SANADIN LABARINA 60

 

Page (60)


***Tun da sukayi sallar asubah ta koma bacci, be fada mata zai fita ba dan yaga alamar a gajiye take tikis har lokacin sai bin gefen gado take karshe ta haye tana jan duvet ta rufe kanta nan da nan kuwa tayi bacci. A nutse ya shirya cikin shigar farar shirt me layin baki daga saman shoulder din, navy blue dogon wando sai light blue tie. Be saka jacket da cap din ba sai ya ajiye su a gefe ya gyara zaman waist belt dinsa sosai ya shiga dan madaidacin kitchen dinsu ya samo coffee yasha kad'an sannan ya fito ya saka dark blue din sau ciki ya dauki briefcase dinsa ya dora cap din akan sa ya rike jacket din a dayan hannu ya zo daidai kanta ya durkusa kad'an yayi mata peck a gefen kuncin ta, ya ajiye mata note a gefen gadon ya fice da dan sassarfa.

  Cikin bacci taji kamar ana taba kofa, ta bud'e idonta kad'an tana wurwurga idon ta a dakin tana neman sa, baya nan sai ta sakko da sauri ta fito falon nan ma baya nan. Kofar taje ta bud'e a zaton ta ko shine ya dan fita sai taga Yasmin a tsaye taci uban kwalliya rike da basket me kyau a hannun ta.


"Goodmorning." Tace mata tana rabawa ta shiga cikin gidan kai tsaye, sakin kofar Jidda tayi tabi bayan ta tana jin duk ta muzanta dan ko brush batayi ba bare wanka.


"Captain fa?" Tace tana kallon falon


"Oh yau fa dole ya fita da wuri na manta, oops ya akayi na yi late har ya fita? Allah yasa ma yayi breakfast dan nasan yau kam zai zama so busy." 


Kallon ta kawai Jidda take bata ce komai ba amma maganganun ta sun dan taba ta, kenan fita yayi amma ta share baki tana bacci babu wanka bare tayi tunanin samar masa abinda zai karya.


"Kanwar sa ce ke amma ko?"


Tace tana zama bayan ta gama karewa falon kallo 


"Umm." Jidda tace tana kokarin barin wajen


"Very beautiful kamar shi, amma fa ya fiki kyau."


Tayi dariya, yak'e Jidda tayi ta wuce kawai ciki ta barta a falon bakin ciki na tirnike ta, daga zuwan ta? Sai ta fara cin karo da irin wannan masu budadden idon? Tana daki tana jin motsin ta a falon ko me take yi oho, wanka ta tashi ta shiga ta dauko wani kaya da take tunanin da BA zata iya sawa ba saboda da kunya amma da taga irin shigar da Yasmin din tayi cikin wani matsattsen jeans da riga ta saka turban kawai akanta ko mayafi babu yasa ta ji itama zata iya.

  Wankan tayi ta fito ta shirya cikin rigar da ta kasance red colour ta shafa kalolin turarurruka masu kamshin gaske harda wani hadin khumra da Anty ta siya mata a wajen wata mata. Rigar da kadan ta wuce guiwar ta sai ta saka socks me dan tsawo ta gyara gashin kanta ta saka hair band ta fito da gashin ta tsakiyar kan. Light makeup tayi ta shafa red jan baki sosai wanda ya sake fito da sihirtaccen kyawun ta. Rigar daga saman wuyan an dan tsaga ta sai ta dora farar karamar rigar sanyi irin me gashin nan. 

  Yunwa take ji sosai, ragowar abincin da sukayi order jiya ta tuno ta fito falon, Yasmin na zaune tana kallo a TV tana danna waya ta saki baki ganin Jiddan, kin kallon ta Jiddan tayi ta wuce kitchen din da yake cikin falon Yasmin din na kallon ta tunda ba wai a rufe yake ba, fridge ta bud'e ta dauko abincin tayi warming dinsa a microwave ta zubo a plate tazo ta zauna a kujerar dake facing dinta ta shiga cin abincin a hankali.


"Ya sunan ki?" 


Dagowa Jidda tayi ta kalle ta, 


"Na'am?" 


"What is your name? Sannan menene alakar ku da Tariq?"


"Jidda, alakar mu kuma wannan shi zaki tambaya ai."


"Me yasa?"


"Zai fi iya fada miki ai."


"But baya tsayawa ya saurare ni ai, ni kadai nake son shi amma shi ko kallo ban ishe shi ba, please i need your help."


