ELHAJJ 7

 


🤎🤎🤎🤎

                    *ELHAJJ*

                                  🤎🤎🤎🤎


Free page 7

    

   Written by

        Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387



*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃



*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*



*LOCATION KANO*


08062073990


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



  Ina gama wankan na shiga daki, a gaggauce na shirya cikin doguwar riga na fito na dora ruwan xafin Koko.


Kafin Mama ta fito har na gama dama koko na zubawa ko wanne daki a cikin jug dinsu, daukar namu nai na kai daki.


Ina cikin shan koko Mama ta shigo cikin atampa sai kamshi take, wannan dabi'ar tace tunda na tashi haka nake ganin tana yi kullum tace dakin Baba toh in zata dawo kullum a shirye zaka ganta fess tayi wanka tana kamshi.


Gaishe ta nai ta amsa fuskar ta adan sake, zama tai tana fadin "ko ke fa gashi nan kinyi wanka tsaf da ke amma ki dinga zama da kazanta nidai nasan wannan na dabi'a ta bace Sam".


Sunkuyar da kai na nai kawai ina juya cup din koko na a hannu, tabe baki Mama tai tace 'ban gane wannan sunssunkiyar da kan da kike ba, ko ni dince baki gane ba".


Murmushi kawai nai gabana yana faduwa, ai ni yau banga ta magana ba tunda nasan abinda naje na hada a gidan Inna.


Ganin naki magana kawai Mama taja tsaki tana janyo jug din zata hada nata Kokon tace "ke kika sani kuma, wannan sabon munafurcin in ma don na yadda ne kije kina aiki a gurin wani gardi toh a banxa don ba yadda xan yi ba".


Turo karamin bakina nai ina mikewa tsaye, fita nai daga dakin na kai cup din gun pampon mu da yake tsakar gida, wanke wa nai na dawo dashi na ajiye a cikin daki a wata drawer da muke sa kayan kitchen dinmu.


A dakin nayi kwanciya ta bacci ya dauke ni.


Cikin bacci naji an dala min duka a cinya, da sauri na mike ina murza idona don dukan ya shige ni sosai.


Yusrah ce a zaune tana dariya ganin yadda na tashi ina murza ido, ai ban tsaya komai ba na janyo hannun ta ta shiga dala mata duka a baya a fusace.


Dariya take kwalkwala wa tana fadin "haba Kawas Inna kiyi hakuri nidai gaskia kar ki burma min baya kinji'.


Cikin haushi nace "ban da iskanci ina bacci kawai xaki zo ki dala min duka haba banxa kawai".


Mikewa tai tana dariya tace "dallah can raguwa kawai".


Wani kallo na mata ina daura dankwali na nace wace "raguwar kema dai kinsan bani ba dai koh, sai dai in ke din".


Girgiza kai tai tace "gaskia fa, ai baxan manta cewa duka na kike ba da".


Mikewa nai ina tabe baki nace "tare kuke keda Inna?".


Daga min kai tai tana Zama a kan gadon tace "ai jiya take cemin kinzo kin ce, ta gaishe ni yau kuma da sassafe tace mu shirya muzo xata ga Mama".


Kallon ta nai naga taci kwalliya da mamaki na kama baki na xan yi magana Kenan nace "bara dai naje na gaishe da Inna sai na zo zamu yi magana".


Dariya Hafsa tai tace "oh Hajia Dije knn".


Palourn na fito anan na samu Inna da Mama suna zaune da alama magana suke yi, Mama na gani na ta galla min harara tayi kwafa.


Narai narai nai da ido na kalli Inna cike da tsoro nace "Inna kin ga Mama tana harara ta koh?".


Inna dake zaune ta dan rangwafo akan kujera tana gyada kai, kallona tai sannan ta juya ta kalli Mama tace "gaskia Maman Hajara bana son wannan abun, meye kuma zaki wani kalle ta fisabilliahi, toh ahir kar naji kar na gani kin Mata wani Abu bayan tafiya ta".


Kallon Inna Mama tai tana sunssunkuyar da kai tace "Inna bafa abinda nace xan mata".


Watsa Hannu Inna tai tace "atoh kar ki samo ma, in har da kin tsara yadda zaki lallasata bayan tafiya ta, yarinyar nan sbd ke take son fara aikin nan don ta dinga taimaka miki tunda nidai take fada min dalilan da zai sa tafara aikin nan bata ambaci kan taba, sau daya ne tace zata dinga siyo muku abin kwadayi kuna ci haba, amma ke sai kice baxa tayi ba haba haba".


