ELHAJJ 10

 


🤎🤎🤎🤎

                    *ELHAJJ*

                                  🤎🤎🤎🤎


Free page 9

    

   Written by

        Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387



*BABY BEAUTY LOUNGE*


*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA  CE*


*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*


PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638


*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*



    A razane na mike zaune ina janye kafafuna jin an zauna a kansu, dogo fuskata nai idona ya shiga cikin nasa, a tare zukatan mu sukai wani irin bugawa da karfi.


Kara waro ido na nai ina kallon wannan Ustaz din dake gabana, ni kai na nasan ina da kyau amma sai naga wannan ya ninka ni a kyau duk da ba farar fata ce dashi ba, babban abinda yaja hankali na gare sa na Kura masa ido shine duhun da na gani a kewaye a kansa, sosai na nutsu ina kallon kan nasa ganin duhun yana baya baya a hankali.


Shi kuwa Elhajj neman ciwon kan da yake damun sa yayi ya rasa, ga wani nutsuwa da ya saukar masa Wanda ya manta rabon da yaji irin ta.


Zuba ma yar mitsitsiyar yarinyar ido yai yana kallon ta, duk da yadda kyaun ta yake fisgar ta amma haka ya zuba mata ido yana mamakin wace wannan da har tazo ta zauna a Palourn da yake saukar bakin sa.


Ganin yadda yake kallona yasa na turo baki gaba, cikin kunkuni nace "haba Ya Ustaz taya zaka wani zuba min ido kana kallona  badai kyau kallon haram".


Dan ware idonsa yai yana lumshe wa a hankali, a ransa yana mamakin maganar ta wai ya zuba mata ba kyau kallon haram, murmushi yake son yi amma sai ya daure, ita wannan mitsitsiyar Mai zai ji a gare ta da har take cewa bakyau kallon haram.


Ganin bai yi magana ba sai lumshe idon sa da yai yasa na mike daga kan kujerar da nake na koma wacce ke kallon sa.


Zuba masa ido nai ina kallon sa kawai, can nace Ya Ustaz baka magana wai, ko dai kurma ne?.


Bude idon sa yai ya kalle ta da idonsa da suka dan chanja colour, yatsina fuska yai Jin wani dan tsami tsami a Palourn yana tashi.


Kallon ta yai yaga ta zuba masa manyan idonta tana kallon sa, hade rai yai sosai a dake yace "Ke kin yi wanka yau?".


Zaro Ido Dije tai sai kuma tai saurin sa hannu ta dafe bakin ta, kallon sa tai tana mikewa tsaya, shinshina jikin ta ta fara ta kalle sa tace "haba dai don Allah Ya Ustaz, ba wani wari da nake wallahi ban yi wanka ba dai sai gobe gaskia kwana uku uku nake bana wanka sbd tattalin ruwa".


Zaro Ido yai da mamaki yace "what?".


Fari nayi da ido nace "yess, tattalin ruwa nake kaga shekaran jiya nai wanka don haka sai gobe zan yi kuma ai bana tsami fah".


Wani yamutsa fuskat yai a dakile yace "kazama ce keh Amma, mai ma kike yi anan".


Hannun nasa ta jikin hijab na rike kuguna a Tsiwace nace "lala-lala Ya Ustaz daka ta, wannan ai zagi ne taya zaka ce wai ni kazama ce, sannan maganar me nake yi anan toh shi MD din nice wacce zan dinga masa gyaran office, aiki ya bani Mai kyau atoh".


Da mamaki ya Kara ware idon sa akan ta yace "shi MD din ne zai baki aikin gyaran office bayan bakya wanka".


Hade rai nai nace "bafa nasan zagi gaskia Ya Ustaz haba, ai maganar zai bani ma bai taso ba don ya riga ya bani aikin nema, ynxu zaman da nake yi anan jiran sa nake yazo mu shiga ciki na gyara masa tsaf".


Ya bude baki zai magana muryar Baba ta karade paloun Yana sallama, lumshe idon sa yai yana gyara zaman sa sosai a Kan kujerar.


Cikin bashi girma Baba yace "barka da zuwa MD".


Kwalalo idanu waje nai a firgice nace "MD kuma Baba? Wannan dinne MD?".


Wani kallon Baba ya min yace "ko kin masa rashin kunya ne Dije".


Yarfe hannu na shiga yi ina fadin "ba abinda na masa Baba, ni fa Ka ganni a tsaye ma gaishe sa nake yi".


Bude idonsa yai ya kalle ta ta kasan ido yadda baxa ta gane kallon ta yake ba, dan girgiza kan sa yai a hankali a ransa yana fadin kila bata da lafia ne shiyasa ta cika suruta haka.


Baba daya lura MD din baya cikin mood din magana cikin nutsuwa yace "wannan itace yarinyar tawa Dije sunan ta, na kawo ta yau ne sai ta fara aikin tunda kace ko yaushe zata iya fara wa".


Idon sa a lumshe yace "bkm Baba, Yasir ya bude mata office din ta gyara kafin na shiga".


