SANADIN LABARINA 45


      Page (45)***Ruwa ya kawo mata ya taimaka mata ta sha ya ajiye yana hawa gadon. A hankali kukan da take ya dauke ya koma sai ajiyar zuciya da take saboda azabar da tasha, sanyi taji na ratsa ta, nan da nan ta soma rawar sanyi ya tashi ya kashe AC ya rage fan din, amma duk da haka bata daina ba, sosai zazzabin ya rafke ta wanda dama take ta jin alamun sa tun jiya amma ta daure sai gashi ya taso lokaci daya dalilin gyaran. 
"Jikinki yayi zafi sosai." Yace yana kama hannun rigar ya zare mata shi, da sauri ta kalle shi shima ita yake kallo, ya girgiza mata kansa ya karasa zare mata rigar baki daya, wani irin yarrr yaji tun daka kansa har zuwa tafin kafafunsa, ya ja ajiyar zuciya ya daure ya ja karamin blanket ya rufa mata a daidai cikin ta zuwa saman chest dinta, idon ta dake a runtse tunda ya janye rigar ta dan bud'e taga ya dauka daga kan gadon, ya cire rigar dake jikin sa har singlet din, saurin maida idon tayi ta rufe tana jin sa ya hawo hadon ya jawo ta jikinsa ya gyara mata kwanciyar, zafin da jikinta yayi ya hadu ya chakude da bare fatar sa. Wani irin yanayi suka samu kansu a ciki musamman shi, ji yayi baki daya duniyar na juya masa, komai ya tsaya chak hatta bugun zuciyar sa ya karu da kaso me yawan gaske. A hankali zazzabin ya dinga raguwa har ya zama sai dan dumi kad'an.
"Gumi nake."
 Tace sai ya sassauta rikon da yayi mata amma ba dukka ba, kanta na jikin kirjin shi tana jin yadda bugun zuciyar sa ke tsere, zufa na cigaba da keto mata ga wata matsananciyar kunya da ta rufe ta, dan babu komai a saman ta sai bra wadda itama kusan rabin kirjinta a waje yake saboda yadda karfen dake rige ta ya zare garin cire zip din rigar. Ta kasa motsi ko kad'an dan ko yaya ta motsa chest dinta zai iya haduwa da jikin sa.
"Are you feeling better?" 
Ya tambaya da k'yar bayan ya daure yayi maganar dan hatta yawun bakin sa ya dauke da k'yar ya nemo shi, be taba samun kansa a irin wannan yanayin ba, shiyasa duk ya kasa controling kansa, wani irin heavy feeling yake ji gashi baya so a samu matsala. Da ka ta amsa masa sai ya zare jikin sa a kasalance ya tashi yana kin kallon ta, duk da dama idonta a rufe yake ita, ya dauki rigar sa ya zura ya shige toilet, mikewa tayi da k'yar ta yi kokarin gyara maballin bra din amma ta kasa, tayi tayi sai kawai ta hakura jin zai fito ta koma ta kwanta tana sake kudundunewa da bargon. Fitowa yayi yana goge kansa da ya jike da ruwa, yana daure da bathrobe alamun wanka yayi, ta k'asan idon ta, take kallon shi ya shafa man sa sai kawai ya zura jallabiya bayan ya fesa turare. Fuskar sa fayau sai dan idonsa da ya dan yi ja kad'an da kansa da yayi masa wani irin nauyi na ban mamaki. Gefen ta ya zauna ya sakar mata murmushi bayan ta bud'e idonta, ya dauki wayar sa yaga text din ban hakuri daga Dr Sufyan da missed calls dinsa, kiran sa yayi ringing daya ya daga yana bashi hakuri
"Ya hakuri captain, muna chan emergency unit wayar na batta anan Dr lounge."
"Ba komai, dama nasan kila kana busy ne, ya aikin?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Masha Allah, dama madam ce ta samu dan targade a kafarta, shine kuma sai zazzabi though da ban sameka ba daga gida an turo irin masu gyaran gargajiya din nan, sai kuma zazzabi daga baya."
"Ayya Allah sarki, kaji tsautsayi, Allah ya bata lafiya, bari sai Dr Amina tazo ta duba ta, ina fatan dai ba aiki ka jikawa yar mutane ba, tsohon tuzuru."
Da sauri Tariq ya kalle ta, yaga ta rufe idon ta, amma yasan taji me Sufyan din yace, murmushi yayi kawai yace
"Sai dai tazo din, please tazo da wuri."
"Ok shikenan, ka duba ta please."
"In sha Allah, thank you."
"DM." 
"Zaki yi wanka?" Ya tambaye ta bayan ya gama wayar. Da sauri ta girgiza kanta
"Ina jin sanyi har yanzu."
"Ok Dr Sufyan zai turo colleague dinsa ta duba ki, in sha Allah zaki ji dadin jikinki."
"Thank you."
"Shissh, get well soon kinji? Pleasee."
Gid'a masa kai tayi ya mike ya fice tabi bayan sa da kallo sannan ta sauke ajiyar zuciya.


