SANADIN LABARINA 52


   Page (52)


***Abinci ta zuba ta zauna tana ci a k'asan carpet suna hira da Aunty sai gashi ya turo kofar ya shigo bakin sa dauke da sallama. A ciki ta amsa Anty kuma ta amsa a fili tana masa maraba. Yanayin da ya ganta a zaune sai ya tuna masa ita ranar da ya fara ganin ta da muryar ta kamar usur wuyanta kamar mirikin lema. 


"Barka da rana Aunty."


"Barka dai Tariq, ya gida?"


"Alhamdulillah Aunty."


"Madallah, ya shirye-shiryen tafiyar?"


"Ana kan yi, Visa din Jiddah ce dama zata dan mana delay kad'an."


Ya karashe yana kallon fuskar ta, tunda ya shigo ta daina cin abincin da take ci yana lura da ita


"Masha Allah, toh Allah ya bada sa'a ya taimaka." 


A yadda Antyn tayi maganar zaka gane cewa ba karamin farin ciki tayi ba da tafiyar Jiddan, abinda dama take ta hangowa kenan dan indai ya tsallake ya tafi shikenan kuma kashin ta ya bushe a wajen Mama da Nafi dan ta lura Nafin ce take sake zuga Mama akan Jidda,yanzu kuwa idan suka tafi ba shikenan ba?


"Bbyna..." Yayi maganar yadda aunty ba zata ji ba, dago kyawawan idanun ta tayi ta sauke su kansa, ya motsa bakin sa a hankali yace 


Kin gama?" 


Girgiza masa kai tayi ta cigaba da juya spoon din


"Ok, ki karasa sai mu tafi."


Gid'a masa kai tayi, yayi murmushi kad'an ya zare glasses din idon sa yace 


"Aunty, gobe zamu je embassy daga nan zamu wuce Kano in sha Allah." 


"Kai dama na biku kawai mu tafi wallahi." 


"Aunty mu tafi kawai toh mana." 


"A ah, babanku ma ba zai yarda ba, nima kuma tsokanar ku nake duk da inason zuwa din amma zan bari cikin next week in sha Allah."


"Toh Allah ya kaimu."


"Amin ya Allah.'


Mikewa Jidda tayi da plate din dan babu kuma in da abincin zai cigaba da shiga dan gaba daya ya hanata sakat da kallon shi duk da idon sa yana cikin bakin glass amma tsaf ta gano kallon ta yake kuma ta san shi sarai zai iya bata kunya a wajen auntyn dan shi kam babu ruwansa ko a jikin sa.


"Jidda dai wannan cin abincin na wasa me wallahi."


"Shiyasa bata kiba ai aunty."


"Aikuwa, a haka ma ai jiddah tayi kumari, sosai."


"Yanzun ma da sauran ta." Yace k'asa-k'asa amma sai da taji, ta juyo ta dan kalle shi ya motsa bakin sa yana mata murmushi ta shige kitchen din ta wanke bakin ta sannan ta fito ta wuce tsohon dakin ta, bin bayan ta aunty tayi suka barshi a zaune tana shiga ta zauna tace Jiddan ma ta zauna, rike da hisnul muslim dinta da counter sai yar jakar da sarka da abun kafar nan suke ciki da ta dauka a cikin kayan ta tazo ta zauna kusa da Auntyn


"Akwai abinda yake damun ki ne?" 


Ta tambaye ta tana kallon yanayin Jiddah da yadda take abu very cool duk da dama chan haka take amma yau sai taga ya karu. Girgiza kanta tayi


"Babu komai aunty."


"Akwai in da yake miki ciwo ne?"


"Ba ko ina."


"Toh na tura miki text tun ranar kin gani?"


"Na gani aunty."


"Yawwa, ki yi hakuri kowacce mace da kika ganta a haka ta fara, girman kenan, ke dai banda gardama dan ita ke jawo ma mutum matsala, dama dai chan kinga ba wasu uban magunguna aka narka miki ba, mafi a'ala dai shine maganin sanyi, idan aka kwana biyu da kanki zaki nemi karin wasu abubuwan ba sai wani ma yaji ba, yanzu dai ki daure kiyi hakuri na lokaci ne da ya wuce shikenan, ki gyara jikin ki da mijin ki sannan kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki."


"In sha Allah Aunty, nagode sosai Allah ya saka miki da gidan aljanna, ba dan ke ba aunty, da bansan ya rayuwata zata kasance ba, da nasan yanzu ina chan cikin wahala da tashin hankali, bani da abinda zan yi na biya ki Aunty."


"Abu daya zakiyi ki biyani, duk runtsi duk wuya karki taba bijirewa mijinki, kiyi kokarin kyautata masa sannan ki sani, soyayya karamar abu ce a zamantakewar aure, kuma ita kadai bata iya dorar da aure, hakuri da addu'a sune babban makami domin akwai kalubalai masu tarin yawa da zasu taso miki, wanda zasu bude miki ido kisan mecece ma rayuwar."


