SANADIN LABARINA 24


  Page (24)***Kwanan ta biyu a gidansu, Baffa yayi mata nasiha da kashedi sosai akan abinda ya faru, ya kuma ja mata kunne sosai akan kar yaji kar ya gani, duk a tunanin sa zata bijire, be san da gaske take son abun. Wuni tayi ranar da tazo a gidan Saude wadda akayi bikin ta da kaka, bata samu zuwa ba lokacin suna examz, gashi hadda tsohon cikin ta, sun sha hira suka tuna da sannan ta dawo da la'asar sakaliya.

  Iya Lami nata haba-haba da ita,ta share ta kamar bata san Allah yayi ruwan ta a gidan ba, dan ko kad'an bata son matar dan babu kalar azabar da bata gana mata ba, akwai wani duka da tayi mata har yanzu da ragowar shatin dukan a gadon bayan ta abunka da fara. Shiyasa taki sakin jiki da ita sam bare ma su zauna suyi doguwar magana. Ranar da zata tafi Aunty ta turo aka dauketa, dan ta karasa abubuwan da bata karasa, dan da safe zasu tafi washegari.

   A tsakar gidan Yaya ta tarar dasu ana ta fama da Yaya tayi tsalle ta dire babu shegen da zai sakata shiga jirgi, idan kuwa akace dole toh ta fasa tafiyar, duk yadda Fauwaz da yazo yaso ya fahimtar da ita sam taki fahimta, kamar ma a tsorace take da al'amarin, gashi a wannan yanayi na insecurity babu yadda za'a yi a barta ta shiga mota, haka kuma a barta ita kadai ma matsala ce. 


"Yaya menene?" Tace tana matsawa kusa da ita


"Yawwa gwara da Allah ya kawo ki, kiji dan wulakanci wai jirgi zamu hau idan zamu tafi."


"Eh Yaya, ba bata lokaci nan da nan zaki ga anje."


"Aikuwa banga uban da ya isa ya sakani hawa jirgi ba wallahi."


"Har Baba?" Fauwaz yace yana dariya 


"Ko Kaka ne, ehe."


"Ah abun azimun ne, bari na kira Baban da kansa yayi miki magana, kila shi yayi convincing dinki."


"Duk ma me zakayi kayi, na gama magana."


"Muje ki zauna Yaya, ki daina yawan fada kina tada hankalin ki dan Allah."


"Toh yaran nan ne duk hanyar da zasu birkita min lissafi sun santa, ina dalili za'a ce dole sai na hau jirgi? Ai ba dole bace Habujan ko? A kyale ni dan Allah.". 


Sai ta fara tari da karfi, saurin tallafa mata jiddah tayi, ta mika mata ruwa tasha tarin ya lafa, zata cigaba da sababi Jidda tayi saurin cewa


"Kiyi shiru karki sake tarin, ba in da zaki a jirgi, a mota zamu tafi ni dake sai su suyi ta hawa jirgin su."


"Yawwa toh idan hakan ne na amince."


Kallon Jidda Fauwaz yayi, kallon kunfi kusa ya juya yana ayyana yadda zai yiwa taurin kan Yayan. Be kira Baban ba kamar yadda yace, sai kawai yaje ya samo maganin bacci, ya ajiye a daki, da safe bayan sun shirya tsaf, sun fito ya dauko lemon exotic madaidaci ya saka mata maganin baccin dan daidai wanda ba zai bugar da ita ba, ya shiga part din ya sameta ta saka sabuwar atamfar ta, da sabon Hijabin ta fari kal, sai takalmin shima sabo tana cike da jin dadi ga sabon lalle a kafar yayi har ya soma duhu-duhu.


"Ya ka gani?"


"Kin fita fes fes ko ba sabula mutuniyar."


"Godiya nake kaji, kasan fa kakanku tsabar dunkum dinsa ko yaba abu bayayi, ni bansan dadin kayi abu miji ya yaba ba, sai bakin rai da turbune fuska kamar shi aka dorawa baki daya matsalar Nigeria."


"Innalillahi, wai Yaya ba zaki kyale bawan Allahn nan ya huta ba, ko me yayi ai yaci ace an yafe masa haka nan."


"Toh ubana, sai ka fada min abinda ya kamata nayi tunda kai ka haife ni, ko kai kake bani ci da sha."


"Allah ya huci zuciyar Hajiye Dije, ga exotic na kawo miki kisha idan kun shiga mota, sai mun hadu a chan dan mu dai jirgi zamu hau."


