SANADIN LABARINA 48


    Page (48)A hankali yanayin fuskar sa ya shiga chanjawa zuwa tsananin bacin rai, cikin kankanin lokaci kamannin sa suka sauya ya koma tamkar wanda be taba dariya ko murmushi ba a rayuwar sa, kallon yarinyar yake yana jin zai iya kakkaryata ya zubar a wajen idan har ya biyewa zuciyar sa.


"Baka ce komai ba." Mama tace tana kallon sa


"Me zai ce? Bashi da abin cewa ai, ni wallahi an cuce ni wallahi an cuci rayuwa ta." 


Anty Nafi tace tana fashewa da kukan munafurci, be ko kalli in da take ba, ya cigaba da kallon Salman ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa dan kallon nasa ya fara bata tsoro, ba ita ba har Anty Nafin tsoro ya shige ta ganin yadda kirjin sa yake dagawa. 


"Tariq!!!" Mama ta kwala kiran sa, ya juyo a nutse yana kallon ta tar,


"Na'am Mama."


"Baka ji me Salma tace ba?"


"Naji Mama." Yace yana kokarin daidaita calmness dinsa


"Amma ba zaka ce komai ba?"


"Bani da abinda zan ce Mama, in dai har wannan dakikiyar kazamar kuchakar yarinyar nan zata zauna ta tsara wannan maganar kuma ku zo dan tabbatarwa, bani da abinda zance akai."


"Tariq karka yi kokarin chanja maganar nan, kasan dai Salma ba zata maka karya ba ko?" Anty Nafi ta fada ganin kamar yanayin da yake ciki ya sassauta 


"Da mahaifiyata nake magana ban sa dake ba!" 


Yace mata a fusace, da karfi. Tsit tayi bata kuma cewa komai ba, ya maida hankalin sa kan Mama ya cigaba da magana


"Idan har yarinyar nan ta kara minti daya a gidan nan wallahi wallahi sai na ajiye alaka da komai na kakkaryata na zubar a wajen nan,."


"Saboda baka son gaskiya ko? Wallahi ba zan yarda dake ni sannan a hanani kuka ba, wallahi mahaifin ka zan gyayawa, ko ka auri Salma wallahi ko na fada masa, kunsan dai dan siyasa ne baya so sunan sa ya baci ko?"


"To hell with you!" Ya dake mata tsawa


"Ki fadawa duk wanda zaki fadawa wallahi, I don't care!" 


"Fauwaz, take them out."


"Calm down Ya Tariq."


"Su fita nace!"


"Tashi Nafi, ma karasa maganar a gida." Mama tace tana kallon yadda yake huci 


"Dole ya auri Salma wallahi dan ba zai lallata min rayuwar yarinya kuma yazo yace ba zai aure ta ba."


"Muje." 


Tashi tayi tana cigaba da kumfar baki, Jidda da tun dazu take jin muryar sa a sama ce ta lallabo ta fito sanye da rigar sa sai yar hular da ta rufe gashin kanta,sun tashi kenan ta fito kallo ya dawo kanta, da sauri ta juya zata koma a tunanin ta basu ganta ba, sai jin Fauwaz tayi ya kira sunan ta


"Aunty jidda."


Tsayawa tayi ta juyo cikin matsananciyar kunya ta karaso falon ta duk'a kad'an tace


"Ina kwana?" 


A gajarce Maman ta amsa tana kauda kanta dan kallo daya tayi wa Jiddan ta gano wani abu, Anty Nafi ta gaisar amma bata amsa ba sai Salma da ta banka mata harara, suka fice daga falon ya rage saura Tariq din da Fauwaz, zama Tariq din yayi yana tallafe kansa da hannayen sa biyu.


"Ya Fauwaz ina kwana?"


"Lafiya lou Jidda, pls ki kula da Ya Tariq bari na dawo."


Sai ya juya shima ya fice daga falon ya same su har sun shiga mota.


A gaban sa tayi kamar kneel down tana kallon hannun sa da ya tallafe fuskar sa dashi, hannu tasa ta kama hannun nasa ya dago idanun sa da suka rini sukayi jajawur ya zuba mata tsoro ya kamata ganin yadda suka koma.


"Ya kike jin jikinki?" Ya fada muryar sa a dashe kamar wanda yasha wani abu


"Naji sauki." 


"Ok."


"Baka da lafiya ne?"


"I'm furious Jiddaaaa."


Sai ya saka hannu ya jawo ta jikin sa, ya rungume ta ko zai samu saukin abinda yake ji.


    Fauwaz ne ya dawo ciki sannan ya cikata yana gyara mata jikin rigar


"Jeki ciki kinji? Karki damu."


Jiki a sanyaye ta shige ciki ya kalli Fauwaz yana tashi tsaye


"Ya za'a yi Ya Tariq? Menene abun yi? Kasan irin wannan sharrin issue ne very complicated, sannan kamar bata sunan mutum ne, hatta Baba idan abun nan ya fita sai sunan sa ya baci sosai duk da ba gaskiya bane."


"Fauwaz I don't care duk abinda duniya zata ce wallahi, this is a great lesson da ya kamata Mama ta dauka, da tun farko ba'a turo yarinyar nan gidan nan ba, ya hakan zata faru? But sai ta biyewa Anty Nafi which ita da kanta tasan how evil that woman is, duk saboda kishi, kishin da bashi da maaana bare tushe."


"But Aunty Nafi zata iya aikata komai to tarnish your reputation in dai har bukatar ta zata biya."


"Har abadah wallahi, kuma in dai ta cigaba da pushing akan maganar nan wallahi sai na bata mamaki ita da ballagazar yar ta."


"Calm down dan Allah, don't frustrate your self mu zauna a samu solution."


"Ba wani solution Fauwaz, tunda hakan suke so hakan za'a yi, muga wanda zai fasa ni dasu."


"Amma idan suka samu Baba da maganar fa? Kana ganin zai yarda?"


"I can't say ko zai yarda ko bazai yarda ba wallahi, ni dai tunda nasan ban aikata ba shikenan." Yayi maganar yana yarfa hannun sa gefe daya cikin bacin rai 


"Nasan kana cikin bacin rai."


"Very! Kasan yadda sharri yake kuwa? Sharri irin wannan? ba zaka gane ba."


"I totally understand, nasan yadda kake ji, it's not easy amma kayi hakuri dan Allah, mu bi komai a sannu wasu matan are cunning yadda baka taba tunani, shaidan haka suke wallahi."


"Allah ya kyauta."


"Amin ya Allah, inaga bari naje duk yadda ake ciki zan fada maka."


"Ok thank you." Ya mika masa hannu sukayi musabiha sannan ya tafi shi kuma ya cigaba da zama a wajen ya kasa mikewa bare ya shiga ciki.


   ***Tunanin abinda ya kawo Maaman take tunda ta koma duk da taga Salma ta kuma san kila akan abinda ya faru jiya ne amma kuma ai be ci ace har sai Maman sunzo da kanta ba, bacin ran dake fuskar Ya Tariq din yasa ta tabbatar akwai matsala babba, wanda ta alakanta da yadda Maman bata son auren su. Shiru shiru be shigo ba gashi bata son komawa ko basu gama maganar ba, zama tayi ta cigaba da jiran sa har ta gaji ta shiga wanka tana fitowa ta ganshi yana duba wasu takardu, dagowa yayi ya kalle ta kad'an ya cigaba da abinda yake yi, wucewa tayi ta dauki kaya a closet ta saka daidai lokacin ya fice daga dakin ya dauki system dinsa ya fara yi mata processing visa!


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links