SANADIN LABARINA 23


 Page (23)


***Kafin isowar Dr Aminu, zazzabi me zafin gaske ya rufe shi, sai rawar sanyi yake saida aka kashe AC falon da duk wata na'urar sanyi me alaka da wajen, daki ya taimaka masa ya kaishi ya kwanta,sannan ya hau examining nashi, ya gama ya rubuta masa magani sannan ya daura masa drip saboda yadda jikin sa yayi weak gashi babu komai da ya saka a cikin sa, fita yayi yaje ya kawo magungunan yace a bashi idan ya tashi ya sha, sannan yayi musu sallama ya tafi. Jigum sukayi a dakin nasa cikin yanayin rashin jin dadi har Daddy ya dawo ya same su. Baya hada yaransa da kowa da komai, shiyasa Mom na kiran sa ya taho gidan ba dan ya gama abinda yake yi din ba, a dakin suka tare gaba daya sai Safeera ce da ta soma jin bacci mom tace taje ta kwanta. Dakin ta, ta shiga maimakon ta kwanta sai ta dauki wayarta duk da kusan sha daya na dare ne, ta kira Jiddah wadda take kwance tana ta juye-juye, tana ganin kiran taki dagawa dan bata san me Safeeran zata ce ba haka itama bata san amsar da zata bata ba. 

   Da safe ya tashi da dan kwarin jikinsa saboda drip din da yasha, Daddy ya gani a dakin yana kallon sa, ya taso da sauri yazo gaban gadon nasa, 


"Isma'il, ya jikin naka?" 


Yace ba tare da yasan dalilin ciwon nasa ba dan Mom bata fada masa ba, dan yatsine fuska yayi kadan sannan yace


"Naji sauki Daddy."


"Toh Allah yakara sauki, bari naje na shirya, ka tashi kayi sallah, sai a kawo maka breakfast saboda ka kara samun kwarin jikin naka, zazzabi bashi da dadi." 


"Tohm, dan Allah amma Daddy inaso na tambaye ka wani abu."


"Ina jinka." Ya tsaya da shirin barin dakin da yake


"So nake a matso da tafiyar karatun nan, ko cikin next week ne."


"Me yasa? Da kace baka shirya ba, an samu change of plan ne ko me?"


"Eh Daddy, yanzu inaso natafi,as soon as possible, please Daddy."


"Ok, ba damuwa ka bari ka kara samun sauki, sai muyi maganar fixing date din."


"Ai na warke, please Daddy."


"Shikenan, ka same ni a falo idan ka gama."


"Nagode."


Tapping bayan sa yayi, ya fita shi kuma ya fada toilet.

   Tun last two months Daddy yake masa maganar masters da zai fara, ya dinga jan abun saboda ya samu Jidda idan yaso suka daidai ta, sai ya tafi tunda ba yawa just two years ne be ma kai ba, har yaje ya dawo lokacin ta shiga university ta fara karatun ta itama, that was his plan, sai gashi komai ya ruguje a cikin yan awowin da ba su gaza ishirin da hudu ba. Ganin haka ya saka shi yanke shawarar tafiya kawai tunda hatta admission yana dashi a hannu da komai, visa kawai zai yi applying wadda yake saka ran in a week ma zata zama ready, babu amfanin zaman sa tunda har Jidda ta k'i shi, bashi da amfanin cigaba da zama gwara yaje ya amfani lokacin da yake dashi.

   


***Duk da Jidda taga kiran Safeera kuma ta sake gani ma da safe amma ta kasa kiran ta, bata so ko kad'an su samu matsaala, ta san kuma d'aga wayarta a lokacin zai iya zama matsala tunda ta san a yadda Ya Isma'il ya fita ta kuma tabbatar da sun san abinda ya faru. 

   Aunty ce ta shigo daga part din Baba, ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a yanayin da taga Mama zata iya komai dan ganin auren nan ya baci, bata so jiddah ta shiga matsala ko kad'an musamman a irin wannan karancin shekarun nata, dama dai duk abinda ta guda kenan, dan dai su iyaye maza basa bawa ire-iren wadannan abubuwan muhimmanci ko kadan, tayi mamaki da har Maman ta dauko kafa tazo, har kuma suka samu sabani da Baba akan hakan wanda ko lokacin aurenta da Baban basu samu irin wannan matsalar ba dan Mama mutum ce me matukar kissa da iya takunta a wajen Baban dan duk wuya bata taba bari yaga aibun ta, amma kuma a yadda ta kasa dauke idon ta akan wannan auren ne ya sakata sake tsorota da lamarin.

