SANADIN LABARINA 54


  Page (54)


***Sun jima a gidan Hajiya babba fiye da yadda tayi zato ko tsammani, suna daki sai ga aunty Mimi ya shigo cike da murnar ganin Jiddan wadda ita tayi duk kokarin ta wajn wayarwa da Hajiya Babba kai akan Jiddan da yanayin halin kirkin ta, a dah su Nafi sun fanfa ta amma da Anty Mimin ta yi mata bayani sai taji ta sauka sosai, har ma tana son Jiddan shiyasa da tazo tayi mata tarbar da Jiddan batayi tunani ba. 

  Sun fito zasu tafi bayan an saka mata kyautar Hajiya Babba a booth suna sake yin sallama sai ga Anty Nafi da Salma sun shigo a motar Anty Nafin driver ya kawo su, kallo daya Tariq yayi musu suna shigowa ya dauke kansa ya shiga motar sannan ya zuro kafafuwan sa waje yana zaro wayar sa, maganar da Hajiya babba tayi masa kenan a ciki akan maganar Anty Nafin da abinda ya faru yayi mata bayanin komai shine ta kira tace su zo ita da Salma sai gasu sun iso dan dawowar su kenan ma daga Abujan ko kaya basu chanja ba suka fito dan dama ko hajiyar bata kirata ba tayi niyyar zartowa tazo ta fada mata irin wulakancin da Mama tayi mata akan Tariq. Mamakin ganin Tariq din da Jidda a gidan yasa ta fitowa da dan sauri bayan ko gama parking daidai driver be ba.


"Tariq dai kaki barin Jidda da tayi zaman ta anan ai, Hajiya ma zata ji dadi."


"Anty zamu dawo, yanz akwai in da zamuje daga nan ne."


"Toh shikenan, sai kun dawo din."


"Sai anjima Anty Mimi."


"Sai anjima Jidda, bye."


Baya ta shiga shi kuma dama yana gaba tare da driver sai dayar motar da take bin su, suka fita daga gidan yana kallon mirror din gaba yaga sanda Anty Nafin ta karaso tana kallon motar tasu ita ma yar iskar yarinyar idon ta akan motar. Shafa kansa yayi yana jin wani dum kamar wanda yayi wani babban aiki. Direct gida aka wuce dasu daga nan. Gidan da ma'aikata masu kula da gidan dan yanzu yawanci Baba anan yake weekends kuma mafi yawancin lokuta tare suka zuwa da Mama dan itace me sabgar yi ga shagunan ta dan ma fauwaz shine karfin kula da duk wasu business dinta shiyasa ko yaushe yana tsakanin Kano din da Abuja yana duba yadda abubuwan suke tafiya.

  Daga bq ta fito ta bawa Jidda key din part din nasu da aka sake gyara shi dazu, mika masa tayi ya karba yana amsa waya ya bude sannn ya matsa mata ta shiga sannan shima ya shiga yana jan suitcase din su zuwa ciki yana cigaba da wayar sa. Ta rasa gane dalilin sauyawar sa lokaci d'aya, duk da haka suna yawan had'a ido amma sai ya fuske yana cigaba da wayar da take tunanin kamar da gayya yake jan hirar. Kayan nasu ta dauka tayi ciki tana kallon sanda ya bita da kallo. A gefe ta ajiye kayan tana karewa bedroom din kallo me dauke da hadadden royal bed din da aka sakawa red bedsheet me zanen heart. A gefe ta zauna ta fito da charger ta, ta jona wayar ta sannan ta nufi toilet din dake manne a falon. Wanka ta fara yi sannan ta dauro alwala ta fito daure da towel Babba. A wajen kayan su ta ganshi yana duba abu, tayi kamar bata ganshi ba saboda rashin kayan dake jikin ta, kad'an ya kalle ta sai tayi tunanin zai mata magana amma kuma sai ya cigaba da abinda yake kamar shima be ganta ba. Juyawa yayi ya fita, jiki a sanyaye ta shirya ta yi sallah sannan tazo ta dauki wayar ta,ta kira  Safeera dan taga kiran ta sanda suna gidan Hajiya Babba .

   Suna cikin wayar ya shigo sanye da  dogon wando fari da t-shirt kamshin turaren sa ya cika dakin daga gani wanka yayi babu ko tantama. A gefen ta ya zauna ya saka hannu ya zare mata wayar daga kunne sannan ya katse kiran yana kallon ta 


"Haka ake lallaba miji?" 


Ya kalle ta rike da wayar bayan yaga da wadda suke yin wayar.


"Na'am?" Tace a dan kaikaice tana kokarin hana idanun sa tasiri akanta 


"Eh, haka akeyi? Baki san fushi nayi ba?"


"Fushi? Me yasa?"


"I'm jealous, kishi nake and you just pretend as if baki gani ba ma."


"Kayi hakuri."


"Ai kinji... A dake ka a hana ka kuka, ayi maka laifi a yi saurin baka hakuri da kazo zakayi yar mitar ka."


"I'm so sorry ba zan kara ba.”


“Ni ba zan hakura ba!” 


“Please…”


“Sai da sharadi idan kinaso na hakura.”


