ELHAJJ 8


 ðŸ¤ŽðŸ¤ŽðŸ¤ŽðŸ¤Ž

                    *ELHAJJ*

                                  🤎🤎🤎🤎


Free page 8

    

   Written by

        Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387



*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃



*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*



*LOCATION KANO*


08062073990


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



  Sosai Elhajj ya zage yaci abincin don ba karamin dadi yai masa ba, yana ci momma na masa hira har ya gama.


Tashi yai yana wanke hannun sa a sink din dake gefen palourn, a nutse yace "Sai da safe Momma". Bai Jira amsar taba ya wuce part dinsa.


Bin sa da wani mugun kallo tai tace "Dani kake magana daga kai har uban naka shege Dan iska kawai na kusa magananin Ka......"


Yana isa part dinsa yaji wata muguwar kasala ta lullube sa, lumshe idon sa yai kawai ya kwanta akan gado ba tare da yai addu'a ba don yama manta ana addu'ar bacci gaba daya...


**

 Cikin tsananin duhu yake ko tafin hannun sa baya gani, daga gabansa rami ne wawakeke sai bayan Sama, shima ramin ne babba, tana tsakiya ana mutane biyu uku ne a gefensa kowa kokarin ganin ta tura sa cikin ramin yake, in wannan sun tura ya Kusa shiga sai wannan suma su tura suma, gaba daya yayi bakikikkirin  sai mummunar dariya kawai ke tashi Mara dadin sauraro.


Daga can gefensa yaga Malam ne yake tsaye a gurin haske, yana tsaye hannun sa rike da carbi cikin daga murya Malam yake fadin "Ka tashi Muhammad, Ka tashi nace ma".


Amma ya kasa sai kokarin miko hannu yake, daga bayan Malam wani haske mai tsanani daya bayyana fiskokin mutanen da suke kokarin tura sa a ramukan nan, da sauri yaga hasken yana nufo sa yazo dai-dai gaban sa kawai hasken ya bace...


A razane ya tashi daga baccin yana murza idonsa cike da tsoro, duk ya hada gumi.


Kusan sati biyu Kenan yana irin wannan mafarkin, amma ya rasa ya zaiyi gashi ba Wanda zai samu ya fadawa dama Malam ne yake sharing irin wannan maganar dashi, toh shima kwana biyu baya zuwa gidan sa haka kurin yake Jin haushin Malam din.


So yake ya tashi yaje yayi sallah amma ya kasa kawai sai ya runtse idonsa yana tuno mafarkin da yai.


Sai da akai asuba sannan ya mike duk jikinsa yayi sanyi, ga wani zazzabi da yake ji yana kokarin rufe Shi.


Da kyar yai alwala yayi sallah a daki don baya jin zai iya fita masallaci, yana idar wa ya koma gado ya kwanta sai anan wani wahallalen bacci ya dauke sa.




***********


Gama aiki na kenan tun da duku dukun safe, a Palour na zauna ina mimmike kafafu na din baya na yadda yake amsa min.


Shigowa Mama tai tana sanye da doguwar riga sai sassanyan kamshi take, mikewa nai zaune nace "Mama ina kwana".


Ba yabo ba fallasa tace lafia qalau, ki shirya anjima in babanku zai fita tare zaku, yace "yau zai gabatar dake a gun MD din".


Zaro ido na nai nace "Mama yau zamu je company din fa kika ce".


A dake mama tace "ko baki ji ni bane sosai, ki tashi kiyi wanka ki shirya don yanxu zai fito kuma kin san sa baya son jira".


Mikewa nai na fita zuwa ban daki, wanke fuska da kafafuna kawai nai na fito, Mama tana zaune ko kallo na batai ba, daki na shiga na mulka mai a fuska ta da kafafuna, kwalli na nasa na dauko hijab dina na sallah Wanda Ya Hajara tai min, dark blue ne dogo har kasa, ya haska farar fata ta sosai.


Kallon kai nai a mirror nayi murmushi, ina tsaye ina gwada yadda zan yiwa MD magana Mama ta kwalo min Kira.


A guje na fito hannuna rike da katuwar jakata, ta Inna ce na dauke mata don yadda nake son jakar duk ta tsofe gaba burmemiya.


Ina fitowa Mama ta kalle ni tun daga Sama har kasa, har zatai magana sai kuma tai shiru kawai tana girgiza kan ta.


Hade rai tai sosai tace "kinji dai abinda na fada Miki, ki kula da kanki banda shiga abinda bai shafe kiba, banda Kula Maza ki rike mutuncin ki sosai".