Kallona Baba yai yace maza bi bayan Yasir din sannan saura ki zauna kina shirme zamu hadu ne.


Turo baki mai ina fadin haba Baba don Allah.


Zaro min ido yai yace zaki wuce ko kuwa?.


Bin bayan Yasir din nai ina marairaice fuska kamar zan yi kuka, shidai Yasir bai ce komai ba sai nuna min office din ya shiga yi da kuma yadda ake gyara wa, har dakin dake cikin office din da toilet dinsa sai da ya nuna min yadda zan gyara sa.


Fita yai ya barni ina kalle kallen office din sbd haduwar sa, daga cikin office dn ana kallon duk abinda ke faruwa a wajen paloun da compound din company sai dai su basa gani.


Ganin zan bata wa kai na lokaci na shiga gyara wa a nutse don fa ni ba baya ba gurin aiki Kam, cikin kankanin lokacin na gyara ko ina, na wanke toilet din cikin bedroom na chanja masa bedsheet, air freshener na fesa ina korafin cewa zan dinga zuwa da turaren wutan Mama ina kunna masa ni dai kamshin freshner din bai min dadi ba.


Kayan dana share da mopping na fito da su na ajiya a inda na dauka a cikin palourn, komawa nai na zauna a kan kujera ina fadin "wayyooo ya'yan hanjina kuyi hakuri kunji, na kusa koma wa gida".


Bude idon sa yai ya kalleta Jin abinda take cewa, mike wa yai kawai a ransa yana fatan gyaran yaki masa yadda yake so ta yadda zai sallame ta ba tare da ya batawa Baba rai ba.


Yana shiga office din ya lumshe idonsa Jin wani kamshi mai sanyi daya ke tashi, bude idon sa yai yana kallon office din ko ina kal an gyara an goge, murmushi yai yana shigewa bedroom din office dn.


An gyara shima ya same sa sai kamshi yake yi ga bedsheet ta chanja masa, sai da ya gama kalle kallen sa sannan ya koma cikin office dn.


Zama yai yana duba files din dake kan table din jefi jefi kuma yakan dago ya kalle ta yadda ta kwanta a kan kujera ba abinda ya shafe ta.



**********


   Duk ta rude ta jike sharkaf da gumi, hankalin ta a tashe tace "ynxu na kan dutse me ye abin yi".


Shiru dan tsamurmurin bokan yai yana Zane akan dutsen dake gaban sa, ya dade yana yi sannan ya dago ya kalle ta cikin muryar sa kamar ta mace yace "ban samu damar ganin ko wace ita ba, amma tabbas shigowar ta rayuwar sa abune da baxai mana kyau ba, don zata iya rusa Miki dukkan shirin da kika dau shekaru 30 kina yi".


Zaro Ido tai tace "duk Shirin da nake yi na kan dutse, sai da abu yazo gangara kuma a samu matsala".


Kara manne kananun idon sa yai yace "tabbas kuwa, ba karamin alkhairi bace Iya a rayuwar sa, mu kuma sharri cev ita a gun mu".


Share gumin fuskar ta tai tace "ynxu meye abin yi na kan dutse?".


Kallon ta yai yace "wannan Karan aikin da zan miki mai matukar hatsari ne, ban taba miki irin sa ba amma matukar xaki iya toh zaki mallake sa, ya kasance sai abinda kike so zai yi ba tare da kowa ya fahimta ba".


Cikin zakuwa tace "zan iya ai na kan dutse matukar akan biyan bukata tace ba abinda baxan iya ba".


Wani leda ya miko mata yar karama dake dauke da garin magani, cikin rawar jiki ta sa hannu ta karba.


Da siririyar muryar sa yace "wannan zaki je can gurin aikin nasa ki barbada masa akan kujerar da xai zauna, ki tabbatar ya zauna akan kujerar, ko wace ita in har ya zauna akan kujerar nan xai ji ya tsane ta kuma zai yi yadda zai yi ya nisanta kansa da ita".


Murmushi tai tace "wannan ai mai sauki ne na Kan dutse".


Ido ya zuba mata na yan dakiku kafin yace "abinda zaki aikata babban abune, zaki kwanta da shi yaron ku sadu a wannan saduwar muna bukatar maniyiin ki da nasa a hade da shi xan Miki karshen aikin ki, daga shi kin gama mallakat komai nasa".


Daskare wa tai a gun tun da taji ya ambaci saduwa, ita dawa zata sadu badai Elhajj ba yaron yayar ta wanda kuma ya kasance da a gare ta.


Ta bude baki zatai magana ya daga mata hannu, cikin hade rai yace "kije kiyu tunani, Amma ki sani wannan shine kawai mafitar ki ta karshe".


Mikewa tai zata fita yace "kar ki Manta ba ke kadai bace kike son ganin bayan sa, da akwai wadanda suke aiki a kansa fiye da Wanda ke kike yi a kansa a ynxu haka, sannan zan iya ce wa sun fi hadari da son mallakar dukiyar sa".


