SANADIN LABARINA 50


    Page (50)


***A zaune Mama take kan ta yayi masifar daukar zafi, ta rasa yadda zata bullowa al'amarin gashi dole ba zata karyata Nafin ba ta zabi Tariq, tasan ba zai aikata ba, bata so kuma maganar ta kai wajen Baba dan tasan dama a ciki yake da ita, kuma zai ce menene dalilin tura yaran gidan Tariq din. Dakin da Nafi take ciki da Salmar ta tashi ta shiga, ta same su sun yi jingum jingum.


"Magana zamuyi Nafi."


"Maganar me Yaya? Bayan kin goyi bayan danki saboda ita Salmar ba taki bace ba."


"Ba haka bane ba, ban goyi bayan sa ba amma kuma ina tantamar Tariq da aikata irin wannan laifin, duk da an ce ba'a shaidar d'a."


"Dama a duk irin wannan abun mace ake cuta, yanzu shikenan haka za'a bar maganar? Ni da ban zafafa ba idan ma hakan ne ai shi sai ya aureta tunda shine ya fara bata ta."


Runtse ido Mama tayi maganar na shigar ta kamar an soka mata mashi, girgiza kai tayi ta karaso ciki ta zauna sosai tana kallon Salma


"Da yaushe da yaushe ne hakan ta faru? Kuma ke kadai ce a wajen ko tare kuke da Amira?"


Kallon uwarta tayi sai kuma ta kalli Maman


"Tun anan gidan ne."


"Yanzu me kike so ayi Nafi?"


"MU rufawa juna asiri, ki saka Tariq ya auri Salma kawai, kinga shikenan mun rufe asirin juna tunda dai ai uwa daya uba daya ba wasa bane."


"Shikenan, zan masa magana."


Sai ta mike


"Mu bar maganar a tsakaninmu dan Allah, har zuwa lokacin da zamu samu bakin zaren."


"Ba matsala."


Fita tayi ta ja musu kofar, da sauri Salma ta tashi ta rungume Aunty Nafi tana kyalkyala dariya


"Ke da kin tsaya sokwanta, ina neman miki inda zaki huta kiji dadi, Allah na tuba gida be koshi ba zaa kai dawa ne? Itama Yayar duk da ita amma dama ina kai ina bari kishiya ta mallake ma da, in dai Tariq ya aure ki Jidda ta zama sorry wallahi, dan sai mun kore ta da kafarta"


"Allah Mami bana son yarinyar nan,."


"Ni kaina ba sonta nake ba,amma tunda uwar Tariq zata sashi auren ki ai dole ma ta tattara tayi gaba dan kin ganni nan? Bana zama da kishiya kuma ban taba bora ba, shi kanshi Babanku da matar sa na same shi amma wallahi da kanta ta nemi saki tayi gaba, ba zata iya ba."


"Yanzu Jiddan ma zata tafi?"


"Dolen ta, ai barewa ba zatayi gudu dan ta yayi rarrafe ba, duk abinda ake dan su wa ma tukunna ake yi? Dan 'yaya ne dama."


"Shiyasa nake son ki Mami na."


"Ki saki jikinki kamar anyi an gama, sannan ki cigaba da acting din da nace miki dan hankalin Maman ya cigaba da tashi, idan yaso kinga zata fi daukar mataki dan tana tsoron magaanar ta kai wajen Baban."


"zan cigaba kuwa."


"Good, haka nake son ji."


Da sauri Mama ta bar jikin kofar bayan ta gama jin komai, dama chan bata yarda da maganar ba dan tasan halin Nafi sarai zata iya shirya komai, kuma dama bata taba sha'awar Tariq din ya auri Salma dan sak halin uwarta take dashi, duk da bata son Jidda amma a yanzu sai take jin gwara Jiddan sau dubu akan Salmar.

    Zama tayi tana tunanin mafita, sai ga Fauwaz ya shigo, dakin ta suka shiga ya zauna sannan ta karanta masa komai da taji.


"Mah wai dama kin yarda ne?"


"A ah Fauwaz, kawai bansan wanne irin tunani zanyi ba."


"Toh wallahi ko kaffara ba zan ba Ya Tariq ko kallo bata ishe shi ba, bare har akai ga haka, kawai dai sharri suke son masa, muka mah ba dan ke ba nasan Ya Tariq sai ya rufe su wallahi."


"Naga yadda ransa ya baci sosai wallahi, shiyasa da yace su fita nace muje dan nima zama na bashi da amfani."


"Amma me yasa bakya son Jidda Mama? Wallahi Jidda bata da matsala kuma nasan zata chanja Ya Tariq fiye da yadda muke tunani,."


