DAUDAR GORA 13


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲      



  ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨

           (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)




            𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻



*_13_*




.........Ta ko'ina bayine masu hidima ga wannan basarakiyar daula. Yo basarakiya mana, dan itace masarauta dake mulkin ƴan ƙasa dama sarakunan ƙasar baki ɗaya. Sun sake wuce gate na biyu inda anan ɗin ma dai katafaren wajene da misaltasa babban aikine ga mai hasashe. Ta ko'ina hadimai ne ke kaiwa da komowa maza da mata. Ga wasu irin gine-gine na alfarma da ɗaukar hankalin mai kallo tamkar ba'a cikin ƙasar Ruman ba. dogayen gine-gine ne da abaya sai dai su hangosu daga nesa tamkar yanda suke iya kallon jirgi yayinda yake keta giza-gizai. Ga wasu irin korayen shukoki tako ina tare da shimfiɗaɗen lafiyayyen titi da za'a iya rantsewa yafi kowanne titi dake a cikin ƙasar Ruman. Kasancewarta farin shiga a ganin wannan shimfiɗaɗɗiyar daula saita fara tunanin anyama kuwa a duniyar mutane take? Kokuwa dai mafarki takeyi ne? Dan sam inda take yafi kama da anguwanin ƙasashen turawan da a tv ne kawai suke iya ganinsu cikin film ko labarai da makamantansu...

       Har motocin suka samu wajen tsayawa aka fito da ita sam ba'a hayyacinta take ba, bawai ƙawatuwa da tarin ƙyale-ƙyalen da aka zubane kawai ke ɗibar hankalinta ba, akwai wani ɓoyayyen tunani acan ƙasan ruhinta da ƙahon zuciyarta mai alaƙa da tabbatar da abinda mutane ke faɗa akan Daular Ruman ɗin......  Saukar sautin busar sarewa mai zaƙi da daɗin saurare da ya fara tashi a cikin daular Ruman ya sauka cikin kunnenta tare da katse tunaninta ya maidota hayyacinta. Wannan saƙone dake isa zuwa kunnen duk wanda ke a cikin masarautar cewar an iso da _Zawjata almilki_. 

        Tsawon lokaci sautin na tashi har sai da saƙon ya isa ga kunen kowan da ake buƙata. Daga Iffah dai bata san ma'anarsa ba, dan haka bata ɗaukesa komai ba. Sai ma share hawayen fuskarta data cigaba dayi, dan har yanzu fuskar tata na lulluɓe ne da hular ƙawatacciyar rigar jikinta da zamu iya kira alƙyaba. Sai dai zuciyarta cike take da alwashi mai ban tsoro ga duk wanda zai iya jinsa a kunne. Ta sadaukar zata mutu, amma ba ita kaɗai ba harda Shahan-shan na Daular Ruman, idan an hanata damar bayyanama duniya a ƙwato musu ƴancinsu, sai ya mutu aga wanda zai cigaba da kashesu. A karan farko ta saki murmushi mai ƙayatarwa, irin murmushin data jima batayiba kuwa........

         Babu wanda ta ɗaga kai ta ko kalla a cikinsu har suka gama bushe-bushen algaitunsu dana sarewa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin matan da suka ɗakkota ta matso gab da ita. 

     “Ran Zawjata-almilki ya daɗe, nan shine sashen Malikat Bushirat. Mahaifiya ga Zakin wannan daula Shahan-shan, Uwa ga duk wani ɗan ƙasar ruman”.