"Ah ka kyauta, kasan kuwa dama na kwana biyu ban sha ba, shegen likitan nan bakin mugu wai a hanani shan kayan zaki kamar shine ubana, shikenan Alhaji yasa akai daina siyo min."


"Yanzu dai gashi nan na kawo miki, kisha karki bawa kowa fa, naki ne ke kadai tawan."


"Uban yan dadin baki, naji ni kira min jiddah mu dau hanya, kar muyi dare duk da dai ance sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a je."


"Gani ma Yaya." Ta shigo sanye da atamfa lemon green and orange tayi mata kyau sosai har sa da Yaya ta kasa dauke ido daga kallon ta


"Wai wai wai, chanchadi."


A kunyace ta karaso ciki, Fauwaz yayi mata signal da ido yana nuna mata juice din hannun, ya fita. Bata gane komai ba, sai ga message dinsa bayan ya fita


"Make sure tasha juice din nan, sai mun hadu a airport."


Kallon juice din tayi ta kalli Yayan, 


"Kisha lemon naki Yaya sai mu tafi, an gama saka kayan a mota."


"Auw toh." Tace tana bud'e murfin, ta kwankwade shi tas da dan sanyin sa dama, jidda ta karbi kwalin ta jefa a dustin sannan suka fito harabar gidan, ta taimaka mata ta shiga motar itama ta shiga, sannan suka fita daga gidan, suna fita motar su aunty itama ta bi bayan su ita da Usman sai Fauwaz din a gaba.

  Bacci ne ya soma daukar Yaya sama-sama, jiddah na kallon ta, ta gyara mata ta jingina sosai bacci me nauyi ya dauketa. Suna isa airport din aka samo wheelchair aka dora ta, aka sakata a cikin jirgin suka lula sai Abuja.***Sabuwar Rayuwa! Sabon Shafi***


Baki sake Jidda take kallon garin yadda ya tsaro, bata dai taba hasaso haka Abujan take ba, ta dai san tana da kyau amma bata kawo haka ba,sosai yayi mata kyau kwarai, ta kalli Aunty sukayi ma juna murmushi, har lokacin Yaya tana ta sharbar baccin ta.

   Unguwar da suka shiga ita ta sake rikita Jidda har ma da Aunty duk da tana boyewa, babbar unguwa ce da manya manyan gine-gine tsararru, cikin tsari gwanin sha'awa. Shiru babu motsin kowa ba zaka taba cewa akwai halittu da suke rayuwa a cikin wajen ba 

    A kofar wani babban tangamemen gate suka tsaya, gate din ya bude da kansa suka kutsa kai cikin katafaren filin gidan, wanda yake dauke da motici manya daga chan gefe, sai shuke-shuke masu ban sha'awa.

   Wani matashi ne yazo bayan sun tsaya, ya bud'e musu kofar ya russuna ya gaida Auntyn sannan yace


"Ga part din chan." 


Ya mika keys din, karba Jiddah tayi, Fauwaz ya zagayo ya leka Yaaya da take ta sharbar bacci, ya kalli aunty ya kwashe da dariya


"Ya za'a yi da ita yanzu Aunty?"


"Ai baka kyauta ba wallahi,."


"Aunty bansan ya za'a mata ba wallahi, kinsan kafiyar Yaya."


"Ni dai kar a samu matsala fa."


"Babu in sha Allah, peaceful bacci fa take, kuje bari na kirawo masu aikin nan na bq su taimaka sai a kai ta part dinta."


"Je ka kirasu dai ina nan, Jidda jeki ke da Usman gani nan."


"Toh." Tace ta rike hannun sa suka nufi shashen da aka nuna musu,tun kafin ta karasa take admiring ginin bare kuma ciki.  Wani security ne daga gate ya taso, ya dan russuna ya gaida Auntyn sannan yace ko akwai matsala, girgiza masa kai tayi tace babu, ya bata hakuri ta koma wajen aikin su, gwada tashin Yayan tayi ta dan tattabata sannan ta kira sunan ta, a hankali ta bud'e idon da kad'an kad'an har ta gama gaba daya,sai ta kalli motar da take ciki ta kalli Aunty


"Kar dai har mun karaso ina ta bacci."


"Eh Yaya, ai wai ashe tunda kuka dauko hanya kike bacci zuwan ku kenan, jidda tace kina mota kina bacci shine nace bari nazo na taimaka miki."


"Wai gaskia nasha bacci, awa nawa kenan ina baccin?"


Ta zuro kafarta waje ta sakko, sai taga kamar lokacin suka baro gida, kamar zatayi magana kuma sai ta fasa hango Fauwaz na nufo su da wasu mata kedaru su biyu, kana ganin su kaga karfafa.