Wani kallo Jidda tayi mata irin kallon baki da hankali din nan, sannan tayi dariya kawai tana cigaba da cin abincin ta dan ta lura sam Yasmin din bata da hankali. 


"Please kanwar mu, wallahi inason shi sosai."


"Naga alama ai, ki sameshi kawai kiyi masa magana nima tsoron sa nake ji."


"Ba zaki iya ba?"


"No ba zan iya ba." 


Tace tana mikewa, taje ta wanke plate din ta gyara wajen ta dawo falon ta zauna tayi connecting wayarta da wifi ta kira Amira facetime, lokacin su kusan biyar din yamma. Bata daga ba sai kawai ta mike ta dan kalli Yasmin din tace


"Ki gaida gida ni na shiga ciki."


"Tafiya zan nima, idan ya dawo kice nazo, ga breakfast dinsa nan hade da lunch zan kawo dinner."


"Chef ce ke?"


"Yes." Tace tana murmushi


"Ok yayi." 


Tace tana yin gaba, ita kuma Yasmin din ta mike sai gashi ya turo kofar ya shigo, tsayawa chak Jidda tayi jin an budo kofar wanda ta tabbatar da shine, kayan jikin ta, ta kalla kunya na kamata amma sai ta daure ta cije ta juyo tana fuskantar sa., Takalmi yake kokarin cirewa ya lura da Yasmin din dake tsaye a falon nasu, sai Jiddah ta ya kalleta ya sake kalla kafin ya tabbatar da itan ce ko wata ce daban saboda tsabar kyawun da yaga tayi masa. Da wani irin salo da bata san ta iya shi ba, ta nufe shi ta karasa da dan sassarfa ganin yadda yake bin ta da wani irin kallo, rungume shi tayi da sauri ya saki jakar hannun sa yana kankame ta sosai a jikin sa.


"Welcome home baby." Tace tana ciro kanta daga kirjinsa, kin cikata yayi yana shakar kamshin turaren da take yi cikin wani irin yanayi


"I missed you so much."


"Ba kai ne ka tafi ka barni ba?"


"I'm so sorry kinji? Bana so na tashe ki ne naga kin gaji sosai, shiyasa amma dama ba dadewa zan ba."


"Tom shikenan na hakura." Tace tana masa murmushi


"You look very beautiful."


Yace yana kallon kayan jikin nata, murmushi tayi ta duka ta dauki briefcase din tasa ta rike hannun sa


"We have a visitor." 


Tace tana nuna masa Yasmin dake tsaye kamar gunki.


"She's not welcome here." Yayi mata whispering a kunne.


"Yasmin welcome, meet my beautiful wife Jidda."


"Oh,okh yayi, Allah ya bada zaman lafiya. But she's young!"


"Young and sweet." Yace yana kissing hannun Jiddan da ke cikin nasa.


"Bari na wuce, Allah ya taimaka."


"Amin mun gode." Jidda tace tana mata murmushi


"Kin manta basket dinki." Tace mata ganin zata fice, banza tayi ta karasa ficewa da sauri. Kicibis sukayi da Ishaq sai kawai ta fashe masa da kuka


"Subhallahi, me ya faru Yasmin?"


"Ishaq Tariq sam bashi da tausayi, ashe aure yayi? Duk yadda nake son shi me yasa baya so na? I'm I ugly? Or what?"


"Calm down, kinsan akwai differences tsakanin ki da Tariq, beside be taba furta miki kalmar so."


"Na sani, kuma I'm 100% ok with that hoping zai iya so na ko gaba ne, amma saboda tsabar wulakanci kaga abinda sukayi min shi da so called wife din shi?"


"Kiyi hakuri please, bari zamuyi magana dashi."


"There no need Ishaq, na hakura wallahi."


Sai ta juya da sauri ta bar wajen. girgiza kai yayi ya fasa zuwa wajen Tariq din kawai ya bi bayan ta.


  

***Yana zaune kamar sarki ta cire masa tie din ta kawo masa ruwa yasha sai ya jawota kan kafarsa ya manna kansa a jikinsa


"Kin yi kyau Jidda na,and naji dadin yadda kika fahimce ni, kuma kika yi treating Yasmin yadda ya kamata ba hauka ba zubar da class, she mean nothing to me kuma itama ta sani, Ishaq ne duk yayi complicating abun yana bata false hope bayan yasan ba haka bane ba"


"Allah sarki, sai dai tayi hakuri."


"Tariq naki ne ke kadai ko?"


"Yes!" Ta gida masa kai


"Good." Yace yana dariya


"Mine and only mine." 