"Kawai bana son ta ne, a bar maganar."


"Yanzu toh me ya kamata ayi?"


"Nasan me zanyi."


"Shikenan, Umaima ta kira wai aakai mata wasu kayan ta."


"Eh Amira ta fada min, sai suje anjima da Maryam driver ya kaisu."


"Ok."


Wayar ta ce tayi kara Fauwaz dake gefen ta, ya miko mata.


"Baba ne, ko sun sauka?" 


Tace tana daga wayar. Gajeriyar magana sukayi yace yana daf da shigowa gidan, tashi tayi tabi ta kofar baya zuwa shashen shi kuma Fauwaz yayi relazing a cikin kujerar yana karo volume din TV. Salma ce ta fito tazo ta zauna tana kin kallon sa, tashi yayi ya zauna yana ajiye wayar hannun sa a gefen sa


"Amaryar Ya Tariq." 


Da sauri ta waigo ta kalle shi, ya kashe mata ido daya yana dariya


"Ashe kinsan sunan ki, sunan kuma yayi daidai dake fa."


"Ya Fauwaz banda tsokana."


"Kai I'm serious fa, Amma kinsan me?"


"A ah sai ka fada."


"Ki kyale shi kawai ki dawo kaina gani handsome guy ga naira gani single."


Tsuke bakin ta, tayi ganin kamar raina mata wake son yi


"Allah kuwa, gwara ki kama saurayi kamar ni bashi da yake da mata ba, kuma wallahi baya son ki..."


"Kuma ba zai taba son ki ba, kinsan mu maza mun fi son mace me aji ba wanda take tura mana kanta ta karfi da yaji ba, sam ba aji bare daraja! Darajeless wallahi." 


Ya sake fashewa da dariya, cika tayi fam ta kasa bude baki bare ta maida masa, mikewa yayi yana tattare key din sa da wayar sa ya zo gaban ta ya karkad'a mata key din a fuska


"Duk sanda kika shirya ki tura application dinki zan duba naga ko zan iya manage."


Tana kallo yayi ficewar sa daga falon, ta tashi da sauri ta shiga ciki kuka na taso mata, kukan bakin cikin da ya guma mata kuma ta kasa bude baki ta rama.

  Wajen Yaya yayi wucewar sa ya sameta kamar ko yaushe tana kulla lalle a kafarta, jan kafar yayi ta kai masa duka da hannun da yake daure da leda da tsumma.


"Jairi.",


"Ni dai idan dan ni kike kunshin nan na yafe wallahi, nafi son kafar taki a haka a dan ya mushe."


"Sai dai kafar matar kace a yamushe ba dai tawa ba."


"Ina da wata matar ne bayan ke gimbiya?"


"Uwar gimbiya, munafuki ai naji abinda kaje kana yadawa wai naje gidan Jidda Tariq ya wulakanta ni."


"Ni? Waye ya fada? Karya ake min."


"Kai tafi chan, ai duk abinda kaje kana cewa ya dawo kunne na tas!"


"So dai ake a hada MASOYA biyu, ki cire lallen nan kizo muje gidan Ya Tariq din muci girkin amarya, sai na barki ko kwana biyu kiyi dan naga alamar kina son zuwa."


"Allah ya tsare ni da zuwa gidan nan,marasa kunya kawai, kai ma ko auren kayi bani ba gidan ka."


"Toh ai bani da wata matar bayan ke."


"Mutan garin ku Fauwaz."


 Baba yace yana shigowa, sosa keya ya hau yi ya durkusa ya gaida Baban ya amsa yana murmushi, 


"Ka raina min uwata ko? Toh kaima sai an raina taka."


"Ba haka bane Baba."


"Ai wannan yaron ya maida ni kakar sa wallahi."


"Rabu dashi Yaya, yaran yanzu ne sai hakuri."


"Ko da yake ai gwara shi, shi wanchan da naje gidan sa ai kora da hali yayi min."


"Wai Tariq?"


"Shi fa, daga shi har Jiddan ashe fitsararru ne ban sani ba, jiran ta nake ai tazo har nan ta samen, taji maganganu wallahi."


Murmushi kawai Baba yayi yace


"Yaya kenan, Ina wuni, mun same ku lafiya?"


"Lafiya lou wallahi, ya hanyar? Hankali yayi gaba ashe ko gaisawa bamuyi, gashi ba hannu bare na miko ma ruwa."


"Karki wahala ma Yaya, tun safe muka dawo wani abun ne ya rike mu."


"Toh Masha Allahu, Allah dai ya bada sa'ar abinda ake nema ya raba ku da makiyanku lafiya yasa a gama lafiya."


