DAUDAR GORA 9


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      



  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)




            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



*_9_*



...........Kasancewar wajene daba kowa ke shiga ba anyhow yasa sai da Iffah tai kiran Sir Fawzan bayan saukarta a bakin gate. Umarnin bama security ɗin wajen wayar ya bata. Bayan yayi magana da security ɗin suka bata damar shigewa batare data san miya faɗa musu ba. Tafiya take a nutse tana ɗan kallon wajen da tsarinsa. Dan babban garden ne mai cike da ababen kallo da ni'imtattun korayen ciyayi da ƙawatatun filawoyi. Ta taɓa shiga sau biyu a dalilin taron makarantarsu ta Islamiyya da aka gudanar a wajen. Ya riga ya faɗa mata inda zata samesa, dan haka kanta tsaye take nufar wajen ranta fes da nishaɗi tamkar ance mata ga wuƙa ga maƙoshin Tajwar Eshaan ta yanka.

      Sai da taje kusan ƙarshen garden ɗin ta tsaya, sai kuma ta shiga canki in canka na number wajen daya bata kasancewar akwai rukuni-rukuni na ɓoyayyun wajen hutawa da manyan mutane sukafi tu'ammali da su idan basa buƙatar wata hayaniya. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta nufi na farkon da zuciyarta tafi karkata. Ƙawatuwar wajen takai mai kallo shagala harya iya manta abinda ya kawoshi, kamshin firanni da wani iska mai busawa a hankali kaɗai na dabanne. Jitai kamar da shakku na shigowarta wajen, amma sai ta dannesa a ƙasan zuciya ta cigaba da takawa tamkar mai sanɗa tana leƙe-leƙe. Ta isa kusan tsakkiya zuciyarta ta shiga gargaɗinta ganin babu alamar akwai mutum mai numfashi a wajen, cak ta tsaya tare da ciro wayarta domin neman sir Fawzan.

      “Ya ALLAHU”.

   Ta faɗa jin ana sanar mata bata da kati kona sisi a wayar. Kamar zatai kuka ta sauketa daga kunenta tana ɗan ƙara danne-danne da cigaba da takawa a hankali batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wani lallausan jan darduma daya haɗu da kalar korayen ciyayi ya bada ƙyaƙyƙyawan tsari ta sauke. Rabin jikinsa akan tum-tum yake. Kansa a risine yana kallon lap-top ƙirar kamfanin apple dake akan wani ƙaramin tum-tum ɗin itama. Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran, sai butar shayi kalar golden akan tray dake tabbatar da set ne dan harda ƙananun cups nashan shayi. Sanye yake da ƙananun kaya farare tas da suka fidda ainahin suffarsa ta masu ta'amalli da ƙarafuna, gashi sun sake fidda ainahin hasken fatarsa da sheƙinta irin na masu jin daɗi. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba.        

       “Mi kake buƙata?”.

   Sassaanyar muryarsa mai zurfi da kamewa ta daki kunenta da alamar akwai wanda yay tsammani ba ita ba. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba'a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago lulu idanunsa masu haske da baiwar bakin ƙwayar tsakkiyarsu ya sauke a kanta. Komai tsayawa yay daga garesa, kamar yanda Iffah ma hatta kaɗawar iskar wajen ta tsaya mata cak... Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu da gayya.

      A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Iffah ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen idanunta da tun a kallon farko ta kaudasu da ga kansa alamar kunya irin ta mace, “Idan ma kai aljanine wlhy nafi ƙarfinka. Wace irin jaraba ce duk inda nai saina ganka”. Ta ƙare maganar da hura bakinta.

          Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu. A zuciyar Iffah fa ta fara tsorata dajin tabbacin mutumin nan fa ƙila aljani ne. Amma sai taga idan ta nuna tsoronsa fa zai ma iya kasheta, saboda a yanzu haka ma ƙarfin hali take, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini. Amma sai ta dake a ƙasan ranta tana karanto addu'ar neman tsari da aljanu.

      Kusan tunani iri ɗaya ne a zukatansu. Dan shima dai zuciyarsa ta ƙara yarda wannan abar aljana ce kawai, yana ganin kuma ya kamata yasan miyasa take bibiyarsa ne?. Nisan data fara masa a idonsa ya fahimci tabar wajen, ilai kuwa can ya hangota tana tafiya cikin sassarfa ta nufi ƙofa. Cin karo data kusan yi da mutum ya sata ja gefe da sauri. Ɗaya daga cikin matasan datai masa gani biyu da su ne, cikin nuna alamar mamaki da tsuke fuska yake kallonta. Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba'a kansu take takun ba.....