Ta dora tana tashi daga jikin sa rike da tie din nasa. Jawota yayi ya maida ita ta zauna


"Then give me cin hanci idan kinaso na zama yours baki daya."


"Me kake so?"


"Anything special."


"Ok an gama ranka ya dade."


"Wow! Sai ni dan gata." Yace yana matso da fuskar sa tata, yasa baki akan lips dinta ya shiga tsotsa a hankali in a passionate way.


***Rayuwa me dadi da inganci suke yi a tsakanin su cike da kaunar Jun, Tariq baya shakkar nunawa kowa irin kalar soyayyar da yake mata musamman yanzu da suke kasar masu jajayen kunnuwa da babu wanda zai damu da abinda kake ciki ko kayi. Tare suka je ya bawa Yasmin hakuri dan ko yaya ne mutumin da yace yana son ka yafi wanda yaki ka, ashe ma tun ranar da abun ya faru Ishaq ya shigar da kansa wajen ta, and she accepted saboda dama sun shaku sosai.

  Duk da busy schedule din Tariq haka yake kula da Jiddan sosai kuma kullum a gida yake kwana tunda har yanzu be fara zama irin so busy din nan ba. Duk abinda zai yi within kasar yake ya dawo amma dai daf yake da fara fita wasu kasashen anan ne kuma dai dole Jidda tayi hakuri, be taba jin yana da second option a aikin nasa ba sai da ya tabbatar dole watarana ya dinga tafiye tafiye sosai kuma ba tare da Jiddan tasa ba.

   Wajen taran dare ya shigo gidan a gajiye tikis yana hanya sukayi magana da Fauwaz akan maganar auren sa da aka tambaya wanda Baba yace dukka zai hada harda su amira tunda itama ta samu mijin maryam dama Ya Isma'il ne, da murnar sanar mata ya shigo gidan amma sai ya sameta a kwance ta lulluba da bargo tana rawar sanyi, da sauri ya yaye mata bargon ya durkusa a gaban ta 


"Subhallahi, menene?" Yace yana dagota jikin sa


"Zazzabi nake da amai." 


Tace tana rufe idon ta saboda tsabar yadda ta galabaita dan kusan sau ashirin tana amai.


"Shine baki kirani ba? Kinga yadda kika galabaita?"


Yace yana cire blanket din saboda yadda zazzabi ya rufe ta sosai. Ruwa ya debo a tap me dumi yazo ya rurrufe dakin sosai yazo ya jawota jikin sa ya janye rigar ta ya shiga goge mata jikin da yayi zafi sosai. Sai da yaga zazzabin ya dan daidaita sannan ya shiga ta wayar sa yayi booking appointments na ganin Dr ya zabi 1hour sannan ya gyara mata jikin ta suka tafi asibitin.

   Suna zuwa akayi mata duk gwaje-gwajen da za'a mata aka tabbatar she's pregnant, tsabar murnar be san sanda ya dagata sama ba, dariya Dr din ta dinga musu sannan ta basu maganguna suka dawo gida. Tun daga lokacin shikenan kuma laulayi ya fara me matukar wahalarwa, duk sanda zai fita kamar zai mata kuka saboda tausayin ta,amma sai ta karfafa masa guiwa ta samu ya fitan baya dadewa sosai yake dawowa sai kuma washegari. Da haka har cikin yayi kwari sosai,daidai lokacin bikin su Ya Fauwaz, be so ba dole yace ta fara shiri ya kaita gidan saboda shima aikin nasa ya fara matsawa sosai dan zai iya tafiya yayi kwana biyu ko uku ma baya nan, kuma ko ya dawo ba zai fi yan awowi ba zai sake tafiya. Murna sosai ta hau yi dan batayi tunanin zasu je gida nan kusa ba, shi kansa be yi tunanin hakan ba amma gwara gidan da ta zauna anan din babu kowa shima ba zama yake ba ga ciki kuma.


***Kwana biyu da maganar tafiyar ya siya mata ticket ita kadai dan bazai samu damar zuwa ba kuma, duk bashi da walwala ganin haka yasa ta nuna murnar ta duk da itama a gefe daya bata san yadda zatayi coping idan babu shi ba, ya riga ya saba mata da caring dinsa haka dole zata sha famar rashin shi. 