   Zama yayi a falon yana tunanin abinda ya faru a while ago, wani irin abu me kama da mayen karfe yaji yana fuzgarshi toward her, da ace kalou take yasan ba zai iya resisting ba, yanzu ma kawai managing kawai yake shiyasa ya fito ya barta dan zama waje dayan ba zai yi masa kyau ba, baya so ya kara mata akan wahalar da tasha da kuma wadda take ciki. Be taba tunani ko hasashen getting intimate with her ba sai yau, yau din ma yanzu amma duk da haka zai kara jira, zai jira right time din.


   Ba'a fi 30min da wayar ba Dr Amina ta karaso gidan ta hanyar amfani da address din da Tariq din ya turawa Sufyan din, a waje ta tsaya ta kira number Tariq din ya mike daga zaman da yayi daidai lokacin Salma ta fito ya kalle ta yayi gaba dan shigowa da ita. Fuskar sa a sake ya wuce mata gaba zuwa ciki ya nuna mata kujera ta zauna yace zai kirawo Jiddan, Salma na labe sai ta fito ta zauna a falon suka gaisa da Dr Aminan.


    Bacci ya sameta tana yi, ya rankwafa kanta ya dan taba ta a hankali, da yake baccin ba me nauyi bane sai ta bud'e idon ta, 
"Dr Amina tazo, zaki iya tashi?"
"Eh." Ta daga kanta
"Ok let me help you." Ya mika mata hannu sai ta noke kafada tunowa da tayi bata da riga, kallon ta yayi sai ya tuna
"Ohh, tashi toh ki sa rigar zan jira ki a kofa." Ya juya mata bayan, tashi zaune tayi ta saka rigar a haka, ta tashi tana dosana kafar ta dauki Hijab ta saka ta taka a hankali ta same shi a tsaye, 
"Sannu." 
Yace yana kama hannun ta, suka fito hannun su sarke da juna. Hannun Salma ta kalla zuciyar ta, ta sosu taji kamar ta tashi ta ture Jiddan, da kansa ya taimaka mata ta zauna ya kuma zauna a gefen ta daf da ita har kusan rabin jikinta na nashi, murmushi Dr Amina tayi ta amsa gaisuwar Jiddan tace
"Sannu amarya." 
Murmushi tayi shi kuma da tun fitowar su yaga Salma yace yana kallon ta
"Ki tashi ki bamu waje, we need some privacy."
"Eh?" 
"Kinji ai, excuse please."
Tashi tayi wani kululun bakin ciki na tokare mata a makogwaro, ta wuce fuuu ya ja tsaki yana maida kallon sa kan Dr Amina din
"Dr I think targade tayi sai kuma fever."
"Garin Yaya amarya?"
"Zamewa nayi Dr."
"Bari na gani." 
Hannun ta nuna mata da kafar ta dan taba hannun kad'an tace mata sannu sannan ta fito da magungunan da ta taho dasu ta mikawa Tariq din
"Dama Dr Sufyan ya fada min komai, so ga prescribe drugs din nan, sai kuma ko za'a dau jinin ta sai aje lab a yi mata Serum Pregnancy Test tunda yafi saurin nunawa."
Dauke wuta jidda tayi kunya na lullubeta, shi kansa kunyar yaji amma ya dake yace
"Bana jin Pregnancy issue ne."
"No ai sai an gwada za'a gane Captain."
"When last kika ga period dinki?"
"Na'am?"
"Feel free kinji? Yaushe?"
"Three weeks ago." 
Tace tana hadiya yawu
"Ok, yaushe kike expecting nashi kuma?"
"Ending week d'in nan.".
"Okh Masha Allah, bari mu jira ko zaki missing period din tunda naga mijinki baya so ya taba masa lafiyar jikinki"