      “Fareedah!”.

  Da sauri ta juyo jin muryar Sir Fawzan daya sauke numfashi da dafe kansa na tabbacin ya jima yana nemanta. “Ina kika shigane wai? Tun ɗazun sai faman zagaye garden ɗin nan nake ni da securitys nemanki, ga wayarki ma taƙi shiga sam”. Maimakon ta bashi amsa sai ta zube a kujerar dake a kusa da ita ragwaf. A wahale tace “Sir ka bani ruwa nasha Please”.

       Sosai yanayinta ya sake neman firgitashi, amma fahimtar ruwan tafi buƙata ba tambaya ba ya sashi barin wajen da ɗan hanzari. Mintuna ƙalilan ya dawo da robar ruwa. Miƙa mata yay bayan ya ɓalle murfin. Tunda ta kafa kai bata koja numfashi ba sai da ta sha fin rabi, ta sauke robar tare da dafe goshinta tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Lokaci ya bata sosai ta samu nutsuwa kafin ya kai zaune a kujerar dake facing ɗinta.

      “Fareedah miya faru wai? Ina kika shiga? Duk kin tadamin hankali saboda security sun tabbatar min kin shigo”.

  A hankali ta ɗago manyan idanunta da launin farinsu ya sirka ta zuba masa. Sai kuma ta janye da sauri tana girgiza kanta dan fuskar mutumin nan kawai ta gani a tare da shi saboda ta sakama ranta aljani ne. Idanunta rumtse tare da yakice tunanin ta sake buɗesu akansa. “Sir lokaci ya ƙure ina abokin naka?”.

         Ya fahimci bata son bashi amsa, sai kawai ya girgiza mata kai. “Rashin ganinki ya sakani a ruɗanin da har ya kira waya ban sani ba, sai daga baya na lura na kirashi shima kuma bai ɗaga ba”.

    “Ya ALLAH, shike nan itama wannan damar ta kufce min!”.

            “Bazamuce haka ba sai munji ta bakinsa, a yau ne dai kawai nake ganin bazai yuwu ba gaskiya, kodan ke a karan kanki ma. Kinga saura baifi mintuna arba'in ayi magrib ba. Kije gida, insha ALLAHU zanbi duk hanyar data dace domin ganin kin haɗu da shi”.

       Kallonsa take kamar zatai kuka. Sai dai saka zantukansa a ma'aunin hankali ya sata kasa cewa komai. 

    “Kiyi haƙuri”.

Ya faɗa cikin sake sanyaya murya yana mata wani lallausan kallo. Kauda nata idon tai daga kansa, taja iska ta fesar da jinjina masa kanta kawai. Dan ta tabbatar inhar tai magana kuka ne zai iya ƙwace mata ma.....


  

      *_MASARAUTA_*


   Gurfane take a gaban Uwa kamar yanda dokar take ga duk wanda ke binta. Duk da matsayinta da girmanta a cikin daular ruman a gaban uwa ita ba komai bace face mai neman biyan buƙata (Wa'iyazubillah). Kamar ko yaushe tsohuwar da suke kira uwa sanye take cikin jajayen kaya, sai dai saɓanin waccan ranar yau inuwarta kawai ake iya gani a jikin bangon ɗakin. Amma abin mamaki babu tsoro ko wata shakkar hakan a idanun hamshaƙiyar matar. Inuwar uwa ta kece da mumunar dariyarta mara daɗin saurare, kai kace za'a iya jinta a duk faɗin masarautar, sai dai abin mamaki iya ita ɗin kawai take jinta. Sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tamkar ba'ita tayin ba.

      “Ta-ƙurya alƙawarina ya cika, zaku iya tunkarar kowa a yanzu da maganar auren Malik-alMuluk babu mai musa miki hatta Malikat da shi a karan kansa balle duk wani mai faɗa masa yaji. Sai dai akwai banbanci a wannan karon da baya. Hhhhhhhh!!”.

     “Umarninki shine abin jira Uwa mai share kukan mai kuka”.