   Ana gobe zata tafi ya kanainaye ta dan tun magriba ya dawo gidan ya hanata sakat duk in da ta motsa yana manne da ita, ji yake kamar yace ya fasa aikin nasa kawai su tafi tare su koma gida suyi normal rayuwar su amma ya zai? Da k'yar ya barta ta karasa hada kayan da zata tafi dasu suka yi dinner yace bacci yake ji ta san sarai kuma ba wani bacci rigima ce irin tasa gashi ita yanzu sam bata san abinda yake so din amma shi kamar wanda aka kara ingizowa baya taba barin ta abu kad'an tayi sai yace tayi turning nashi on, haka dai take daurewa yanzun ma haka ta daure dai dan ta lura da duk take-taken sa zai iya canceling tafiyar yace sai wani lokacin shiyasa take ta lallabawa tana bin sa yadda yake so din.

   Ita ta fara tashi da safe bayan sun yi sallar asubah maimakon ya barta ta karasa abinda zata karasa kafin su tafi amma ya ki barin ta, ya rike ta kam yana tura kansa cikin rigarta wajen da tafi komai daukar hankalin sa yanzu a jikinta saboda yadda suka kara girma sosai. Bata hanashi ba duk da ta kai karshe amma haka ta taimaka masa ya samu abinda yake so sannan sukayi wanka tare suka shirya. Zai wajen azahar sannan suka fita zuwa airport din suna zuwa yayi mata duk abinda zai yi, ya rakata har cikin jirgin yana rik'e da ita, sai da ta zauna sosai tana kallon sa yayi hugging dinta so tight a hankali ya rad'a mata


"Ki kula min da kanki da babyna "


"In sha Allah."


"I love you so much Jidda nah."


"I love you too."


"Allah ya kiyaye, call me da kun isa dan Allah "


"I will, in sha Allah."


Tashi yayi ya juya ya fice ganin saura kadan jirgin ya tashi, yana tsaye daga gefen wajen jirgin ya soma tafiya a hankali a hankali har ya daga sama, ya sauke ajiyar zuciya yana komawa ciki dan shine zai dauki next passengers din da zasu tashi zuwa Manchester.


   ***Kasancewar ba wannan ne tafiyar farko ba sai taga dan saukin tafiyar duk da shima ta galabaita, san gefen ta akwai wasu couples da yaran su,su biyu kuma yan Nigeria ne sune ma suka zama kamar yan uwanta. Matar me suna Amrah da Mijinta Sultan (Abinda Ke Cikin Zuciya) sai yaran su biyu, sun burgeta sosai saboda yadda suka shaku da junan su kuma yadda sukeyi ita da mijin nata ya kara sa mata kaunar Ya Tariq dinta tana hasaso suma sun zama haka watarana. Exchanging contacts sukayi da matar daidai lokacin da suka iso filin jirgin na Abuja. Mama ce da kanta tazo daukar ta, tunda ta samu labarin cikin Jiddan take cike da matukar farin ciki, sun dade da shiryawa da Baba kuma tsakanin ta da Anty babu laifi kadaran kadahan Yaya ce dai take shan gata daidai gwargwado a wajen ta. 

   Mamakin Jiddan ne ya dadu sanda suka fito taga Maman a tsaye tare da Amira da Usman suna jiran ta, da sauri Amira ta taho zata rungume ta Mama ta daka mata tsawa


"Baki da hankali ne? Baki ga halin da take ciki bane ba?"


Kunya ce ta kama Amiran ita kuma Jidda ta dinga dariya ta karaso ta russuna zata gaida Maman tace Maza Maza ta mike ba'a son me ciki da durkuso,tashi tayi a kunyace ta gaida Maman ta amsa tana kallon cikin nata.


***Rayuwa ce ta cigaba da garawa cikin ikon Allah har cikin Jidda ya shiga wata tara, an yi bikin su Amira Wanda Jidda ta zama itace akan komai dan hatta Mama ita ta barwa ragamar komai duk abinda zatayi sai ta nemi shawarar Jiddan wanda take cike da kaifin tunani hakan ya sa ta kara shiga zuciyar Maman sosai.

   Yaya ce tazo ta zauna da ita da k'yar sanda ta shiga wata takwas dan sai da Baba yasa baki sannan ta yarda tazo suka zauna. Waya suka gama kenan da Ya Tariq yace ta tashi ta fita ta dan zazzagaya gidan saboda tace masa bata jin dadin jikinsa. Yunkurawa tayi da nufin tashi taji wani abu ya soke ta da sauri ta durkusa ta kwala kiran Yaya.  Tare suka shigo da sabuwar me aikin ta da mama ta kawo mata bayan Godiya, da sauri ta fita tace a kunna mota dan har Jiddan ta kai kasa saboda wani irin murdawa da cikin ta yayi ga wani irin ciwon mara da ya taso mata gadangadan. Yaya ce ta riketa tana mata sannu, Godiya taje da sauri ta sau waya ta kira Aunty ta fada mata, sai ta aika Usman tace ya fadowa Mama aikowa mayafi kawai ta yafa ta fito, kafin taje sun wuce asibiti sai ta bisu chan din.