   


Dariya sukayi a tare, ya girgiza kansa
"Dr ba haka bane ba, kawai dai..."
 "Shikenan ba damuwa ai, tasha wannan maganin ko ma da akwai pregnancy din ba zai effecting nasa ba, sai wannan da zata shafa Allah ya kara sauki."
"Amin thank you so much."
"Haba haba ba komai, Allah ya kara dankon soyayya."
Sai ta mike
*Bari na koma dan akwai patients sosai."
"Ok, zamuyi magana da Dr Sufyan din akan duk charges din, thank you once again."
"Ok, nagode sosai, amarya Allah ya kara sauki."
"Amin nagode." Tace ta rakata da ido har ta fice shi kuma ya zauna yana mata kallon k'asa-k'asa
"Amarya."
 Yayi mimicking voice dinta, murmushi tayi masa wanda yake sake narkar dashi, ji yake zai iya fasa tafiyar baki daya yayi zaman sa a nan kawai dan baya son yayi nisa da ita ko nan da chan.


   Mama ce ta kirashi a waya tace yazo tana son ganin sa, a dole ya fita ba dan yaso ba, ya barta tana bacci a daki ysa Amira ta dinga duba ta.


   Da la'asar ta tashi sai taji dan dama-dama, ta fito falon ta samesu suna kallo Salma tayi wanka ta sha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau, kuma ba laifi tayi kyau sosai sai dai illa daya kitson attachment din dake kanta da ta zubo dashi gadon bayan ta. Ran Jidda ne ya sosu har taji kishi sosai a ranta amma ta danne dan duk yadda Mama taso ta ga gazawarta zatayi kokari wajen toshe ta. Daki ta koma bayan ta dan zauna kad'an taje ta hada ruwa me zafi ta gasa kafar da hannun sannan tayi wanka ta fito ta shirya cikin hadadden lace din da akayi musu ita da Ya Safiyya da Umaima, sosai ya zauna das a jikin ta ya fito da ainahin kyawun jikin, bata shafa komai a fuskar ta ba sai eye liner da lipstick kadai da ta saka, sai turare da ta fesa sannan ta dawo falon a lokacin Amira ce kawai Salman ta shiga ciki, gud'a Amira tayi ta saki duk da bata iya ba,hakan ya jawo hankalin Salmar ta fito dan ganin abinda ake wa gudar sai taga ashe wai da jidda take, ranta ne ya baci tazo ta zauna a chunkushe
"Na zata ma wani abun kike ma gud'a wallahi, kika saka na fito da sauri,Mtsw."
"Kinsan fa ba zaki gane irin abubuwan nan ba, kin saka bakin hali a ranki da mugun nufi, shiyasa ba zaki taba banbance komai ba." 
"Amira?" Ta ware idon ta ranta na sake baci dan sosai Amiran ta soma kaita makura
"Ni kike fada wa haka?"
"Eh mana, menene abun tsaki dan Allah, jidda fa itace matar gidan nan, dole mu da muke gidan ta muyi respecting hakan, amma kamar ma baki san haka ba, haba!"
"Ban sani ba, tunda ai ba ita ta gina gidan ba ko?"
"Ba ita da gina ba amma dan ita aka gina, beside mace tafi iko akan gida fiye da mijin ta,dan babu me cewa gidan Ya Tariq sai gidan Jidda."
"Kyale ta Amira, karki bata bakin ki dan Allah." 
A kufule Salma tace 
"Ina ruwanki? Bana son shishigi Malama." 
Murmushi Jidda tayi, 
"Kinsan nasan kece kika zubar da mai dazu ko? Sannan na zabi rufa miki asiri  ko?"
"Me yasa zaki rufa min asiri? Ai da kin fada."
"Bana so ki tafi ne ban gama bakanta miki rai ba, baki gama ganin abinda zai saka zuciyar ki bugawa ba."
"Thank you Jidda." 
Amira tace tana jingina mata da hannu, tsaki taja ta mike ta shige daki ta barsu suna mata dariya,a yadda take jin haushin Jidda zata iya yin komai, kuma ba in da zata har sai ta tarwatsa rayuwar Jiddan sai dai kowa ya rasa ayi biyu babu.

 

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links