   “Hhhhh Ta-ƙurya shiyyasa bana baƙin cikin taimakonki, zan kuma cigaba da taimakonki kiyita na sara keda duk mabiyanki. Ragamar kasancewar gida a hanun wasunki bashine zai sa su zama masu ƙarfin ikoba sama da naki. Ki shiga ki fita a haɗa gagarumin aure na bajinta tsakanin wannan yarinya da Malik-alMuluk. Hakan zaisa su shagaltu da tunanin komai ya canja musamman shafe watanni tara da Zawjata-almilki da suka rage suka kwashe gidan nan batare da ko ciwon kai ba. Ina son ki nuna bajinta irin wadda ko Malikat bazata yiba, Daular ruman zata cigaba da kasancewa a tafin hanunki a baɗini koda a zahiri kinada wanda suke nuna sunfi ƙarfinki. Ranar mako zata zama ranar sa'a Hhhhhhhh!!!”.

      Sautin dariyar ya cigaba da nesa da kunuwanta har inuwar uwa ta ɓace. Nannauyan numfashi ta sauke tare da murmushi mai nuna tsantsar farin ciki. Ta dubi ƙyaƙyƙyawan farin tafin hanunta da jini keta kaikawo tana sake maimaita kasantuwar daular ruman a tafin hanunta da uwa ta ambata mata. Tabbas ita ɗin mai sa'a ce, sa'ar da zata iya nunata a gaban duk wasu sa'ointa koma wanda suka ɗarata. Fatanta kawai ALLAH ya kaita ranar cikar burinta gaba ɗaya domin tabbatarma kowa dake cikin Ruman ma ba daular ruman kawai ba  *Saka ƙwan kaza bashi ke nufin mallakar akurki ita ɗaya ba* sannan zuwan *mai guri bashi ke tabbatarda naɗewar mai tabarma ba*.......


    ★★_______★


     Kwanaki biyu kenan Iffah bata sake neman sir Fawzan ɗinta ba, ta kuma kashe wayarta ta yanda shima koya nemeta bazai sametan ba. Ita tasan dalilin zaɓar yin hakan, duk da yanayinta ya nuna tana da damuwa dan babu walwala tattare da ita sam tun baro garden ɗin da tayi. Yau ma data kasance bazataje makaranta ba kamar yanda ta saba ta tashi taya Ummu aiki, sai dai yanda take komai kamar mara laka a jiki yasa Ummu nutsuwa a nazartar ta.. 

    “Wai lafiyarki kuwa Iffah? Tun dawowar fitar da kikai shekaran jiya duk kin wani canja. Ko jikin naki ne?”.

          “A'a Ummu, kawai dai kaina na ɗan mun ciwo ne ƙasa-ƙasa. Amma na san barci ne da bai isheni ba”.

   “Barci kuma? To miya hanaki barcin?”.

  In'ina ta fara na rashin sanin abinda zata faɗa. Sai kuma tai ƙasa da kanta ganin yanda Ummu ta kafeta da idanu. Ummu mace ce mai yawan tsantseni wajen tarbiyyar ƴaƴanta. Komai tana binsa a sannu babu garaje ko gaggawar akan tafida yaranta tun kafin sukai haka, shiyyasa cikin sauki take iya sanin matsalolinsu da saurin fahimtar sabuwar hanya da suka ɗauka saɓanin wadda ta sansu da shi. Yanzu ma dai ɗauke kai tai ga Iffah ta cigaba da hidimar gabanta batare data sake magana ba. Daga baya ma saita ƙirƙiri jan Iffah da sabuwar hira da bata da alaƙa data farko. Tun Iffah na ɗararewa har ta saki jikinta...


      ★Washe gari ta ɗan danne kaso sittin cikin dari na damuwarta dan kar Ummu ta hanata zuwa makaranta. Sai dai koda taje makarantar ma dai zaune kawai ta kasance badan ta nutsu a fahimtar komai ba har aka tashi. Kanta tsaye ta fito domin samun abin hawa a bakin gate kamar sauran ɗalibai. Da ƙyar ta samu tare da wasu da suke kusan a anguwarsu, sai dai zasu rigata fara sauka...

      A hankali wata baƙar mota dake fake ɗan nesa da makarantar tasu ta fara bin bayan mai Mototaxi ɗin da sam shi hankalinsa baima kai ba. Haka suma su Iffah babu wanda ya kula da motar. Da mai motar ya fahimci zasu zargesa sai ya canja salon bin nasu. A haka har aka sauke abokan tafiyarta. Motar ta cigaba da binsu har titin anguwarsu, anan aka dakata har mai Mototaxi ɗin ya shiga ya kai Iffah ya juyo zai fita suka tsaidashi..........✍


       _To ke kuma baƙar mota daga ina🙆🏻?._

       


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links