Kan Mama a kasa tace "Inna ni gani nai da kinga makaranta take, gashi yarinya ce karama ga Dijen ba wani hankali ne da ita ba".


Daga ma Mama hannu Inna tai tace "dakata mana Maman Hajara taya zaki ce Kawas baa da hankali, Shekarun ta dai dai har 15, a shekarun ta fa aka miki aure da kuma kika zauna sannan kice yarinya ce ita".


Sunkuyar da kai Mama tai kasa tana jin yadda Inna take mata tonon silili, wato dai tun da ita aka mata aure a shekarun Dijen.


Gajeran tsaki Inna tai tace "sannan maganar makaranta da kike fada ina ji shi mai gidan yace Duk lokacin data tashi daga makaranta taje ai ba aikin zai hana ta ba, yarinyar nan kema shaida ce tana da kamun kai dai-dai gwargwado sannan ga baban ta shima acan yake aiki nasan zai sa Mata ido AI, nidai Don Allah ki bita da addu'a kawai taje tayi kika sani ma ko ta samo min sabon ango acan".


Kan Mama a kasa tace "toh shikn Inna, Allah yasa hakan shine mafi alkhairin sa Zan fada wa Malam din cewa na amince sai ya fadi ranar da zata fara zuwa".


Murmushi Inna tai tace "ko kefa, Allah ya miki Albarka dai".


Ni kuwa da nake gefe cikin sauri na koma daki jin Mama ta amince ina sauke ajiyar zuciya.


Kallon Yusrah nai dake waya da saurayin ta sai makale murya take, tsaki nai ina zama a gefen gadon lokaci daya ina janyo littafina na seera ina dubawa.


Sam bana Jin abinda Yusrah take fada don tayi kasa da murya sosai, ban kuma damu dana ji din ba sai dai kawai ina mamakin meye take cewa ne ita da saurayin nata nifa sam ban san me ake cewa ba in ana hira da saurayi, kuma hakan be dame ni ba Sam.


Yusrah data gama waya ta jiyo ta kalle ni tace "Kawas Inna yanee?".


Ban kalle ta ba sai ma mai da hankali na da nayi kan littafin ina dubawa sosai in da aka Kara mana.


Kwace littafin tai tace "gaskia Dije baki da kirki, kina ji ina miki magana amma kika min shiru".


Tabe baki nai ina lumshe idona nace "toh me zance Miki Yusrah na shigo naji kina waya da kato sai kashe murya kike".


Baki bude Yusrah tace "ynxu Babyn ne katoh sbd baki da kirki Dije".


Da mamaki na kalle ta nace "wai da baby kike waya dama sai wani maqe murya kike yi, baby dai da na sani inya inyaa".


Tsaki Yusrah tai tace "gaskia baki hadu ba wallahi, saurayi nane fah, ke bakya yin saurayi shiyasa baki san komai ba".


Kwanciya nai akan gado nai kwanciyar rigingine ina kallon Sama nace "toh meye a soyayyar ke nifa baxan yi aure ba sai na ga karshen boko yarinya".


Dariya Yusrah tai tace "lallai ma Dijen nan au sai kinga karshen boko, kin ga ni kuwa ina gama secondary school zan fitar da gwani na a min aure don gaskia ina bukatar sa".


Ba tare da na fahimci zancen ta ba nace "toh wai meye a cikin auren banda iskanci daga kayi aure namiji ya rike ma hannu shikenan kayi ciki kazo kana fama".


Da mamaki Yusra tace "ban fahimci zancen kiba, kamar ya daga anyi aure sai a rike ma hannu Ka samu ciki kuma?".


Kankance ido nai nace "eh mana ko ba haka bane?".


Dariya Yusrah tai tana tafa hannu tace "kar kice min baki san meye aure ba Kawas Inna?".


Turo baki nai gaba nace "na sani mana gashi ina ganin Mama kullum zata gaishe da Baba ta kuma masa girki in ranar girkin tane sannan ta kwana a dakin sa shikenan ai, yarinya ni zaki ce ban san aure ba".


Salati Yusrah take tana dariya tace "tabdijan zauna na fayyace Miki komai yarinya, ashe ba abinda kika sani".