"Ah ashe ma ta tashi."


Sai ya juya wajen su yace


"This is the second Madam, greet her."


"Good morning Ma'am."


"Good morning." Tace a takaice


"You can go." Ya ce suka juya zuwa in da suka fito, salati Yaya ta rafka tana tafa hannu


"Yanzu tsabar lalacewar ta kai lalacewa har da arna a gidan nan, na shiga uku ni Hajara yau naga abinda yafi karfi na."


"Kai Yaya, house help ne fa, kuma ba arna bane kawai dai basa jin hausa ne."


"Toh dan tsabar iyayi a rasa irin ma'aikatan da za'a dauka sai wannan zandara-zandaran zawarawa? Wai na shiga uku na lalace."


"Fito na rakaki bangaren ki, kin ga yadda aka miki kuwa, harda katuwar TV ta bango gas fridge dinki cike da kayan dadi, kuma Baba yace zaa dauko miki gwaggo kuyi zaman ku."


"Da gaske?" Ta washe baki tana fitowa gaba daya, 


"Muje ki gani, Anty sai mun shigo."


 Yace yana rike hannun Yayan, ita kuma Aunty ta nufi part din da jiddah ta shiga, wanda yake da yar tazara tsakanin su da wani hadadden part da yake a tsakiyar gidan wanda aunty ta tabbatar na matar gidan ne.

   A tsaye ta samu su jidda suna karewa yar karamar daular tasu kallo, ita kanta Auntyn sai da ta jinina, yayi kyau sosai duk da ba wani katon gani bane, kayan su aka shigo musu dasu, sannan Auntyn ta lallaka dakunan ta nunawa jiddah nata ita ma ta shiga nata.

   Amira ce kawai ta rage a gidan duk sun tafi school itama bacci ta koma bayan tayi sallah tunda tasan zuwan su jiddan ba lokacin bane. Wajen sha daya ta tashi, tana sakkowa daga gado tayo waje, suka hadu da Mama a falo tana duba wayarta, da kallo tabi Amiran kamar ta fuzgo ta, ta dake ta haka takeji dan yadda take son jiddah ko ciki daya suka fito sai haka. Bata dai kulata ba har ta fice ta kuma san in da zata dan taga shigowar su gidan ta window, ta kuma ga duk abinda ya faru tsakanin su da Yaya duk da bata ji me suke cewa ba, sakin curtain din tayi kawai ta cigaba da abinda takeyi.

   Da sassarfa ta isa part din sannan tayi knocking, Jidda ta zo ta bud'e suka rungume juna cikin tsananin farin cikin ganin juna. Fitowa Aunty tayi da murnar ta, Amiran ta gaishe ta sannan suka kule dakin jiddah ta tayata hade kayan ta waje daya a cikin wardrobe suna yi suna labari, yawanci akan school din da zasu fara zuwa ne next week da kuma yanayin rayuwar garin da yadda zasuyi mingling da yaran manya, ita dai jiddah ta san matsayin ta, bata sa a ranta zatayi rayuwa irin ta su ba, saffa saffa dai kar ta zak'e, duk da haka tasan dole ne ko taki ko taso rayuwar ta sai ta sauya ta sake daukar ta zuwa wani bigire na daban.


***Dawowar su Abuja ya sauya abubuwa da dama daga rayuwar Jiddah, sati daya cif da zuwan su suka fara zuwa wata private university a abujan, course daya sukeyi sai ya zama kullum tare suke duk in da kaga daya zaka ga daya. Sai dai a wajen da Jiddan tasan zai iya shafar matsayin ta na matar aure, wanda ta rike hakan da matukar muhimmanci, bata kuma sakaci bare ta yi wani abu da ya sabawa Allah.

  Sau biyu taje gaida Mama a satin da suka zo amma da kyar take amsawa, tayi saurin barin wajen, haka Jiddan zata tashi jiki a sanyaye ta bar part din, na farko aunty ce tace taje ta gaishe ta lallai dan da, da yanzu ba daya bane, akan haka taje amma sai data gwammace bata je ba, haka dai ta daure ta sake zuwa a karan kanta bayan Amira tazo wajensu tayi mata korafin zuwa nasu part din, nan ma dai same abinda ya faru da farko shi ya sake faruwa. Duk abinda ya faru bata fadawa Aunty ba, boye mata kawai tayi a matsayin babu komai dan taga yadda Auntyn take tada hankalin ta akan maganar auren.

[

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links