"In sha Allah aunty."



 Tace cikin muryar kuka, ita kanta tasan akwai kalubale sosai a rayuwar aure tunda taga yadda ita kanta Auntyn tayi hakuri kafin yanzu da komai ya wuce sai dan abinda ba zaa rasa ba, ta kuma ga yadda Baffan ta yasha wahala a wajen Iya Lami , sannan ga yadda Yaya a kullum take labarin wahalar da tasha a rayuwar auren duk da ba lallai dan abu ya samu wane kai ma ya same ka ba, amma idan ka sawa ranka Allah zai iya jarrabarka shikenan zaka zauna lafiya kuma cikin shiri.


   Hawaye Aunty take amma bata bari Jiddan ta gani ba, tasa bayan hannun ta, ta share sannan tace ta je su tafi kar yayi ta jira, zata aiko da sakon Baffa da zata tafi masa dashi. Tashi tayi jikin ta yayi matukar sanyi ta jawo mayafin ta har saman fuskar ta yadda ba zai ga fuskar ta ba har ya gane kuka tayi ba. 

  Waya yake ta fito tana kallon k'asa, ya zura mata ido yana so ya gano wani sauyi a tare da ita, yanayin tafiyar ta ya nuna kamar she's down, katse wayar yayi bayan ya ciro ya daga kunnen sa, ya mike tsaya ya zura ta a aljihun gaban rigar sa, ya riko hannun ta yana leka fuskar ta, hawaye ya gani yayi a kwance a fuskar tata, yasan definitely wata maganar sukayi da aunty amma be san wacce ba, baya fatan tasan maganar Salma da abinda yake faruwa wanda yayi tunanin Auntyn ma bata sani ba, tsoro ne ya darsu a ransa kar dai ko auntyn ta sani shine ta fadawa Jiddan


"Menene?" 


Yace ciki nuna tsantsar kulawar sa, gefe daya kuma yana jin tsoron amsar da zata bashi dan be san a yadda zata kalli abun ba, tunda yanzu ne ta fara sanin sa bare ta banbance abinda zai iya da wanda ba zai iya ba.


"Ba komai." 


"Tom ki daina kukan kinji? Muje mota sai ki fada min menene."


Da ka ta amsa masa, ya karbi yar jakar daga hannun ta ya rike mata dayan hannun suka fita daga falon. Motar na nan in da ya ajiye ta dan haka kawai bud'e mata baya yayi ya taimaka mata ta zauna sannan shima ya shiga da sauri, ya jawo ta baki daya jikinsa da yake motar tinted ce, kukan shagwaba ta saka masa ya rikice ya rasa yadda zai yi, ita bata san baki daya kukan ta rikita shi yake ba, kuma shine babban weak point dinsa, tapping bayan ta ya dinga yi a hankali har ya samu tayi shiru, ya zaro tissue daga saman dashboard ya goge mata fuskar bayan ya dago ta daga jikin sa 


"Menene?" 


"Ni Baffa na."


"Kike so ki gani? Shiyasa kike kuka?"


"Eh." Ta gid'a masa kai, ajiyar ya sauke da karfi jin ba waccan magaanar bace yace


"Zaki ganshi gobe in sha Allah."


"Sai me kuma?"


"Babu komai."


"Ok..." Ya zare jikinsa a hankali ya fito ya dawo mazaunin driver yaja motar suka bar gidan.



***Masifa aunty Nafi take Salma kuma na ta gursheken kuka, tsabar wulakancin abinda Ya Tariq yayi musu ace a gaban su sai dinga romancing matar sa, gashi wallahi ita da gaske take tsananin son sa da kaunar sa take kamar ta je ta shake Jidda har lahira, ita kanta Aunty Nafi taji haushin wulakanci da yayi musu ai ko ba komai ita matsayin uwa take a wajen sa, amma saboda wulakanci shine zai maida su yan iska yana rungumar mace a falon mahaifiyar sa.  Banko kofar akayi Mama ta shigo tana huci kamar zakanya, tashi aunty Nafi tayi tana kallon ta da mamaki


"Ki tattara yarki da tsummokaran kayan ki, ki bar min gida na, kuma wallahi wallahi Tariq ba zai taba auren Salma ba, tunda ke muguwa ce makira, baki duba karfin alakar mu ba, har ki kala wa dana sharri saboda kawai son zuciya."


"Ban gane sharri ba, kina nufin Salma sharri tayi wa Tariq kenan, kuma kin goyi bayan sa?"


"Eh sharri kikayi masa bakar muguwa, wallahi sai kin tafi bani ba ke kuma wallahi."