Ta bude baki zatai magana Mama ta kwalo mana Kira, mikewa nai muka fita a tare.


A zaune a kasa muka same su suna cin abinci a plate daya, flask din abincin Mama ta nuna min tace "gashi maza dauki kuje ku ci".


Da dan mamaki nace "Mama yaushe har kika gama abincin ban sani ba?."


Harara ta tai tace "ina zaki sani kina can kina bacci".


Turo baki nai ina kallon Inna dake kallon mu itama, abinci ta kai baki tace "wai me kuke yi a daki ne?".


Dan tabe baki nai nace "Yusrah ce tace xata koya min meye aure wai ban sani ba".


A tsorace Yusrah tace "wallahi karya take Inna, ni mai na sani kuma kiji tsoron Allah Dije".


Da Mamaki nace "ke Yusrah ynxu fa kika gama cewa ni yarinya ce xaki fayyace min komai kuma sai ki Musa".


Mama dake kallon mu girgiza kai kawai tai fuskar ta a hade tace "bana son Jin irin wannan maganar daga yau kunji na fada muku?".


Daga mata kai mukai muka shiga dakin, haka muka ci abincin sai haushi na Yusrah take ji, Nima ko ajikina don nasan gaskia na fada.


Sai yamma Inna suka tafi har lokacin kuma Yusra bata min magana ba.


Bayan tafiyar su Inna, Mama ta xaunar dani tamin nasiha sosai akan Kula da kai na da kuma rike mutuncina, nidai kai na na kasa ina gyada Mata kai har ta gama.


A daren kuma ta samu Baba da maganar amincewar ta yayi murna sosai yace Mata ta fada min gobe da safe na shirya mu tafi tare tunda MD din ya riga yasan da maganar.



******

   

    Tashi yai bayan ya gama magana da Papa akan sabon companyn da yake shirin budewa, Wanda an gama komai kawai rana zai sa ya bude sa.


A gajiye yake matuka kawai dai tsabar kokari ne irin nasa da baya wasa da business dinsa, cikin part din Momma ya nufa kai tsaya, yana shiga tana fitowa daga dakin ta.


Kallon sa tai fuskar ta dauke da murmushi tace "Elhajj har kun gama maganar da Papa din naka".


Gajeran murmushi yai yana shafa fuskar sa, Zama yai akan kujera a hankali yace "Momma abinci".


Wani murmushi tai tace "ina zuwa bara naje na hado ma da kai na".


Kitchen ta nufa miyar dake cikin fridge ta dauko ta zuba a tukunya tadan Kara mata ruwa kadan, lalle kawa tai ta tabbatar ba Wanda yake shirin shigowa kitchen din ta bude wata drower a kitchen din da key, drower din ba Wanda yake bude ta don ta musamman ce a kitchen din da key take kulle ta duk lokacin da zatai amfani da ita take budewa.


Wani leda ta dakko yar karama ta bude, garin magani ne a ciki wani murmushi tai ta juye sa duka a cikin miyar, tana zubawa wani bakin hayaki ya tashi ya mamaye miyar.


Kamar 2 minutes hayakin ya yaye duka sai kamshi da yake tashi.


Juye masa miyar tai akan tuwo leda daya data sa masa, bata sa spoon ba sanin halin sa baya cin abinci da spoon sai bowl data zuba ruwa a ciki na dauraye hannu shi kansa ruwan ta sirka sa da wani rubutu fari.


Murmushi tai tana gyada kai ta dauki tray din ta nufi Palourn dashi, a yadda ta barsa haka ta same sa.


Ajiye masa tray din tai tace gashi Son maza zauna da kyau kaci favourite dinka nayi dama.


Mikewa yai sosai ya zauna yana murmushi, hannun sa ya sa a ruwan ya dauraye yana gama wanke hannun nasa kansa ya sara, bude abincin yai ya fara ci ba tare dayai bismillah ba don ya manta ma ana bismillah in za'a ci abinci a wannan lokacin.........




Elhajj kana cikin wani hali🥹


Hajia Dijen mu za'a fara aiki gobe ko ya zata kasance kuma🤔🤔



Gaskia Sisters bakwa yin comments🥹



*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300  KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA, DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


09066728387



Comments Nd share plz




Mrs A.M🥰

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links