Shiru tai kawai yana goge gumin dake tsatsafo Mata, ita Kam har ynxu ta rasa su waye suke son ganin bayan Elhajj bayan ita, ta hanga ta hanga Amma bata samu damar gane ko su waye ba.


Cike da damuwa ta tari taxi ta nufi airport don komawa Kano, karya tayi wa Papa dama tace zata je gidan kawar ta sunyu gobara shine tazo Enugu don ganawa da na kan dutse..  




*******


Zagaye palourn yake hannun sa a bayan sa gaba daya ransa in yayi duba ya baci, cikin bacin rai yace "haba haba Hajia wani irin cin mutunci ne wannan, Kamar ni ace xan jewa Yaya da wannan bukatar amma ya nuna min cewa baxai iya min ba".


Hajia Batulu itama ran nata a bace tace "Ai ba tun yau nake fada ma cewa Yaya Hassan bai dauke Ka matsayin kani ba amma kaki yarda, ina fatan dai ynxu Ka gane".


A zafafe yace "tabbas na fahimta ynxu kuwa Hajia don Yaya ya bani mamaki, 500m kawai nake nema fa ya bani na shigo da kayana amma ya hana, kuma kinsan tunda ya hana shima wancan tsinanan Dan nasa bazai bayar ba".


Cikin Jin haushi sosai tace "ai Alhaji baxai bayar ba wannan abin haushin da mai yayi kama, kai ka dogara da shi kana aiki a karkashin sa, dan kama ya dogara da dan sa haba mu kenan ba xamu taba samun ci gaba ba kenan sai dai mu Zama koma baya a gunsa".


Zama yai a gefen Hajia Batula yana huci yace "ynxu meye shawara?".


A kufule tace "shawara daya ce ai Ka yadda na nufi gurin malamai kawai a san yadda za'a yi wallahi, don wannan abun yayi yawa".


Shiru yai kamar baxai ce komai ba jikin sa yana sanyi wata zuciyar tana tuna masa cewa twin dinsa ne fa yake shirin Kai wa gun boka.


Ganin kamar baxai yadda ba yasa hajia Batula dinga ziga sa har sai da ya yadda, ya kuma mata transfer din kudi masu nauyi Wanda zata bawa bokan.


Salim da tunda suka fara magana yake tsaye a bakin kofa bai shigo ba sai da ya gama jin duk abinda suka ce.


A razane ya shigo palourn yana fadin "haba Mum plz kar kuyi haka mana, meye ribar ku ynxu sbd abin duniya zaku fada halaka".


Daga masa hannu Hajia Batula tai tace "kaga Salim dakata in kai zuciyar ka ta mutu baza Ka iya nema wa kan Ka yan ci ba toh kar Ka hana ni nema wa baban ka Wawa kawai Wanda bai san inda yake masa ciwo ba".


Kallon Alhaji Hussain yai zai yi magana shima ya daga masa hannu, dole yayi shiru kawai ya juya ya fita daga gidan zuwa nasa gidan ransa a bace.....




**********


Mikewa nai Jin ana kiran sallah, toilet din palourn na shiga nayi alwala, shinfida dan kwali na nayi a kasan tiles nai sallah.


Ina zaune ya fito daga elevator da alama shima masallacin yaje bayan sa Yasir ne dauke da ledoji manya, ina kallon su har suka shige cikin office dinsa.


Sai da sukai wajen 10 Minutes da shiga sannan Yasir ya fito, kallona yai yace MD "Yana Kira"


Da sauri na mike nace "badai laifi nai na a Ya Ustaz ba koh?".


Dariya ya kyalkyale da ita yace "wai MD kike cewa Ya Ustaz".


Tabe baki nai nace "toh kai baka ga yadda ya sha jallabiya bane irin ustazan islamiyya dinnan".


Murmushi yai yace "nidai jeki kar ki sa nayi laifi".


Tura kofar nai bakina dauke da sallama, Kan sa na akan computer din sa Yana dannawa bai dago ba har sai da ya gama abinda yake.


Ni kuwa idona na kan table dinsa ganin take away, roba biyu fried rice ce taji liver sai kamshi take, dayar robar kuma KFC ne a ciki manya manyan kaji, ga drinks da ruwa a kai sai wata robar da aka sa chips Nd plantain.


Wani yawu na hadiya ina kallon abincin cikina sai kukan yunwa yake.


Tun da ya dago yake kallon ta, magana yake mata akan sakon da zata karbo masa a reception amma yaga alama hankalin ta baya kansa.


Dukan table din yai da karfi yace keeeee.....


A razane na dago na kalle sa na tare da tunani komai ba na shagawabe fuska nace "Ya Ustazu Ka taimako min da kazar nan rabona da kaza naji shekara inaga, kuma gaskia ni bana wa cikina hakinci Rai na ya biya Allah".


Ware idon sa yake kawai yana kallon ta yana jinjina wa karfin halin ta........




*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300  KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


09066728387



Comments Nd share plz





Mrs A.M🥰

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links