"Amin Amin Yaya, addu'ar kenan."



***Tana nade a cikin blanket ya dauki towel ya daura a kugun sa fuskar sa fes gaba daya bacin ran da yake ciki ya neme shi ya rasa,sai farin ciki da ya mamaye ilahirin zuciyar sa. Jidda ta biya shi har da kari dan duk hasashen shi baya taba hasaso hakan sai yau da ya tsinci kansa a cikin duniyar Jiddan me cike da abun mamaki. Takowa yayi ya tsaya a saitin kanta ya dan runkwafo ya shafi gefen fuskar ta da hannun sa ta maze taki ko motsawa.


"Nace fa i'm sorry ba zan sake ba." 


Muskuta jikin ta tayi,taki kallon shashen da yake, murmushi yayi ya sa hannu zai yaye bargon ta rike gam tana bud'e masa idon ta


"Muje na miki wanka."


"Ni bana so."


 Tace kwalla na biyo gefen fuskar ta, dan ba karamin wahala tasha ba sai tace ma yafi mata first time din wahala


"Karki zama raguwa mana, tashi kinji? Na daina ba zan kuma yi ba."


"Ni ka daina kulani."


"Toh tashi ki yi wanka ki rakani wajen Baba, if not aka tambaye ni zance kina gida kina kuka dan nayi..."


"Na shiga uku, naji toh zan tashi, ka tafi."


"Um um, nayi googling yadda ake so kuyi, let me help you kar azo a samu matsala, dan bana wasa da wannan sweet place din." 


Ya karashe yana dage mata gira daya ya lashi gefen lips dinsa, juyar da kanta tayi mamakin rashin ta idon sa na sake cikata


"Wai dama kana magana sosai?"


Ta tambaye shi bayan ta sauko da kafafuwanta jikinta a nannade da blanket din. Dariya tambayar ta bashi dan shi kansa yasan yayi baki idan yana tare da ita, dan murmusawa yayi k'adan ya kama hannun ta ya mikar da ita, ta danyi kara kad'an yayi saurin jawo ta jikin sa.


"Menene?"


"Kafata ce take min ciwo."


"Sannu, lets take our bath sai na miki massage."


"Ka fara yi sai nayi."


"Tare zamuyi."


"Eh???"


"Yes! Sunnah ce, Manzon ALLAH (SAW) ya kasance yana wanka tare da matan sa (Allah ya yarda dasu.)"


Shiru tayi jin irin misalin da ya kawo wanda bata isa ta ja ko ta noke ba. Kama blanket din ya yi ya cire ya daura mata dan karamin towel iya cinya ya sakata a gaba har toilet din.  Da kansa ya hada mata ruwa da dan salt kad'an yace ta shiga shi kuma ya tsaya gaban sink ya dau brush ya soma brushing bakin sa. Bata da yadda zatayi haka ta shiga duk da dama jiyan ma ta shiga dan babu abinda aunty bata fada mata ba tun kafin ma ranar, kuma har text message sai da tayi mata ta sake jaddada mata. 

  Kusan 15mint ta dauka a ruwan sannan ya taimaka mata ta fito ya jata cikin whirlpool bath tub da ya cika musu da ruwa, idon ta a rufe duk kunya ta hanata sakat amma shi kamar ko a jikin sa, haka suka shiga tare tana nokewa tana komai amma ya hanata katabus, cikin wani irin salo ya dinga tafi da ita, ta kasa hanashi dan sosai take karbar sakonnin da yake aika mata. Kamar yadda da jini yake bi ya kai sako zuwa kwakwalwa haka sakon sa ya dinga zuwa matar har chan cikin kanta. 

 Kusan minti talatin suka dauka kafin ya fito da ita tamkar karamar baby, ya ajiye ta sannan ya taimaka mata ta ya shirya ta cikin riga da skirt na atamfa shi kuma yasa wani yadi me laushi ya dora hula shigar da ba kasafai yake yin ta ba, kuma ba karamin fito da ainhin kyawun sa take ba. Tana zaune tana admiring abin ta, tasan kawai ALLAH ne ya bata ba wai dan ta kai matsayin ba, amma ta ko ina Tariq din lamba daya ne, duk da ko dazu sai da ya kara jaddada mata how lucky he is to have her amma kuma tasan ita ta fishi zama lucky din, kawai dai shi namiji ne shiyasa. Mayafi ya dauko mata da handbag tunda ya hanata yin komai, ya yafa mata da kansa dan hatta gashin kanta shi ya gyara mata shi ya saka mata wayar ta a handbag din ya rike sannan yace su tafi.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links