SANADIN LABARINA 43


 


                  Page (43)


***Kad'a kansa yayi zuwa ciki ya rage kayan jikin sa, ya shiga ya watsa ruwa ya fito, ya saka gajeran wando da bakar t-shirt ya nufi dakin nata. Murd'a kofar yayi ya shiga da sallama a ciki sosai. Tana tsaye gaban mirror fuskar ta da ruwa alamun alwala tayi. Takawa ya shiga yi har zuwa daf da bayan ta, suka hada ido ta cikin mirror din ta turo baki tana kokarin barin wajen ya riko ta, ta baya ya zura hannuwan sa ta, ta tsakanin cikinta ya rungume ta a tsakanin chest dinsa.


"Me nayi miki?"


Yayi maganar a cikin kunnenta, ta dan ya mutse fuska ta kauda kanta, jawota ya yi da baya da baya har zuwa wajen gadon still yana rike da ita ya zauna yana mata masauki a saman cinyar sa sannan ya sake riketa gam yadda ba zata tashi ba


"Sai kin fada min, me nayi kike share ni?"


"Ba komai."


"Ba wani, fada min naji."


"Sallah zanyi fa!"


"Sai kin fada min zan kyale ki, ba wani wayo da zaki min irin na ranar."


"Ni ba komai, please ka kyale ni."


"Ba zan kyale din ba, kuma kika kara kwakkwaran motsi sai na baki mamaki, kinsan kuma gidan ba mu kadai bane."


Shiru tayi ta daina kokarin tashi din dan bata san me zai mata ba, wata irin kasala yake ji hade da wani irin yanayi me wahalar fassarawa, rike ta ya sake yi sosai a jikinsa yana shakar kamshin turaren jikinta da be taba jin irin sa ba. 

   Harhada kalaman da zai fada mata ya shiga yi a zuciyar sa, ya rasa exact words din da zai yi amfani yace mata abinda taji ba gaskiya bane ba, matsala aka samu, amma kuma ta yaya? Baya so ya karyata kansa da kansa ko yace mata be fada ba bayan tasan komai, hakuri zai bata toh? Ko cewa zai Jiddah ina sonki? Da sauri ya hau girgiza kai, gwara ma ya bata hakurin kawai. Gyaran murya yayi ta dan motsa kad'an ya sake riketa 


"I'm sorry toh." 


"For?"


"Komai ma, duk abinda nayi miki na sanshi ko ban sani ba kiyi hakuri kawai."


"Kuma dole ki hakura ma, tunda na baki hakuri." 


Ya dora yana sake jaddadawa kansa yayi daidai abinda yace. Murmushi ta samu kanta da yi, be ma san takamaimai yadda zaiyi ya bata hakurin ba, be saba ba ko kuma dai tsabar ego dinsa ne ba zai barshi ba, dole zata kara jan ajin ta sosai tunda yanzu ta gama gano yadda ta yi tasiri sosai a cikin rayuwar sa.


"Kinjiiiii ?"


Ya ja maganar jin bata ce komai ba, girgiza kanta tayi tace


"It's not enough, ni ban hakura ba."


"Gosh! Why? Mesa? Ki hakura mana kawai."


"A ah, ban hakura ba, zan tashi nayi sallah pleaseeee, zan koma wajen su Amira kuma."


"Wallahi baki isa ba, ba in da zaki. Yar karamar yarinya dake kina bani headache, ba na baki hakuri ba, mistake ne ba haka nake nufi ba, ba zan sake ba kuma."


"Toh zan yi sallah."


"Naji, naji."


Ya saketa ta tashi, ya mike a tunanin ta fita zai sai kawai taga ya saka key a kofar ya cire key din ya dawo ya haye gadon ya kwanta rigingine. Bata ce masa komai ba, ta koma toilet ta sake wata alwalar sannan tazo ta tada sallah yana kallon ta, ta idar ta mike ta cire Hijab din ta maida shi cikin wardrobe dinta ta, ta dauki rigar baccin ta milk colour da wani khumra me shegen kamshi ta shiga toilet din ta chanja ta shafa turaren a dukka gabobin dake jikin ta har da k'asan guiwar ta kamar yadda Ya Safiyya tace mata sannan ta fito, ta maida su wajen da ta dauka tazo ta dayan side din ta dauki wayarta akan drawer ta zauna daga gefen gadon tana dannawa. Kamshin turaren ne ya dinga shigar masa hanci ya chakude da wani mixed feelings da ba zai iya resisting ba, mikewa yayi ya zauna sannan yace


"Come here." 


Kamar bata ji shi ba, ta cigaba da danna wayar gabanta na faduwa saboda yadda taji muryar sa very deep.


"Jiddaaaaa..." 


"Um?" Ta waigo ya nuna mata kusa dashi


"Zo nan"


Dan jim tayi tsoron ta na daduwa sosai, tasowa tayi tana jan kafa tazo gabansa ta tsaya tana kallon kasa, daidaita kansa yayi yana sauke ajiyar zuciya bayan ta zauna a gefen sa kafafunta na kasa. Matsowa yayi ta bayan ta, ya sakata a tsakiyar kafafunsa ya dora kansa a gadon bayan ta.


