SANADIN LABARINA 44

   Page (44)

***Dago ta yayi ya tallafo ta jikin sa yana tambayar ta me ya faru?" Hannun ta take nuna masa da yake mata zafi da zugi, hannun ya rike ta yi kara yayi saurin saki, ya dagata sama chak Amira ta matsa ya kai ta tsakiyar falon yana dudubabata. 

"Ina ne yake miki ciwo?" Yace yana kallon hannun nata da yaga tana son motsa yan yatsun, nuna masa hannun tayi tana hawaye, sai babban dan yatsan kafarta ta dama 

"Dukka hannun ne?"

 Ya tambaya yana maida hankalin sa kan kafar tata. Yan yatsun ta biyu ta nuna masa, ya gano tayi targade ne, tausayin ta yaji sosai, ya taimaka mata ta kwanta a cikin doguwar kujerar falon ya mike ya nufi daki don dauko wayar sa. Amira ce take mata sannu, tana kallon gefen rigarta da ya baci da mai

"Mai ne ya zube akan hanyar?" Ta tambaya wani tunani na darsuwa a ranta

"Um um, ni ban sani ba, ban zubar da mai ba ni, da na fito yanzu kuma babu komai, sai da na koma naji na taka mai."

"Salma ta shiga kitchen din ko?" Tace ranta na baci

"Eh."

"Ita ta zubar da man kuma da gayya ta yi wallahi."

"Wace ta zubar da mai?" Yace yana karasowa ciki rike da wayar sa a hannu yana son kiran Dr Sufyan, 

"Na'am?" Ta zaro ido tana mikewa daga durkuson da tayi a gaban Jiddan

"Waye ya zubar?"

"Mai ne inaga ya dan zube a kofar shine ban lura ba na taka."

 Jidda tace tana son dauke maganar 

"Ok."

 Yace yana share maganar kawai, yayi kiran wayar, be same shi ba, sai ya dawo ya zauna a gefen ta ya matso da ita kusa dashi yana kallon hannun yadda yan yatsun suka so ma kumbura haka ma na kafar 

"Sannu, suna ciwo?" 

Daga mishi kai tayi, ya dan taba kad'an tayi kara yayi saurin janye hannun sa

"I'm sorry."

 Mikewa Amira tayi ta bar falon ta samu Salma ta gama shan tea din suna waya da Anty Nafi, a kanta Amira ta tsaya maimakon ta cigaba da wayar sai ta katse tana kallon ta

"Lafiya?"

"Me yasa kika zubar da mai a hanya kinsan Jidda ce zata shiga kitchen din."

"Mai kuma? Yaushe?"

"Oho, kinsan me nake nufi."

"Ni ban zubar da komai ba, karki min sharri."

"Nasan ke kika zuba a hanyar dan ta fadi, toh ta fadi kuma har tayi targade amma hakan be chanja yadda Ya Tariq yake son ta ba, sai ma kara musu closeness da yayi."

"Sai kiyi kuma, ni ban zuba komi ba, kuma suyi ta kara son junan su ni ina ruwana?"

"Da ruwan ki mana, tunda dai kin damu dasu, kuma wallahi gwara ma ki hakura Ya Tariq ba zai taba son ki ba, I'm sorry to say amma iyakar gaskiyar kenan, the earlier the better gwara kiyi ma kanki fada."

"Zancen banza, ni ban san abinda kike fada ba, idan ma hakan ne laifi ne?"

"Laifi ne mana, kina kokarin raba hadin da Allah ya riga ya hada."

"Shikenan, haka din ne ma, kuma ki jira kiga yadda zan dawo da hankalin Ya T kai na."

Dariya Amira ta kwashe da, ta zauna tana kallon Salmar kamar wata mara hankali ko tunani, ko giyar wake Ya Tariq yake sha ba zai taba son ta ba, ita kanta Maman tasani kuma bata masa sha'awar Salman kawai dai tana so tayi amfani da su ne wajen muzgunawa Jidda.

"Sai ki bada himma, kafin me gidan ya gano kece kika zubar da man nan ya kada keyar ki, kinsan kuma ba zan rufa miki asiri ba wallahi."

"Yanzu me ya hanaki fada masa?"

"Jidda ce ta rufa miki asiri,da nasan ko sakan ba zaki kara ba, dama darajar Mama kikaci wallahi, baya so ya bata mata shiyasa."

"Oh, ai da ta fada ita din ma, munafukar yarinya kawai."

"Kissa tafi ki iyawa wallahi, tafi boka tafi Malam, ki zauna ki dauki course din yadda ake tafi da miji cikin ruwan sanyi, kinga idan kinyi aure kya samu na gwadawa."

"Wai Amira ni da Jidda waye dan uwanki ne? Uwa daya fa uba daya iyayenmu ba wasa ba, amma kamar ma nice bare jidda ce yar uwarki."

"Kusan hakan ne ai." Ta juyar da kanta cike da haushin Salmar***A bacin rai Yaya ta nufi wajen Maman bayan ta samu labarin wai Amira da Salma na gidan Tariq har da kwana ma, bata san da wannan tsohon rashin mutuncin ba sai da Aunty ta fada mata, aikuwa ta wanke kafa taje ta samu Maman tana kirga lissafin wasu kudade a daki me aikin ta, ta shigo tace Yaya na mata magana a falo, ture abinda take tayi ta fito ta samu Yayan a tsaye ko zama batayi ba.

"Barka da safiya Yaya."