Kallon shi tayi ya kashe mata ido


“Sai kin saka min rigar nan kin yi fashion parade sannan zan hakura.”


“Innalillah!”


“Yea! Idan ba haka ba nayi ta fushi na daina kulaki!” 


 Ya juyar da kansa gefe daya yana turo baki kamar karamin yaro.


“Shikenan zanyi, amma sai dai anjima!”


Juyowa yayi yana murmushi


“Why not now? Me yasa sai anjima?”


“Ni dai kawai.”


“Shikenan I will wait! Amma karma kizo min da wani excuse wallahi. Inaso naga matata ehe.”


“Tell me, waye wannan ismail din? How much did he know about you?”


“Ba zamu kyale maganar ba?”


“No it’s better ayi ta kawai Jiddaaaa.” 


“Ok, yayan Safeera ne, both of them helped me alot a rayuwa ta, sun so ni a yar kauye ta da rama ta, basu taba kushe ni ba ko aibata ni.”


“OMG!” Yace yana kokarin rike ta, ta dan matsa kadan tana kin kallon sa


“He nuna interest akaina and I said no, be takura min ba, he left daga nan aka daura min aure, and I waited for good 1year, since then ban sake ganin sa ba coz dama a time din ya tafi karatu, this is the first time bayan long time da na ganshi, and yasan nayi aure, kuma nasan babu wani abu a ransa.”


“Jiddah!” 


Ya kira  ta ganin yadda mood dinta ya sauya. He misunderstood everything yazo yana ta fushi akan iska. Kin kallon sa tayi saboda yadda idanun ta suka cicciko zatayi kuka. Juyowa da ita yayi suna kallon juna, tayi saurin sauke kanta kasa ya sa hannu ya tallafo fuskar ta.


“I’m so sorry kinji? Dan Allah Kiyi hakuri ki daina tuna abinda ya wuce, nayi kuskuren fadan abubuwan chan Amma wallahi wallahi ba har zuciya ta ba, I was just looking for an excuse to hold on to, ba nayi ne don cin fuska ba, dan Allah forgive me! Wallhi nayi regretting, I regret everything har rashin dawowa ta,forgive me dan Allah!”


Kuka tasa masa ya jawota jikinsa ya rungume zuciyar sa na wani irin zafi, yasan zata dade bata manta ba, bayan ka zauna zaman jiran mutum ba shekara daya amma ya dawo yace baya son ka, dole da ciwo ontop of that kuma ma ya hada da kushe ka, dama zai iya dawo da lokacin baya ya goge duk abinda yace din, Amma Yanzu kam it’s too late. Ta dan dade tana kukan kafin tayi shiru sai ajiyar zuciya da take a hankali, tana da saurin kuka karamin abu yanzun nan zai sakata kuka sosai, bayan ta yake tapping a hankali ya kasa ce mata komai har tayi shiru din. D’ago ta yayi yana kallon yar fuskar tata, hannun sa yasa ya goge mata ragowar hawayen da take ya shafi saman lips dinta da yake ganin shine kawai last option dinsa da zai yi amfani wajen sake bata hakuri.


“I’m sorry.” 


Yace muryar sa ta shige ciki sosai. Sai ya matso da fuskar sa daf da tata, ya dora hanci sa a saman nata yana gogawa kadan kadan yana kokarin saka mata idonsa a cikin nata saboda taga how sorry he is, a hankali ya kai bakin sa saman nata ya hade su waje daya, sannan ya sa hannun sa ya zagaye ta cikin ta ya matso da ita so so close.

  Kusan minti biyu ya dauka yana kissing dinta a hankali, kafin ya cikata yana maida kansa ya hade goshin su waje daya, idon ta a rufe yake jikinta yayi wani irin sanyi, ya riga ya gano lagon ta. Kissing aaman 


“Please Kiyi hakuri, ki daina tunawa kinji? Ya wuce ba zan sake ba. I love you so very much, bansan irin son da nake miki ba wallahi! Kukan ki is one of my weaknesses dan Allah ki daina kinji?”


G’id’a mishi kai tayi, ya rike hannun ta yana mata murmushi


“Did you love me?” 


Ya tambaye ta for the first time cike da tsoron kar tace masa a ah.


“Umm? Kina son Ya Tariq dinki?”


“Eh…” ta daga kanta kunya na cikata 


“Yes! Say it naji, pleaseee.”


Kasawa tayi, ta boye kanta a kirjin sa tana dariya kadan kadan


“Kunya kike ji?”


“Umm…”


“Ni dai sai kin fada min naji.”


“Ba zan iya ba.”


“Zaki iya, pleaseeee!”


Yawun bakinta ta tattaro fuskar ta har lokacin na cikin kirjin sa,


“Na rufe ido na, inajinki fada mjn, tell me you love me.”


Dagawa tayi kadan taga ya kulle idon sa, kallon fuskar ta dinga yi tana admiring din ta, ta dan kai hannu kadan ta taba gefen sajen sa, ya rike hannun yayi kissing dinsu still idon sa na a rufe 


“I’m waiting…”


“I love you so much.” Tace da sauri kamar wadda aka tunkuda. Dariya ta bashi amma sai ya kanne ya bude idon sa 


“Wow! I love you more baby.” Yace yana mata murmushi

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links