Rau-rau nai da ido nace "Toh Mama kar ki samu damuwa, ba Wanda zan bari ya rike min hannu bare nayi ciki, kuma kinga ni ban fara al'ada ba balle ace koh".


Tsaki Mama tai tace "Allah ya shirye ki gaskia, wuce muje ya fito jiran ki yake".


Sum sum nabi bayan Mama muka fito, duk mutan gidan suna tsakar gida sai hada hada suke yara zasu tafi makaranta.


Ban kalle ko wacce a cikin su ba sai Baba na kalla nace "ina kwana Baba".


Yana duba wasu file a hannun sa yace "lafia qalau, kin shirya dai ko sosai".


Murmushi nai ina daga Kai nace "sosai ma, tsintsiyar ce dai nake tunanin ko na ari ta Mama" .


Ba shiri ya dago ya kalle ni, girgiza kan sa kawai yai yace "basai kin dauka ba da akwai komai a can ai".


Gyada kai nai, ina daga ma Mama hannu, Umma dake zaune a kofar dakin ta ta buga tsaki mai karfi har sai da kowa ya juya ya kalle ta.


Baba ne yace "lafiyar ki ke kuma kike bugawa mutane tsaki".


Hararar sa tai tace "haba Malam, kama ta yai gaskia kayi adalci akan wannan lamarin, taya zaka samo wa Dije aiki ita kadai bayan ga Hajjo a zaune a gida haba, Fure don Allah wannan adalci ne?".


Inna fure dake sosa kunnen ta da tsinken ashana tace "ina fa Maman Hajjo, ai ni shiyasa ban yi magana ba kar ace toh bakin ciki kake, amma maganar gaskia wannan ba adalci bane".


Kallon su kawai Baba yai kafin yace "ynxu ku baku ji kunya ba, nan fa a gaban ku Yarinyar nan tace tana son na nema Mata aikin ko Shara ne, amma sai kuka fara maganganu cewa Allah wadai ya'yanku suyi aikin Shara, toh ynxu kuma da ta samu shine ku ke hassada?".


Zumburo baki gaba Umma tai tace "Malam kadai duba gaskia".


A harzuke yace "baxan duba ba din, ke wallahi ko MD din da Kan sa yace in ina da wata yarinyar na kawo a bata aikin cewa zanyi banda ita munafukai kawai".


Kallona yai yace "wuce muje".


Wani murmushi nai ina gyada kai na bi bayansa.


A bayan machine dinsa na zauna ina rike da jakar sa da tawa, a hanyar ba Wanda yace wa kowa komai har muka isa company din.


Tunda muka shiga gabana yake faduwa, amma sai na share ban bada hankali na akan hakan ba, sai kara ware manyan idona nake ina kallon katon company din.


Parking machine dinsa yai a inda yake ajiye wa yace "sakko muje toh".


Bin bayansa nai sai wulla idona nake a companyn ina jinjina girma da kyaun sa.


Ciki muka shiga bansan lokacin dana lumshe ido na ba sbd sanyin AC, duk inda muka wuce sai gaisawa Baba yake da mutane yana gabatar dani a matsayin Yar sa wacce zata dinga gyara office dn MD.


Ni dai nawa murmushi ne kawai, lokacin da muka zo zamu hau elevator Baba hannu na ya rike ya kalle ni yace "ki nutsu nasan halin ki".


Gyada kai nai ina kankame hannun sa, a ciki ma sai wur ga ido nake kamar na sa ihu, na nutsu ne kawai sbd Baba.


A 6th floor muka tsaya wanda tun da muka shigo companyn banga inda ya Kai sa haduwa ba, palourn ne za'a ce wanda ke dauke da kujera set 1 da center table ba carpet dai ga Standing AC da kuma ta bango, sanyi ko ta ina.


A cikin gurin paloun da akwai kofa wacce nake tunanin Banda ki ne, daga gefen hagu kuma da ba komai a gun, glass ne ya mamaye bangon sai kofa a tsakiyar glass din ko ba'a fada ba nan ne office din MD din.


Daga karshen glass din bangaren hagun anan akai wa secretary din MD nasa gurin, dake dauke da kujera da table.


Gurin secretary din muka nufa, cikin fara'a ya mike yana fadin "Baba kai ne da kan Ka, ina kwana".


Murmushi Baba yai yace "lafia qalau Yasir ya aiki?".


Murmushi yai yace "Alhamdulillah Baba".


Kallona Baba yai da na shagala gurin kalle kalle yace "ba ki iya gaisuwa bane?".