   Wayar Jidda ce ta sake kara a karo na uku tun shigowar aunty, ta kalle ta cikin son neman karin bayani tace


"Ki daga mana ana ta kiranki kina ji." 


Yadda Auntyn tayi sounding yasa ta gane ranta a bace yake, daga wayar tayi sannan tace


"Hello Safeera."


Wani kallo Aunty tayi mata, sai ta tashi sum-sum-sum ta bar falon zuwa dakin ta, girgiza kai kawai Aunty tayi,ta shige daki itama ta hau tunanin yadda zasu fara hada kayayyakin da zasu bukata a chan din dan ba komai zasu dauka ba.


***Shiru jiddah tayi tana sauraron banbamin masifar da Safeera take akan kin daga wayarta bayan tasan dole ne ta kira ta, sai da ta gama tas duk da bata sako maganar Isma'il din ba sannan tayi shiru Jiddan ta bata hakuri


"Bana kusa da wayar ne, kiyi hakuri."


"Ko dai kika ki dagawa ba, kar nayi miki maganar Ya Isma'il."


"Ba haka bane ba fa."


"Toh me? Ni dai ban ce miki dole ki so shi ba, babu dole ai a soyayya, dama kiran ki nayi muyi wata magana amma shikenan." 


Ta wayance kawai dan bata ga amfanin dawo da maganar baya ba, ita da kanta Jiddan idan taga ta share zancen zata saki jikinta har ta bata labarin abinda ya faru.


"Dan Allah fada min, wacce maganar ce?"


"Ah ai kuma shikenan, idan kin matsu kina so kiji ki kirani da kanki."


"Toh zan kiraki, kinsan me ya faru? I'm clueless gaba daya, bansan ma wanne irin tunani zan ba."


"Oya,tell me ina jinki."


"Uhm... Jiya aka daura min aure."


"Wait what!!!" Ta fada da dan karfi dan yadda maganar tayi shocking dinta


"Kamar ya? Ban gane ba, aure kuma, da wa?."


"Ya Tariiiiq."


Dip Safeera ta dauke wuta, kamar bata kan wayar, sai da ta ja wasu yan sakanni sannan tace


"Yanzu dama all this while jidda kinsan yayanki za'a aura miki amma kika ki fada min,haka kika dauki friendships dinmu? Baki yi trusting dina ba ko? Shikenan nagode."


Ai kafin Jiddah tayi magana ta katse kiran, ta kalli wayar ta girgiza kai kawai, me neman kuka ce dama aka jefe ta da kashin awakai, dama zuciyar Safeern a kusa take da abinda ya faru tsakanin su da Ya Isma'il, sai kuma katsaham tace mata an daura mata aure bayan dah tana dan da hope din ko aka kara turawa Ya Isma'il din ya samu kanta, duk da tasan Jidda kaifi daya ce tun basu kai yanzu ba,idan tace yes toh babu abinda zai sakata dawowa tace no, haka ma vice versa.

  Sanin cewa sarai ko ta kirata ba zata daga ba, ya sakata tura mata sakon text message, tayi mata bayanin abinda ya faru a takaice, ta ajiye wayar daidai lokacin Aunty ta kwalo mata kira, da saurin ta, ta amsa ta fita dan ta lura sarai Auntyn a wuya take akan maganar auren nan.

   A daki ta sameta ta fito da kayan wardrobe dinta gaba daya, tana ware su,zama Jiddan tayi ta shiga tayata, anan take fada mata maganar tafiyar, shiru tayi dan bata kuma san kalar sabuwar rayuwar da zasu fada ba, tun bayan komawar Maman Abuja aunty ta samu yancin kanta, bata da wata damuwa dan idan ba sallah da akayi ba suka zo babu wani abu da yake hada su waje daya, shima har a gama hutun sallar su tattara su koma ba wani zama Maman take a gidan ba,kullum cikin fita take.l shiyasa yanzu take hasaso irin zaman da za'a yi, gata kuma, wanne irin tarbar Maman zata yi mata? Shin zata taba karbar ta kuwa a matsayin matar Baban danta? Toh wai me da sanin ta kuwa akayi auren nan? Sai ta tuna da sunan bararojin da ta taba kiran ta dashi cikin son nuna kaskancin ta, ajiyar zuciya ta sauke, dan tasan tabbas akwai kalubale babba a gabanta, amma koma menene tana rokon Allah ya duba ta, ya kawo mata sauki.