  Cikin ikon Allah ana zuwa ba'a fi minti talatin ba Jidda ta haihu haihuwa me sauki kuma lafiya lou dan ko karuwa batayi ba. Murna a wajen Mama tayi saurin kiran Anty t fada mata sannan ta kira Baba shi kuma ya kira Tariq yana tsaka da shirin tahowa dan ranar zai baro kasar sai ga kyakkyawan labari. Sujuduj shukur yayi yana kara godiya Allah da ya sauke ta lafiya.


  Mace aka samu me kama daya sak da Jiddan har farin kamar dai yadda Tariq din kullum yake jaddada mata me kama da ita yake so. Nan da nan asibitin ya cika da su Anty,  Amira, Ya Safiyya da babyn ta haka ma Umaima, Ya Fauwaz da matarsa. Maryam ce kawai bata nan tana Kano amma an kirata an fada mata. Baba ne yazo yaga sabuwar amaryar tasa wadda Yaya ta rike ta kam ta hana kowa sai dai Ka kalle ta a hannun ta, Baba kawai ta bari ya dauka shi da abokin sa amma daga su bata sake barin kowa ba. Kasancewar kalou aka haihu yasa basu kara awa daya ba aka sallame su. Gida aka wuce da ita part din Mama in da dama tun kafin haihuwar tasa aka gyara mata dakin dan so take ta kara wanke kanta a wajen Tariq din da Baba har ma da Jiddan.


    ***Tana zaune bayan anyi ma jarirriyar wanka yamma Mama tazo tace ta taso ruwa ya yi, tashi tayi ta dora towel a saman kanta ta shiga toilet din, Maman ce da kanta tayi mata wankan towel din ta gasa masa jikin ta sosai sannan ta nuna mata yadda zatayi tsarki sosai, ta fita ta barta taje ta kunna bunner a dakin sai ga Anty ta shigo ta dauki babyn ta fito da ita falon wajen bakin da akayi.

  Farfesu me zafi aka kawo mata Maman da kanta tasa ta taci sosai sannan ta bata magungunan ta tace ta kwanta ta huta sosai ta fita ta jawo mata kofar dakin. 

  Ta dade sosai tana baccin cikin baccin taji kamar ana shafa mata fuskar ta, bud'e idon ta tayi dake cike da bacci ta ganshi yayi kneel down a gaban ta yana kallon ta cike da tsantsar tausayin ta. Da sauri ta tashi tana bude baki, sai ta rungume shi cike da farin cikin ganin sa


"Jidda nah!" Ya furta yana kara rungume ta sosai


"Thank you so much, nagode nagode nagode, kin gama min komai a duniyar nan da kika haifa min Princess dita."


Gefen ta, ta kalla jarirriyar na ajiye a kusa da ita tana bacci, ya dade da shigowa yana kallon su cike da so da kauna, ji yake kamar ya hadiye su saboda kauna.


"Kin ganta ko? Kamar ku daya har idon naki ne Baby."


"Haka nima nake?"


"Sosai."


"Amma kalli fingers dinta irin naka ne."


"Na gani Jidda, Allah kenan, Allah ya raya mana ita yayi mata albarka, I love you so much."


"I love you so so so much." 


Ta maida masa tana sake hugging dinsa


"Kayi mata huduba?"


"Yes! Na saka mata Halimatussadiya."


"Da gaske?" Ta waro idon ta


"Da gaske, Anty ta chanchanci fiye da haka."


"Nagode nagode nagode mijina."


"Shssh, babu godiya a tsakanin mu, ina sonki sosai fiye da yadda nake son kai na, zan iya yin komai saboda farin cikin ki."


"Inason ka sosai, beyond words! Allah ya barmu tare har karshen rayuwar mu."


"Amin Ya Allah!"


"What next?" Yace yana bude hannun sa


"A very beautiful beginning in sha Allah."


"Zaa bude sabon chapter rayuwar Jidda da Tariq."


"In sha Allah."


Tace tana sake kwanciya a jikin sa.

ALHAMDULILLAH!!! TAMMAT!!!

  


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links