WATA UWAH 7-8

 


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


   🌹🤱🏻WATA UWAH 🤱🏻🌹


    🙆🏻‍♂️(RAYUWAR ABDUL) 🙆🏻‍♂️


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


  

 Story & written by

mommyn fareesa


   Free page 7&8


*cigaban labarin*

..........da misalin k'arfe 10:15 am "yah Abdul ne zaune atsakar gidan kan kujera y'ar tsugunne"yasha wankansa"yana sanye da yadi brown colour riga da wondo"d'inkin me gajeran hannu"kansa bbu hula"suman kansa da sajensa sunsha gyara"yayi y'ar rama da haske"sai daddad'an k'amshi ke tashi ajikinsa"sosai yayi wani irin kyau"yanata yanke farcensa na hannu"meenah na kitchen tana girki "tanata sauri ta idar sbd tana so 12: pm ta tafi skul"goggo kuma na zaune kan tabarma cikin baranda"fuskarta bbu annuri ta dubi yah Abdul tace"kai !anjima kazo ka wankemun kayana da dare kamun guga"kansa ak'asa ya amsa da to"meenah ta fito dg cikin kitchen d'in tana fad'in yaya pls Assignment d'in fa?kawo na miki"da sauri ta nufi parlour"bbu jumawa tadawo da book a hannunta ta mik'a masa ta zauna k'asa agefensa"shi kuma yadena abinda yakeyi yafara yi mata Assignment d'in da mata bayani ta yadda zata gane"meenah na sauraronsa tana tunanin irin brain d'in da Allah yabashi....sallamar kabeer ce ta dawo da ita tunaninta"sai dai tasaki baki ganin da mace yashigo kuma dg gani bbu tarbiya atare d ita sbd yanayin shigar dake jikinta yanuna hakan


  goggo kuwa baki washe tahau tarbarsu "tana cewa su shiga ciki,yyinda budur war tayi wa yah Abdul k'uri da idonta,dan yyi bala'in tafiya da imaninta...lolx"yana juyowa suka had'a ido  da ita"yawurgo mata harara had'e da Jan tsaki....afusace kabeer yace yaya budurwar tawa kakewa tsaki dan wulakanci? "Yafad'a had'e da kok'arin shiga parlour"dan ita goggo harta shigama"


Mamakine sosai a fuskar yah Abdul da tsananin bacin rai"yad'ago yana dubar kabeer" kansa yanuna yace" kabeer ni kake  gayawa mgn sbd karuwa ?" 


Salati goggo tayi dg cikin parlourn, jiki na b'ari ta fito zani a hannu tana cewa"sharri zaka masa?" yo ai kai yadace acewa manemin mata "kuma  hariji! ko atunaninka bansan irin wankan da kakeyiba kullum da asuba ?shine zaka masa sharri?abanza kak'i aure kana lalata yaran layin nan.....kuka meena ta fashe dashi had'e da salati tana cewa" anya goggo kece mahaifiyar yah Abdul ?" 


dakk'uwa ta mata had'e da cewa" inna sake jin bakinki banyafemiki ba "


kabeer ko fitowa sukayi da budurwarshi,wacce itama tana mamakin halin goggo dan azatonta yah Abdul d'in d'an kishiyar goggone ashe dantane wai!ta fad'a aranta


Yah Abdul kuwa dafe kansa yyi dake sarawa "ga wani d'aci da bakinsa keyi " yyinda zuciyar sa ke k'una ,duk abinda goggo ke masa be tab'a jin zafin abinba irin na yauba "tuni idanuwansa sukayi jajir...


Kabeer dake shirin fita shida budurwar ta shi yakalli yah Abdul awulakance yace "oh ashe  TALLE ce ke yiwa AUDI gori??"


Azuciye yah Abdul ya mik'e tsaye yanayin taku biyu ya funcikosa "har suna bige budurwar,"wani wawan punch yabasa abaki ....kabeer yazaro ido zai rama"tuni yahau jibgarsa,yyinda goggo ke zaginsa da aibatasa  dan ita a tunanin ta k'ila kabeer din zai iya bige yah Abdul din "da taga yana jibgarsa tukum"ta hau tijara yayinda meenah keta kuka...


yah Abdul sarkin fushi "dan be iya fushiba "amma yanada hak'uri be damu da goggoba dukan kabeer kawai yakeyi "yyinda budurwarsa tayi waje gudun kar a had'a da ita...


Koda goggo taga be bariba tuni ta matsa tana marinsa had'e da cewa" ALLAH yahad'aka da sharrin masu sharri  tunda kamasa haka.....cak yatsaya had'e da dukewa a gurin jin goggo na masa baki"yana hawaye masu zafi had'e da bata hak'uri,banxa tayi dashi takama kabeer me kumburarrar fuska suka shige daki dashi"


meena dake kuka tazo ta mikar dashi tsaye tana basa hakuri had'e da cemasa bbu abinda zaifaru dashi ai beda laifi..


shiru yyi amma yana tsoron bakin uwah.