"Yawwa, yanzu Aisha tsakani da Allah abinda kikayi ya dace Kenan? Ki dauki yara yan mata kice su je su zauna da yaran nan, ina aka taba yin haka? Ko dan ita jidda ba yarki bace ba? Idan akayi wa daya daga cikin yaran nan zaki ji dadi? Itama fa mutum ce kamar kowa, iyayenta na son ta kamar yadda kike son naki yaran."

"Baki kyauta ba, kuma kin bani mamaki, amma ba zan ce komai ba, ba kuma zance su dawo ba, amma fa ki sani, shi sharri dan aike ne, dan haka ki kula, ki kula!"

Sai ta juya tayi ficewar ta, dan tasan Maman ba zata tanka ba, dama kuma ba dan ta tanka tazo ta same ta ba, amma ta fada mata, kuma idan har ita din ba mahaukaciya bace zatayi abinda ya dace, mutane suna da masifar son kansu, shiyasa sam bama cigaba, dan ka shine d'a, d'an wani kuwa babu ruwan ka da duk ma halin da zai shiga.
Shiru Maman tayi bayan fitar Yayan, a kasan zuciyar ta, tana jin bata kyauta ba, amma kuma tsanar Jidda ya danne rashin kyautawar, shiyasa har take jin batayi komai ba, ita dai abu daya kawai take so, Jidda ta kyale mata danta, bata bukatar sake hada wata alaka da Halima bayan wadda ta hada a baya.

    Tana zaune ya zubo mata pepper soup din da aunty ta kawo musu da chips, ya zauna ya saka fork ya debo chips din bayan ya hado da tsokar naman ya nufi bakin ta,a kunyace ta bud'e ya shiga bata yana hada mata da tea me zafi, sai da taci ta koshi sannan ya ajiye ya sa tissue yana goge mata gefen bakin ta yana kallon bakin, yana son dan mitsitsin bakin ta har baya iya dauke ido daga kansa, yana son kissing dinsu a ko da yaushe saboda softness dinsu, daurewa yayi ya share ya zubo kad'an yaci dan already ya karasa golden morn din da ya fara sha. Sake kiran Sufyan yayi still no answer sai yayi tunanin ko yana da emergency case. Ya kyale shi idan yaga kiran zai biyo yasan. Har azahar tayi be kirashi ba, ga hannun ya kara tsami sosai sai ya yanke shawarar kiran Aunty ya kira ya fada mata in brief duk da be fada mata yan yatsu biyu ne da na kafa ba, cewa tayi zata turo jummai daya daga cikin masu aikin gidan da ke bq ta iya gyaran targade, dan kwanaki Usman yayi ita kuma ta gyara masa. Godiya yayi ya ajiye wayar. Baa dade ba sai gata Sam ya kawo ta, ya bud'e mata kofar da kansa ta shigo ta gaishe shi ya amsa yace ta shiga, ta samu Jiddan a zaune suka gaisa ta kalli hannun da kafar, sannan ta kalli Tariq din

"A kawo wuka da manja."

"Wuka?" Yace

"Eh yallabai, sannan dole sai an rike ta, targade daya ma ya aka kare bare har uku, Allah dai ya kiyaye gaba."

"Me za'a yi da wukar? Yanke hannun zaa yi?" Jidda tace hawaye na zubo mata dan ta taba yin targade tasan azabar sa

"Ba abinda za'a yi da ita, kawai zan dan yi amfani da ita ne."

"Amira!!!" Ya bud'e muryar sa ya kirata, ta fito da sauri yace ta kawo knife da manja, taje ta kawo ta zo ta zauna tana kallon ikon Allah, matar ta shafa manjan a jikin wukar sannan tace Tariq ya rike Jiddan, ya matso ya zauna yana jawota jikin sa ya shiga tapping bayan ta

"Calm down,ba zai ciwo ba, I'm here."

Kankame shi tayi tana chusa kanta cikin jikinsa, matar ta kama hannun ta dora wukar a jiki ta dan yi yan sakonni sannan ta cire ta fara taba hannun, ai jidda bata san sanda ta hau kuka wiwi tana kokarin kwace kanta, ya matse ta tausayin ta na kara kamashi, kuka take sosai tana kiran Baffan ta har akayi biyu sannan yace a barta ta huta, ya tashi da sauri ya karo AC din falon saboda yadda take zufa, ya rungume ta yana mata sannu, juyar da kai matar tayi sai kuma ta mike tace zata dan fita waje, tana fita Amira ma ta tashi, sai a lokacin taga Salma a jikin kofar da zata kaita dakin da suke, yi tayi kamar bata ganta ba ta wuce ta. 
   Kanta yake shafawa yana jera mata sannu, har ya samu tayi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa, har jikin ta ya fara zafi saboda azaba, ba dan ciwo bane da cewa zai a kyale ta haka amma dole ayi na kafar dan yasan ba zata iya taka kafar na idan ya kwana.
  
"Ta zo ta karasa miki ko?"

Da sauri ta hau girgiza kai

"Dan Allah a barshi, zai warke da kansa, Dan Allah zan mutu wallahi."

"Shshhh, ba zaki mutu na, kuma ba zai zafi kamar wadanchan ba, kiyi hakuri a karasa kinji? Pleaseeee."

Da ka ta amsa masa da toh, ya leka ya kirawo matar ta dawo, ta kama kafar itama ta gyara aikuwa tasha kuka sosai, ana gamawa ya dauke ta chak ya wuce dakin sa, ya kaita ya kwantar a saman gadon ya zame mata hannun rigar ta zuwa kafadarta yana jera mata sannu.
Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links