    A karo na farko Iffah ta ɗan ɗago idanu ta dubeta kaɗan daga cikin alƙyabar, kanta a ƙasa yake ita a dole bazata iya ko haɗa ido da ita ba domin girmamawa. komai batace da ita ba, sai dai ta dubi katafaren ginin da ya tabbatar mata da maganar matar. Idanunta ta maida ta risinar kawai batare data nuna alamar tama jita ba. Abin mamaki bai nema tsaida bugawar zuciyar Iffah ba sai da suka shiga wannan katafaren gini, bayi sai zubewa suke akan gwiyawunsu tamkar wasu masu neman gafara ko kuma Tajwar Eshaan ɗinne da kansa. Zaman faɗa muku daula da dukiyar dake a wannan sashe ma ai ɓata lokacine, dan haka na baku damar ƙiyastama zukatanku kawai.... (Lol😉😋😆)


        ★Karan farko na tarihi, karan farko na rayuwa, yau ga Iffah gaban *_Malikat Busheerat_*. Mace ta biyu ga tsohon Tajwar Haysam ibn Abdull-Majeed. Mahaifiya ga Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdill-Majeed Shahan-shan na wannan ƙarni. Hamshaƙiyar mace mai tsananin ƙyau tamkar itace ta zaɓama kanta ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da zubin halittar ta. A kallo ɗaya da Iffah tai mata daga cikin hular alƙyabar jikinta ta kasa sake ɗaga idanu ta ƙara saboda kwarjininta. Ta tabbatar ta isa a kirata _Malikat_ (Sarauniya), Uwa ga fir'aunan sarki kuma. Kishingiɗe take a ɗaya daga ƙayatattun kujerun katafaren falon daya amsa sunansa daular duniya, wanda kafin isowarsu cikinsa sun wuce manyan faluka da suma suka amsa suna daular duniya bama ta ruman ba kawai. A gefe da gefenta wasu matanne cikin shiga ta alfarma suma har su huɗu, sai hadimai dake zagaye da ita kowanne da hidimar da yake a gareta cikin matsanancin taka tsan-tsan da kai. Dan ko wadda ke tare da ita suna shigowa zubewa ƙasa sukai jikinsu har tsuma yake yi, ita Iffah har tsoroma suka bata tare da mamaki mai girma na wannan ƙarfin iko.

       Iffah dai na tsaye har sai da ɗaya daga cikin matan nan dake tare da Malikat ta miƙe ta kamota ta zaunar ƙasa bisa lallausan carpet ɗin dake a falon saitin Malikat Bushirat da har yanzu tana a kishingiɗenta kuma ko sau ɗaya bata ɗago ta kalla kowaba tunda suka shigo. Kusan minti biyu falon yay tsitt babu wanda ya sake koda motsin kirki, sai ƙarar na'urar sanyi dake tashi kaɗan-kaɗan da wani ƙamshi na musamman.


(To masu karatu inhar Malikat na'a haka, yaya shi kuma Tajwar ɗin zai kasance kenan akan izza da mulki?🤔.)


      Iffah da shirun ya isheta kaɗan ta ɗago idanunta ta cikin hula ta saci kallonsu. Sai taga su duka har Malikat ɗin ashe ita suka zubama idanu. Haka kawai tasha jinin jikinta, dan kallone bana a santa ba, kallone dake buƙatar nutsuwa kafin a bashi fassara. Kaɗan taja numfashin dake neman maƙale mata a maƙoshi da ƙara yin ƙasa da kanta hular ta sake rufe fuskarta ruff. A hankali, cikin son ɓoye rauninta da hawayen dake neman kwace mata ta furta “Barka da yamma ranki ya daɗe”.

       “Malikat ta amsa miki, tare da maraba a gareki”.

  Ɗaya daga cikin matan ta amsa a maimakon Malikat da har yanzu batako motsa daga kishingiɗar da tayi ba. Sai dai ta ɗago ƙyawawan idanunta farare tas ta sake zubasu akan Iffah, idanun ta juya a hankali ta dubi ɗaya daga cikin matan nan dai dake kusa da ita. 

      “An gama ranki ya daɗe”.

