa jiki ya hada zufa sosai, damtsen hannun sa ta kalla tayi saurin dauke idonta, murmushi yayi k'adan ya zo saitin ta ya wuce ta gefen ta, ya shige ciki. Ajiyar zuciya ta sauke ta matsa tsakiyar falon tana duba abinda ya kamata ta sauya masa wajen zama, duk da babu datti ko kad'an amma sai da ta kara gyaran falon sannan ta shiga kitchen din.

   Toilet ya wuce kai tsaye yayi wanka ya fito yana goge jikin sa wayarsa tayi kara,ya sa hannu ya dauka ganin sunan Mama ya saka gaban sa faduwa, tattaro jarumtar sa yayi sannan ya daga.


"Ina kwana Mama?" Yace bayan ya amsa sallamar ta


"Lafiya lou, kun tashi lafiya?"


"Alhamdulillah."


 Yace mamakin tambayar na kama shi 

  

"Toh Yayi, yaushe zaka fito?"


"Anjima k'adan da nayi breakfast Mama."


"Toh ka zo inason ganin ka."


"Toh in sha Allah..." 


"Madallah..."


"Mamma abinda ya faru jiya...?


"A bar wannan magaanar, ya wuce kawai, ka cigaba da shirye-shiryen tafiyar taka, Allah ya taimaka ya bada sa'a "


"Amin Mama." 


Yace muryar sa na bayyanar da tsantsar farin cikin da ya shiga. A gaggauce ya karasa shiryawa, be tsaya ko abinci yaci ba ya tafi. Tana kitchen taji fitar mota daga gidan, ta fito da sauri amma tuni ya bar gidan shi da Faisal. Wani iri taji ta tsaya rike da spatula tana jujjuya abinda yake faruwa a kanta.


"Ko dai ya gama deciding rabuwa da itan ne?" Ta tambayi kanta,  tunda dama ya fada ba sau daya ba sau biyu ba, ita ba spec dinshi bace ba, yanayin yadda ya d'an sakar mata shiyasa har ta fara samun hope, amma kuma idan ta tuna wasu mazan players ne na karshe, kuma zasu iya komai sai taji duk an dauke mata karsashin ta. 

   A kasalance ta gama abinda take a kitchen din wanda take yi don shi yayi tafiyar sa ba ko sallama, juye komai tayi akan dinning ta wuce daki bayan tasha ruwan tea kad'an. 

    Missed calls din aunty ta gani da ta koma dakin, ta kira ta bayan sun gaisa tace ta aiko Sam ya kawo musu abinci, tayi godiya suka ajiye wayar ta kwanta tana sake-sake a ranta har dai lokaci ya dan ja, sannan ta tashi tayi wanka ta saka wani silky material ta dan gyara fuskar ta da powder da eye liner sai lipstick ta dawo falon ta zauna tana kunna TV. Knocking akayi ta mike ta bud'e, yarinya ce ba zata wuce shekara goma ba, rike da flask sai wani babban basket a ajiye a gefenta,basket din Jidda ta dauka suka shiga ciki tana mata kallon rashin sani


"Ya sunan ki?" Tace bayan ta karbi kayan hannun ta, ta ajiye a saman dinning


"Godiya."


"Sunanki kenan Godiya?"


"Eh."


"Ok..." Tace tana gid'a kanta, 


"Tace ki kirata wai."


"Aunty?"


"Eh." 


"Ok."


Ta dau wayar ta kira Aunty, wai ashe sabuwar me aiki aka kawo mata, tunda Aunty taji Tariq din ma tafiya zai a karshn satin shine ta samo mata me aiki daga kauyen Abujan, ita Jiddan ma bata san tafiya zai ba, godiya tayi wa Auntyn tace yarinyar ta taso, ta zagaya da ita ta kitchen daga gefe kafin bq akwai daki da toilet a ciki, dakin yana da kofa ta cikin falon farko amma ginin kitchen ya dan boye ta,ta nuna mata a matsayin dakin ta.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links