"sannan yana zargin anya goggo ce mahaifiyarsa kuwa?"


 har d'akinsa dake soro ta rakasa "kafin ta dawo xuciyarta cike da tausayinsa..


   kwana 2 da faruwar haka"gaba d'aya yah Abdul sau 2 yake shiga gidan arana"idan yashiga da safe zai gaisheta yayi wanka yafita"sai in shiga toilet yakama yake shiga amma ko abincin gidan yadena ci"

     

Idan ruwa zai kama da dare koda asuba awaje yakeyin bukatarsa baya shiga gidan"


sosai damuwa ta masa yawa acikin y'an kwanakin"ga sha'awa dake masifar damunsa"


Afanninsa da jidda kuwa be koma zuwa gidan suba ,saidai yakirata ta waya kimanin sati 2 kenan"


Ayau yakama Tuesday" kuma ayau ake yin kamun maryam"


Tun wajen k'arfe 4:30 pm  jidda ta shirya cikin d'inkin ankon"doguwar riga gownt ce wacce ta bayyana ainahin suran jikinta"dan ba yah Abdul tabama d'inkin ba"


mayafi bak'i ta yafa samqn kanta"bayan tasaka y'an kunne"tayi parking gashin kanta data k'ara attach aciki"


 plate shoes tasaka ta rik'e y'ar post tata wacce ta saka baby nokia d'inta aciki"


magajiya na kwance samqn gadonta na k'arfe tabi jidda da kallo tana murmushi tace"masha Allah kinyi kyau"muje naga yadda zaki dinga taku d'aid'aya"


Jidda na dariya suka fito dg cikin d'akin"ummi na tsakar gidan tana girka tuwon dare"bilkisu na islamiya"kallo d'aya tayiwa uwar da y'ar ta d'auke kanta"


Asoro suka tsaya magajiya tayi k'asa da murya tace"anjima dan Allah kitafo mana da kaza"dan nasan yadda kikayi kyau haka zakiyi sabon saurayi"sai kice yasiya miki"


Jidda na k'ok'arin mgn Abba yashigo cikin soron"tab'e baki magajiya tayi"yadubi jidda fuska ad'aure yace"ina zataje?" gun bikin k'awarta maryam mana"


baki yi hankalin turata islamiya ba sai gidan biki?" shin wai wace irin UWACE ke magajiya?"


yanzun ahaka zata fita da wannan shigar dake nuna tsiraici?


Dan Allah mlm kabar yarinyar nan ta sarara haka mana"ai zamani yazo da hakan ba wani abu ba"ke jidda wuce kije"


Jidda batayi mgn ba tayi gaba"Abba ya girgiza kansa yayi cikin gidan yana tunanin anya zai iya cigaba da zama da magajiya?"wacce ta kasa tayi hankali har yanzun"ko kwanciyar aure zaiyi da ita saiya biyata kud'i ko tak'i yarda dashi"


hakan yasa sai yayi wata da watanni bbu abinda yafaru tsakaninsu da ita"


Ummi dake zaune ta amsa sallamar sa"atake ta fahimci ransa ab'ace yake"


mlm sannu da zuwa"yauwa sahura"bani buta nashiga bayi"dato ta amsa ta tashi ta zuba ruwa ta rusuna tana mik'a masa"


magajiya ta shigo tsakar gidan tanata gatsine da yada haibaici"bbu wanda yatankata acikinsu"


Afannin jidda kuwa time d'in data isa gidansu amarya harma anfara tafiya"dan Asee baby tama jima acan"


hakan yasa itama tabi wasu suka iso"duk yadda jidda ke ganin ta had'u dataga wasu cikin ankon sun d'auki babban dressing ta raina kanta"


musammun k'awarta Asee baby"dan takalmi da hand bag da agogo da y'an hannu"zuwa gyale da sark'a da tasaka ajikinta" kud'in su zasuyi kimanin 60k"ga wayarta iphone a hannunta"in baka santaba zaka d'auka Asee baby d'iyar masu dashi ce"


sosai jikin jiddan yayi sanyi taji tanaso takai Asee koma tafita"


Agefen Aseen ta zauna"Aseen ta dubeta tana tab'e baki tace"nazata ai Abdul d'in naki bazai barki kizo ba?"


sai kace aurena yakeyi?" nasan ko kinyi auren bamu sani ba"dallah nidai kidena mun maganar"kinyi kyau sosai wlh k'awata"hmm kema haka"


dan ma kin tsaya k'auyanci da duhun kai"ki nuna kyauwunki abin ya gagara"kin tsaya wajen talaka fatararre"sai kace kyawun nasa zai baki?"


Shiru jidda tayi ta kasa mgn"Asee na murmushi tace"tashi mu koma can zamuyi mgn dake"


babu musu suka matsa agefe Inda babu mutane sosai"


Asee na murmushi tace"nifa jidda bazan b'oye miki komaiba sbd bana shakkar kowa"tafad'a tana juya idanuwanta"


kafin taci gaba da cewa"miye aciki idan kin zab'i rayuwar hutawa dg baya ki tuba?"yanzun haka acc nawa da hand bag nawa akwai mak'udan kud'ad'e"


rabon dana ci abincin gidanmu har na manta ma"dan abinda nakeso nake cima raina"nasaka suturan danake so"naje yawan gari"na rik'e wayar danake so"


Ko ko wanki da guga banayi biya nakeyi amun"kinga kuwa dole nayi kyau na murje"


Amma ke kinason hutu da gayu amma kina tsayawa sokwanci da tsoro" ko kuma soyayya ta rufe miki ido bayan matsiyacine beda ko sisi"


Amma kinajan kud'ad'e saiki auresa kiyima kanki kayan d'aki"dan ni nan wlh dakike gani inba mai kud'i nasamu ba bazanyi aureba"


kazo kayi auren haihuwa 3 akasa ganeka sbd kajik'e"amma idan mai kud'i nefa mijin?


Ko last 2 weeks  d'in nan mun had'u da wani sabon Alh wanda babawo yahad'amu"kusan 500k naja wajensa"


zaro ido jidda tayi tana fad'in 500k fa kikace Asee???........✍️


wasa farin girki akwai sark'akkiya alabarin da zazzafar soyayya agaba kunsandai alkalamina😊


wannan book d'in nakudine 

Normal grp 300

Vip grp 1000

Special people 2k wato 3pages in a day 


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina  08100084251 

300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


  banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo  dan Allah banda kira❌ 


Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50

 Normal grp 500f

Vip grp 1000f

Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links