Matar ta faɗa da girmamawa alamar ta fahimci mi take nufi. Tsam ta miƙe zuwa inda Iffah take, ta kai hannayenta biyu ta kama hular alƙyabbar tai baya da ita, ƙyaƙyƙyawar fuskar Iffah datai jajur saboda kukan da tasha abinka da farar fata ta bayyana. Idanu Iffah ta rumtse sakamakon jin al'amarin a bazata, ga wani irin harbawa da ƙirjinta yayi har sai da ta ambaci (Hasbinallahu wa-ni'imal wakil) a zuciyarta sannan taji numfashinta da yay sama yay ƙasa a lokaci guda ya daidaita. Kaf hadiman ƙasa sukai da kansu, dan haramunne a garesu kallon fuskar *_Zawjata-almilki_* kai tsaye. Yayinda Malikat Bushirat ta motsa a karo na farko daga kishingiɗar da tai idanunta akan Iffah. Kusan kallon mintuna biyu tai mata kafin ta janye idanun cike da ƙasaitar masu isa, yatsun hanunta ta ɗan murza suka bada sautin (ɗass! Ɗass!!!) har sau biyu. Tamkar ƙiftawar ido hadimar dake tsaye riƙe da wani ƙasaitaccen bowl kalar gold da adon stones masu ɗaukar ido ta iso gaban Iffah da kanta ke ƙasa har yanzu tana ambaton ALLAH a zuciyarta ta zube tamkar mai neman gafara. Kanta a ƙasa alamar bazata iya kallon Iffah ba ta miƙa mata bowl ɗin hannu biyu bayan wata a cikin sauran hadiman ta matso da sauri ita kuma ta janye farin ƙyalle da aka yana a saman bowl ɗin tare da murfinsa, tatacciyar madara fara tas ta bayyana. Cikin rawar murya da tsantseni hadimar ta furta, 

     “Ya Zawjata-almilki! Wannan madara ce mai daraja daga hannun Malikat domin nuna maraba da zuwa a gareki cikin DAULAR RUMAN”.

      Shiru Iffah bata da alamar motsawa, har hakan ya bama duk wanda ke gurin mamaki har Malikat Bushirat. Tsahon sakanni goma kafin ta ɗago. Manyan idanunta da sukaci kuka har suka gode ALLAH ta zubama bowl ɗin tare da hadimar dake gurfane a gabanta tamkar mai neman gafara. Kanta ta girgiza a hankali tare da sake maidashi ta risinar. Cikin motsa laɓɓanta a hankali tace, “Wannan karamci abin alfaharine a gareni da nuna tsantsar godiya ga Uwa gareni dama ƙasar Ruman baki ɗaya. Sai dai ina mai neman afuwar jinkirtamin shan wannan madara sakamakon azumtar wannan yini da nakeyi batare da nasan yau zata kasance rana mafi daraja da alfarma a gareni ba”.

        Kalaman Iffah da tasirinsu tamkar saƙar ƙudan zumace cikin kuttu a zukatan duk wani mai numfashi dake a wannan falo. A zahiri da baɗini kuma babu wanda mamaki bai bayyana akan fuskarsa ba, saboda abune da bai taɓa faruwaba a cikin daular ruman. Malikat Bushirat tai ƙyauta a jinkirta amsa tare da biyo jinkirin da sharhin da babu gargada akan harshen mai furtashi. Wannan abu yakai a kalla Iffah a sake kallonta dan ko ƴaƴan gidajen sarauta goma cif da aka kawo daular a irin matsayinta basu samu ƙwarin gwiwar ƙin shan irin wannan madara ba. Hasalima kowaccensu da rawar jiki take amsa ta shanye tas ta bada bowl ɗin tana mai gurfana a gaban Malikat domin yin godiya. Ba'a matsayi kuma kawai ba hatta a shekaru Iffah itace mafi ƙanƙanta a cikin Zawjata-almilki goma sha huɗu da aka kawo gidan.

      Ɗaya daga cikin matance ta zabura idanunta dake nuna ɓacin rai akan Iffah. Sai dai abin mamaki Malikat Bushirat da idanunta ke kan Iffah ko ƙyaftawa babu ta ɗaga mata hannu alamar ta zauna tare da sakin wani ƙasaitaccen murmushi. Nuni tai akan a rufe madarar. Ruf aka maidata yanda take hadimar ta miƙe daga gaban Iffah da tunda ta sake maida kanta ta rissinar bata ƙara ko motsawa ba.