   Suna aikin Aunty na kokarin nuna mata rayuwa da kalubalen da yake cikin rayuwar aure, taana ji tana kuma daukar komai a kanta, har suka kammala aikin taje ta zuba abinci ta koma dakin ta, taci sannan itama ta hau ware kayan nata, tana daukar wanda zata bukata ta. Hakan ya jata har yamma dan sai da ta hada komai kaf dan zataje tayi kwana biyu a gidan su kafin ranar tafiyar da zata dawo ana I gobe. Sai da ta gama tas sannan ta dauki wayarta, taga reply din safeera, tayi murmushi kawai ta sake tura mata wani,


_"Wednesday zamu koma Abuja."_


Sakon na shiga ta biyo shi da kira, ta dauka tana murmushi dan tasan wata masifar ce


"Nima wallahi dazu na san da tafiyar." Tayi saurin cewa tana dariya


"Allah Jidda ko? Yanzu dan Allah shikenan tafiya zakiyi ki barni? Ni kadai ga Ya Isma'il shima tafiya zai,haba dan Allah."


"Zamu zo sallah fa, ko weekend nasan ba wai mun tafi gaba daya bane, ni ma ba son tafiyar nake ba, kinga achan zamu fara school ni da Amira shiyasa ma."


"Ai shikenan, zan shigo gobe."


"Ok Allah ya kaimu, sai kinzo."


"Amin, bye."


"Bye."


Maimakon ta ajiye wayar sai ta samu kanta da shiga photos din wayar, ta bude hotunan sa, tana dubawa,tana tuna wai mijin tane,an daura musu aure, bata san me take ji game da hakan ba, kawai tasan tana jin ta at ease, bata da wata damuwa ko fargaba a zuciyar ta. Ba kamar idan taga Isma'il ba, ba kuma kamar ace Isma'il aka aura mata ba, ta tabbatar zata iya bori akan hakan.

    Ya Fauwaz ne ya kirata, tana dagawa ya hau yi mata kirari


"Kaga amaryar Ya Tariq, kaga amaryar Captain Tariq, kaga amaryar international pilot, eh Masha Allah, ban taba ganin perfect couples irin ku ba, kun yi matukar dacewa, da za'a bada award za'a iya baku award din perfect couples of the year."


Dariya take tunda yafara maganar, 


"Kai Ya Fauwaz." Tace farin ciki na mamaye zuciyar ta


" Allah da gaske Jiddo, auw Aunty Jidda."


"Na shiga uku, nice Auntyn?"


"Emana, kin zama matar Big B, ai dole ace miki Aunty."


"Kai dai Ya Fauwaz ka iya tsokana wallahi."


"Allah ba tsokana bace, da gaske nake. Har Allah, Allah nake ya Tariq ya dawo yaga amaryar sa, nasan ji zai yi kamar an tsunduma shi a aljanna."


"Hum umm." Tace tana giggling 


"Toh ya ake ciki?"


"Alhamdulillah wallahi."


"Toh Masha Allah, dama nace bari na kira matar yaya, kar ya dawo yace mun bar masa mata babu kulawa."


"Ya Fauwaz ko?" 


"Na barki lafiya toh."


"Nagode."


Wani irin dadi ne ya rufe ta, dan ba karamin dadin kalaman Fauwaz taji ba, ya bata kwarin guiwa sosai wanda har ta soma hasaso rayuwar ta anan gaba kad'an. Murmushi tayi tana lumshe idanun ta, ta furta a hankali.. Matar Ya Tariq


***Washegari da wuri Safeera tazo, suka shige daki suka shiga hira, har kusan azahar sannan ta je ta kawo musu abinci suka ci sukayi sallah, sannan Safeeran tace zata tafi dan Mom ma da kyar ta barta tazo dan dai tana son duk abinda suke so ne, mayafi ta yafa ta rakota gate in da driver gidan su yake jiranta. Hakurin abinda ya faru tsakanin ta da Ya Isma'il ta bata dan duk yadda taso dauko maganar da suna ciki Safeeran taki yarda da ta dauko maganar sai ta goce da ta sake daukowa sai ta shashantar da maganar ko ta nuna bata ma ji ba. Yanzun ma tsaki tayi kawai ta harare ta,ta shige mota. Part din Yaya ta wuce ta sameta kafarta na mata ciwo, ta dauko maganin da ake shafa mata, ta shafa mata a kafar sannn ta zauna tana rage mata zaman kadaitar.

[

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links