"Waye yabaki hint akai na? Fauwaz? Safiyya? Ko wa?"


"Naa..mm?"


"Fada min, nasan dole a cikin su ne, so suke na zauce ko? Shine suka saki kike dagula min lissafi."


"Ni ba kowa."


"Ba wani, I can read your mind, nasan sune I have no doubt, munafukan yara."


Dariya tayi yayi murmushi shima, yana feeling so comfortable da suke tare, 


"Tafiya zanyi." 


"Tafiya?" Tace


"Eh, zan koma in da na fito."


Shiru tayi ta tafi tunani, tafiya zai kenan ya sake barin ta? Ko zuwa zai ya dawo? Ji tayi duk babu dadi amma ta kasa cewa komai, jin tayi shiru yasa shi cewa


"Ko bakya so na tafi?"


"Ummm, bana so." 


"Me yasa?"


"Ba komai."


"Dole akwai dalili, tell me, idan naji dalilin babba ne zan fasa kwata-kwata, nayi zamana anan watching you all day long." Ya karasa maganar a ciki ciki yadda ba zata ji ba


"Zaka dade ne ?"


" Eh, kamar shekara daya haka." Ya tsokane ta


Dauke wuta tayi gaba daya, ta tuna Yasmin, zuciyar ta,ta fara raya mata abubuwa masu yawan gaske, juyo ta yayi da hannun sa ta dawo tana kallon shi, sai yaga gaba daya ta nuna damuwa a fuskar ta, walwalar ta ta ragu sosai


"Tell me, bani reason me karfin gaske, da zan fasa na zauna anan."


"Nasan ba zaka fasa ba, bansan kuma me zaka je kayi a chan din ba, Allah ya kiyaye ya dawo da kai lafiya."


"Zaki bini?" Ya samu kansa da tambayar ta, shiru tayi bata ce komai ba, ya dinga kallon ta kamar ranar ya fara ganin ta, hugging dinta kawai yayi a kalla hakan zai sa ya samu saukin bugawar da zuciyar sa takeyi da karfi wanda har yake tunanin zata iya ji.


"I love you Jidda." Ya furta a chan k'asan makoshin sa, wanda ya shiga har cikin kwakwalwar ta ya zagaye ilahirin jini da bargon ta, ji tayi kamar ana zare mata kasusuwan jikin ta, ta runtse idon yar karamar kwalla ta biyo gefen fuskar ta, be san taji ba, a tunanin sa ba zata ji maganar da yayi ba, shiyasa be kawo komai ba, bata nuna masa taji ba, ta yi luf yana shakar kamshin jikinsa da ya kasance ya kama jikin a ko da yaushe kamshin yake yi.


   Sun dade a haka, shi ya fara zare jikinsa yana gyara mata zama a sosai a jikin sa, tayi luf kamar mage, a duk lokacin da ta ji ta a jikin shi sai taji gaba daya komai na duniyar ya tsaya chak, bata ji da tunanin kowa sai duniyar su, me dauke da iya su biyu kawai. Hannun sa a saman gashin ta, yana shafawa a hankali har bacci ya soma fizgarta, yana ganin sanda take rufe idon ta, sai ya sake gyara mata kwanciyar sosai yadda zata ji dadin yin baccin ba tare da takura ba. 

     A zaune ya soma baccin shima dan baya so ya motsa ya katse mata baccin ta, sai chan dare ya janye ta ya kwanta shima yana sakata a jikinsa yayi mata rumfa da jikinsa. Ran Salma ya kai kololuwa a baci amma sanin Amira ba zata biye mata ba yasa bata ce komai ba, ace dan wulakanci tunda ta shige bata saka fitowa ba, ko sai da safe ai ta ce musu, gashi babu damar bin bayan su amma dole ta kira mamin ta gobe ta fada mata Ya Tariq din yana son Jidda dan ko makaho zai iya tantancewa tsananin son da yake mata a yan sakanni da basu wuce biyar ba, bata san Jiddan ma A bace sai da taga ta kama hannun Ya Tariq din ba kunya sun yi shigewar su, ita duk kallon wawiya yar kauye take mata duk da wayewar da tayi amma ta raina ta sosai, sai gashi tayi abinda ya bata mamaki ya kuma daure mata kai dan Ya Tariq din ma bata taba kawo zai iya yin abinda yayi jiyan ba, su Mama bonono suke wato rufe kofa da barawo, a tunanin su ba zai taba son Jiddan ba sai gashi zata basu mamaki. Tana kallon Amira tana jan munshari amma ita ta kasa tana tunanin me yake wakana a chan wajen su, son Ya Tariq din take da mugun kishin sa, dan tun ba yau ba Anty Nafi take kwadaita mata auren Tariq din shiyasa duk tabi ta gama tsara rayuwar ta, da yadda take so ta kasance, ko wannan gidan da suke ciki a buri da hasashen ta yayi mata mugun kad'an gida take so na alfarma na kece raini da ma'aikata birjik suna mata hidima ta huta sosai taji dadin rayuwar ta. Ta dade tana wannan lissafin wasikar jakin kafin ta samu bacci ya dauke ta mara dadi.