"Ahayye! Tab Amma sannu Aisha, kina nufin zaki rabu dani akan danki? Yaran yanzu da ba shaidar su ake ba?"


"Nayi, kuma kema kinsan duk abinda kuka fada akan sa karya ne, toh wallahi ko ku tafi da kafarku ko securities su fidda ku."


"Aikuwa wallahi ba zai yiwu ba, a dake mu a hana mu kuka, ba za'a bata min yarinya kuma ace zaa kore mu ba, wallahi ba inda zamu ko Tariq ya karbi Salma ko kuma zance ya karada dukka kasar nan."


"Idan kin ga dama ki dau loud speaker ki zaga kaf duniyar nan kina fada, babu abinda zai faru illa kanki da zaki WA illah, dan ko a yanzu babu me karbar yarki da wannan banzan halin nata ballantana son zuciyar ki yasa ki bata suna, kinga zata kare a haka ba aure."


Mamakin yadda Maman take kokarin wargaza musu plan dinsu ya saka jikin ta sanyi, amma sai ta hana ta gane halin da ta shiga tace


"Ai akwai hukuma ko? Wallahi sai naje sun bi min hakkin 'ya."


"Kije binnin sin ma, kuma wallahi ko a hanyar gidan mu na chan Kano na sake ganin ki sai na saka an rufe min ke an jefar da mukullin."


"Naji duk abinda kuke fada ke da yar taki kuma nayi recording din komai, dan haka sai a bi wani sarkin ,tunda baki san halacci ba."


Shiru Aunty Nafi tayi ganin dai da gaske Maman ta gano plan din su, kenan ta ji maganar ko dai so take ta sakata fara feeling quilty?


Juyawa Maman tayi ta fita, jim kad'an sai gata ta dawo da wasu masu aiki daga bq su biyu kedaru majiya karfi,suka shigo dakin tace su kwashe kayan su Anty Nafin su fitar mata dasu, tsoro ne ya shigi Anty Nafi, tana so tayi magana amma kuma tana tsoro dan bata taba ganin bacin ran Maman haka ba sai yau, dan komai akayi mata bata cika tankawa ba, shiyasa tayi tunanin zata iya amfani da wannan damar ta cutar da Maman ta kakabawa Tariq Salma ta samu hankalin ta ya kwanta.


"Ba sai an mana wulakanci ba zamu fita." Tace tana yin wajen kayan, zata taba Mama ta dakawa masu aikin tsawa tace bata son jira su kwashe kayan, da sauri suka suri akwatin tasu sukayi waje, Salma babu ko mayafi akan ta sai wata hula ita kuma Aunty Nafi sai mayafi suka fito Maman na tsaye suka wuce, already tayi waya gate tace sam ya sauke su a tasha suna fita aka saka musu kayan a booth Salma sai kuka take Anty Nafi kuma ta kasa cewa komai saboda yadda ran ta yayi bala'in baci.


Zama Mama tayi a nutse tana dafe kanta da yake mata kamar zai rabe biyu, bata san ta tara damuwa haka ba sai yau da Baba ya birkice mata, ta kuma san kafiya irin tasa shiysa ba zata taba amincewa ya aiwatar da abinda yayi niyya ba, da kanta zatayi kokarin ganin Tariq da Jidda sun bar kasar baki daya gwara su je su karata a chan duk da bata son Jiddan bata kuma san yaushe zata so ta ba amma gwara ita akan salma.da ta gama saida mutuncin ta a titi.

  Maryam ce tazo ta zaune a gefen ta, ta dago tana kallon ta sai ta girgiza kanta


"Ya akayi? Zaku je gidan Safiyya daga nan ku wu kaiwa Umaima kaya."


"Ok sai muje gidan Ya Tariq?"


"Bana son neman magana."


"Dan Allah Mama, ba zamu dade ba."


"Toh naji, idan kunje KU gaishe su "


"Har Jiddah?"


"Ban sani ba." Tace tana jan tsaki


"Wai Mama, Anty Nafi yar gidan ku ce itama Hajiya Babba ce ta haife ta?"


Girgiza kanta tayi


"Bamu da alaka ta jini ko kad'an, yar abokin Alhaji ce, zumunci irin na da da iyayen suka rasu shine aka bawa Hajiya Babba ita dan dama gida daya muke tun a dah, shine muka taso tare babu wani banbanci, amma kinga ai yanzu ta nuna min jini ba karya bane ko? Tunda na tabbata abinda tayi min Mimi ba zatayi ba, anyways, we learn from our mistakes, ya wuce in sha Allah."


"In sha Allah." 


"Tashi kuje kar kuyi dare."


"Ok ina kayan suke."


"Suna cikin daki na, ki taho min da wayata na kira Dr Iman tazo tayi mun bp."


"Ok mah." Ta wuce ciki ita kuma Maman ta kurawa waje daya ido tana tuna abinda ya faru.

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links