Da sauri na dago na kalle sa ina turo baki nace "ina kwana".


Dariya yai yace "lafia qalau".


Harara ta Baba yai ya kalli Yasir yace "MD bai shigo ba".


Cikin girmamawa Yasir ya daga kai yace "bai shigo ba, ina ga sai anjima ko bayan Azahar".


Gyada kai Baba yai yace "Allah ya kaimu, dama yace zai bawa Dije aikin share masa office ne shi ne na kawo ta yau, amma in ba komai sai ta zauna anan ta jirasa in ba damuwa".


Dariya Yasir yai yace "bakm Baba, ta zauna in yazo sai na kira ka din".


Godiya Baba yai masa ya kalle ni yace "wuce muje, ki zauna akan kujerar can ki jira, banda fitina ki nutsu wallahi".


Turo baki nai nace "Haba Baba in kana fadar haka ai sai ayi tunanin ko bana Jin magana ne".


Girgiza kai Baba yai kawai ya wuce.


Zama nai akan kujerar bansan lokacin dana lumshe idona ba sbd laushin ta, murmushi nai ina kwanciya akan kujerar nace "ai ni ko dan nasha AC na kwanta akan wannan kujerar na dinga zuwa kullum ma wallahi".


Ina kwance ina shakar kamshi tun ina jin maganar Yasir da yake amsa waya har bacci ya dauke ni anan.....






*********


A hankali ya shiga bude idon sa ya suka masa nauyi, da kyar ya tashi yana kallon Agogo karfe 11 har da rabi ta kusa.


Da sauri ya sakko daga kan gadon yana mika, duk da kan sa dake masa ciwo kamar zai rabe amma haka ya daure ya shiga toilet yayi wanka.


Ya dan dade sannan ya fito yana tsane gashin kansa dake digar da ruwa.


Cikin kasala ya shirya cikin wata jallabiya coffe colour haka kurin yaji yau baya ra'ayin sa kaya mai nauyi, turare ya fesa sosai sannan ya dauki jakar sa ya fito kafar sa sanye da takalmi mai laushi kamar silifas.


Bai tsaya shiga cikin gidan ba kawai mota ya shiga security yaja suka nufi company, duk da yunwar da yake ji amma baya son tsayawa bata lokaci don cin abinci da akwai file din da xai yi signing.


San da suka shigo companyn da kyar ya fito daga motar, duk jikinsa kamar wanda aka yiwa dukan tsiya.


A hankali ya fito gabansa sai bugawa yake da karfi, lumshe idonsa yai a hankali yana tafiya duk Wanda ya gaishe sa daga masa kai kawai yake ya wuce har ya shiga elevatorn.


Bugawa zuciyar sa take da karfi har sai da ya dora hannun sa ya daura akan kirjin sa dai-dai saitin zuciyar sa, lokacin da elevatorn ya bude sai da ya rintse idonsa da karfi.


Tattaro dukkan nutsuwar sa yai ya shigo palourn Kan sa na wani irin sara wa, Jin jiri na dibar sa yasa shi Zama akan kujera da sauri.


A razane na mike zaune ina janye kafafuna jin an zauna a kansu, dago fuskata nai idona ya shiga cikin nasa a tare zukatan mu sukai wani irin bugawa da karfi.....




********


Ihuuu mai firgitar wa kasurgumin bokon yai da yasa ta saurin masawa gefe sbd yadda rumfar da suke tana girgiza kamar zata fado kansu, ga ihun masa da ya hargitsa dajinn...


Ya dau mintuna suna yi kafin ya dago ya kalle ta idonsa kamar wuta sbd tsabar jaa, da katuwar muryar sa yace "kin makaro wannan ranar nake jiye Miki kika tsaya wasa, ynxu sai abinda kIka gani kawai ta riga ta bayyana....."


A firgice tace "wace ta bayyana la'ananne?".


Daka Mata tsawa yai yana buga wata kwaryar dake gabansa, kallon ta yai cikin bacin rai yace kina kallo ko, ya bace bat baxan iya ganin sa ba matukar yana tare da wannan Yarinyar, aljanun dake jikinsa duk sun fita a dai-dai wannan lokacin sbd kusancin da ya wanzu a tsakanin su...


Gaba daya ta gama firgita, gumi duk ya jikata, banda rawa ba abinda jikin ta yake za ta sake magana ya daka Mata wata tsawa data sata mikewa ta kwasa a guje tana sakin fitsarii......





*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300  KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


09066728387




Comments Nd share plz




Mrs A.M🥰

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links