   Amira ce ta rigata tashi ta riga su dukka ma tashi dan har su Jiddan basu fito ba a daki Ya Tariq din ma yayi sallar asubah shi da Jiddan suka koma suka kwanta duk da nokewar da take tana jin kunya amma yaki barin ta, dole ta kwanta tana zara ido ya kanainaye ta da hannayen sa ko kwakkwaran motsi tayi a jikin sa zatayi shi. Godiya taje ta taso tazo ta gyara falon tas tayi moping Amiran na guiding dinta ta dauko turaren wuta ta saka a burner nan da nan gidan ya dau kamshi ta koma daki tayi wanka ta fito kenan Salman ta tashi daga baccin wanda bata jin ko sallar asubah tayi tana bacci, mika tayi tana kallon Amiran da ita ma kallon ta take


"Kinyi sallah kuwa?"


"Yanzu zan yi." 


Ta sakko daga gadon ta dauki towel din da Amira tayi amfani dashi ta shige toilet din, tsaki Amiran tayi dan bata son sharing da kazanta kuma akan towel din kusan sau uku suna fada amma taki daina dauka. Cigaba da shiryawa tayi tana cikin shiryawar Jidda ta kwankwaso ta shigo ciki ta zauna a gefen gadon tana kallon yadda gadon ya hargitse.


"Goodmorning Matar Yah."


"Kina da matsala, ina Salma?"


"Ta shiga toilet,jiya shine kika gudu kika barmu."


"Bacci nayi da wuri shiyasa, "


"Fadi gaskiya dai, ko dai Ya Tariq ya hanaki dawowa?"


"Eh shine ya hanani, tunda haka kike so kiji."


"Good, a cigaba da rikita min yayana, I trust you."


Dariya Jiddan tayi, Salma dake tsaye jikin kofar toilet din taki fitowa ko zasu fadi wani abun ta samu dorawar sai taji tace


"Kunyi breakfast kuwa?"


"A ah, amma aunty ta kira a wayar ki dake falo, dan har zan sama mana wani abun sai kuma ta kira na dauka tace Sam ya taho."


"Yawwa, na huta bari na kirata." 


Ta mike ta fita, sannan Salma ta fito, Amira ta kalleta ta tabe baki ta dau wayar ta.

   Zuwa tayi ta kira Aunty tana dauka ta fara fada


"Amira da Salma a gidan nan suka kwana wai?"


"Ya Aunty, jiya suka zo."


"Jiya? Ina Tariq din? Me zai sa su kwana a gidanku?"


"Zuwa kawai sukayi Aunty."


"Karya ne, turo su akayi wallahi, wannan wane irin abu ne, kina ji na, karki yarda ki yi sake ki saki mijinki har su samu dama akanki, yarinyar nan Salma ba dan Allah aka turo ta ba, idan kika tsaya shashanci sai ta raba ki da gidanki."


"Aunty, waye zai turo ta? Kuma tayi me?"


"Ta kashe miiki aure mana."


Zaro ido tayi, 


"Ni? Akan me yasa?"


"Oho, karki tsaya tambaya kiyi abinda ya dace, kuma bari, dani suke zancen wallahi na daina kyalewa, Yaya zan fadawa wallahi."


"Aunty dan Allah ki daina shiga matsala akai na."


"Ba wata matsala, na daina kyalewa kawai."


Fitowa yayi sai tayi shiru tana sauraron Auntyn, a gefen ta ya zauna sai tayi saurin cew


"Shikenan aunty, sai yazo."


Ta kashe ta ajiye wayar a gefe, 


"Sam ne zai kawo mana breakfast in ji Aunty?" Gid'a kansa yayi yace


"Ni nake nake so."


"Nawa?"


"Um... Golden morn zan sha."


"Ok,." Ta mike ta nufi kitchen din, ta shiga taga ko ina an gyara tsaf, tasan da tainakon Amira dan amira sam bata da son jiki ko kad'an, bud'e cabinet din da tarkacen kayan su madara suke ciki ta dauko golden morn din ta ajiye akan iceland ta dauko mug, motsi taji a bayan ta ta juyo sai taga Salma ce ta shigo kitchen din, ta wuce kai tsaye wajen sink ba tare da tace komai ba, dauke kai Jidda tayi dan bata isa itama ta kula ta ba, musamman bayan aunty ta fada mata dalilin dayasa aka turo ta, cup ta dauka ta dauraye a sink din sannan tazo gefen ta, ta bud'e ta dauko kayan tea ta zuba a cup din tana had'awa. Fita jidda tayi bayan ta dora komai akan dan madaidacin tray ta wuce daki dan ya bar falon, ta kai masa sai ta tuna babu ruwa a fridge din cikin dakin ta dawo da nufin dauka, tana shiga tsantsi ya kwasheta, ta kwalla kara da karfi kafin ta zame gaba daya ta fadi a daidai kofar kitchen din. A guje ya fito Amira ma haka suka nufi kitchen din a rikice 
*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links