       A karo na farko Malikat ta motsa laɓɓanta, cike da izza da ƙasaita irin ta manyan masu mulki. “A kaita masaukinta”. Ƙasaitacciyar muryarta ta ratsa zuciyar Iffah tare da girgiza gaɓɓanta cikin ikon harbawar jini. Sunan ALLAH ta ƙara tsarkakewa a zuciyarta dan tabbas Malikat ta cika Malikat ɗin babu tantama. Saboda muryar tata kanta barazanace ga duk mai yunƙurin kawoma girmanta wargi da saka tsantseni a zuciyar duk wani talaka dake a ƙarƙashin mulkinta.

      “Ki huta lafiya, cikin aminci da farin ciki”.

   Iffah ta faɗa cikin risinar da kanta alamar girmamawa lokacin da take miƙewa bisa taimakon ɗaya daga cikin matan nan. Yin hakan ya sake saka zukatansu a mamaki, ita kanta Malikat Bushirat da kallon ƙasan ido ta bisu har suka fice. A ƙasan ranta tana mai jin farin cikin samuwar Zawjata-almilki data dace da gudan jininta tilo kuma Shahan-shan na ƙasar Ruman gaba ɗaya. A ganinta lokacine daya dace tai yaƙi da maƙiyanta masu yaƙar Zakinta a yanzu dake zagaye da su.....


          ★★Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni amarya Iffah (Zawjata-almilki) an isa da ita sashenta dake gab da sashen matan Tajwar Eshaan su biyu da har yau suke raye, sannan kuma kusa da katafaren sashen Tajwar Eshaan da yafi kowanne gini ɗaukar hankali da kayan kyale-ƙyale da tsagwaren dukiya a cikin Daular Ruman harma da tsantsar tsaro... Sashen Iffah ya kasance shima sashe dake ɗauke da nau'in kayan more rayuwa da a kallo ɗaya mai karatu zai tabbatar da sai dai Zawjata-almilki ɗince kawai kam ta dace da zama a cikinsa. Kamar yanda al'adar take anyi rakkiyar Iffah dake kan keken doki tare da busar sarewa mai daɗin saurare har zuwa sashen nata. Iya masu hurumin shiga kawai suka shiga har cikin bedroom da suka kira matsayin master bedroom nata. Sai dai suna fita ta miƙe daga zaman ɗofanar da tai a gefen gadon, cikin ambaton sunan ALLAH da zubar hawaye ta jaye hular alƙyabar ta ta ƙarema ɗakin kallo na tsahon mintuna uku. Komai batace ba ta ɗauka akwatinta da aka shigo da shi ta fito a ɗakin tare da jawo ƙofar. Bata wani tsaya kallon falon data fito ba, sai dai tabi kowace kusurwa na cikinsa domin lissafa adadin ƙofofin dake a cikin. Ƙofar da lissafinta ya tabbatar mata ta nufa, cikin ɗan jimami da tausayin kai ta murɗa ƙofar mai kalar ruwan gold. Ɗakin ta shiga bayan ta leƙa kanta cikinsa. Shima ɗin dai a ƙayace yake da komai na alfarma. Sai dai komai nasa ya banbanta da kalar na wancan ɗakin. Amma shima duk abinda ke cikinsa royal ne irin kayan da suka dace da gidan hamshaƙan masarautu kamar Daular Ruman. Ajiyar zuciya ta sauke bata samun nutsuwa ba, sai ta son rage nauyi mai danƙarewa a ƙirji kawai har numfashi ya gaza samun damar fita yanda ake buƙata. Jikkar ta ajiye tare da zama bakin gadon ta rushe da sabon kuka.........✍



_To ko burin Malikat Bushirat zai cika kuwa? Kokuwa dai itama Iffah zata suɓucema ƙwarin gwiwar tata tamkar Zawjata-almilki na baya da suka shuɗe ta hanyar kisan da har yanzu ba'a san wanene sanadinsa ba?. Idan Shahan-shan ne da kansa yaya Malikat zata kasance a wannan yaƙin kenan? Dan masu iya magana kance fa DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA.._


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links