SANADIN LABARINA 51

 

  ©®*_*_Hafsat Rano_*_*


                  Page (51)
***Da kansa yake driving din hannun sa daya akan steering while dayan na rike da hannun ta dake saman kan gear yana murza shi a hankali. A haka suka karasa gidan da yake dan cike da mutane saboda dawowar Baban. Sai da ya shiga ciki sosai sannan yayi parking. Da dan saurin ta, ta kama handle din zata fita ya riko ta, ta juyo yayi kissing din lips dinta sannan ya cire mata lock din, murmushi me tsada ta sakar masa, ya maida mata sannan ta fita, yana kallon ta har ta shige ciki, kashe motar yayi ya fito yana saka bakin shade ya toshe idon sa.


   Da Usman ta fara cin karo ya dane ta yana kiran Ya Jidda. Da sauri Aunty ta fito sai ta tsaya tana kallon Jiddan cike da mamakin ganin ta


"Wa nake gani?"


"Aunty nice." Tace a kunyace tana rike hannun Usman din da yake cike da murnar ganin ta


"Lallai sannu Tariq, shine ya sako ki a gaba kuka taho gida?"


"Kai Aunty, ina wuni?"


"Lafiya Lou, toh ai gaskiya ce, kwana nawa yau dududu."


"Ai an daina irin wannan aunty."


"Lallai, toh kuna lafiya dai ko?"


"Eh aunty." Tace a dan kunyace tana tuna abubuwan da suka faru tsakanin ta da gogan nata


"Ya targaden?"


"Alhamdulillah, yayi sauki."


"Masha Allah, Allah ya kara sauki, na zata ma fa gobe Tariq din zai tafi. Shiru kuma ban ga yazo ba."


"Nima dai ban ga yana shirin tafiyar ba."


"Ok kila ya d'aga, anma naga ya karbi passport dinki? Ko tare zaku tafi ne?" 


Ta dan bigi cikin ta, girgiza kai jiddah tayi


"Nima dai ban sani ba, ranar dai yace min wai zan bishi?."


"Sai kika ce a'ah?"


"Ban ce komai ba."


"Kaji sokuwa, me zaki zauna kiyi bayan zaman jiran sa da kikayi a baya? Sannan ke ba kin huta da kowa ba, ba'a ganki ba bare a kafa miki kahon zuk'a."


Shiru Jiddan tayi, dan ita har hango tafiyar tasu take tare kawai dai bata son nunawa auntyn ne


"Kin je kin gaida Maman Fauwaz din ne?"


"A ah nan ya fara kawo ni, yace zai ga Baba ne."


"Ok, sai kuje da Usman ki gaishe ta, Yaya ma tana nan tana jiranki, kun mata laifi wai."


"Innalillahi, Hajiya Yaya."


"Zakuyi mata bayani tana nan tana jan maganar dan sosai ranta ya baci wallahi."


"Ni wallahi bani bace Ya Tariq ne."


"Sai kije ki bata hakuri, dan shi kam dama sun saba."


"Taso Usman ka rakani."


"Bari na karasa shiryawa kafin ku dawo."


"Ok." Tace ta kama hannun Usman suka fita bayan ta gyara yafen mayafin ta sosai dan ta lura baya so


***Wajen Mama suka fara shiga bata nan tana part din Baba, tana zaune bata ma san Maman bata nan ba Maryam ta fito da murnar ta sai ga Amira ma sun fito tare da Salma. Chak ta tsaya tana kallon Jiddan dake zaune suna magana da Maryam. Wani kululun abu ne ya zo mata makoshi, ta karaso tana yamutse fuska ta zauna a kujerar dake gefen su tana dauke kanta ta dauki remote tana kokarin chanja channel. Babu wanda ya kulata a cikin su duk sun rude da ganin Jiddan a ganin ta ma kamar sun kasa zama waje daya musamman Amira da take tsokanar Jiddaan da tayi fresh ta kara haske ita kuma tana cewa taji tsoron Allah. Tsaki taja wanda ya jawo hankalin su kanta, ta tabe baki tana kallo TV


"An bi an ishe mu da ihu kamar yau kuka taba ganin ta."


"Ina ruwanki?" Maryam tace tana hararar ta


"Kinsan ta Mero, wai Ya Tariq fa take so ashe shine duk tasa wa Jidda kahon zuk'a."


Gaban Jiddan ne ya fadi maganar ta dan tsorata ta, Amma sai ta daure tace


"Ayya abun tausayi, ai Baby nawa ne ni kadai, ta gama haukan ta, ta hakura na tsare gaba na tsare baya."


"Correct my girl." Maryam tace sai sukaa tafa da Amira suna kwashewa da dariya 


"Zan baku mamaki wallahi dukkan ku. Mtsw!" 


Ta mike sai gashi ya shigo, ita kadai ta ganshi dan su suna kallon ciki ne basa ganin me shigowa, kuma ta kofar baya ya shigo alamun daga wajen Baba yake


"Allah nasan irin su Ya Tariq ba dai iya love ba, kinsa masu shiru-shirun nan wallahi hmm, bomb!!!"


"Ba ruwana idan yaji ke kika sani." Tace tana musu dariya, Maryam ce ta karbe


"Ai gaskiya ce ,Allah sa nima Salim dina ya iya soyayya, mu soye mu rakashe abun mu."


"Amin wallahi."


"Ehem ehem."


 Yayi gyaran murya yana gimtse fuskar sa, yaji duk abinda suka ce tun daga farkon hirar da Jidda ta kirashi da baby da kuma wadda suke yi yanzu, dadi daya yaji da Jidda tayi hankalin boye sirrin su, wanda mata da yawa yanzu suke bayyana sirrikan su ga kawayen su bayan haramun ne Allah ya hana. Diriricewa Amira da Maryam suka yi dan basu taba kawo zai shigo shashen ba, idon sa akanta tayi saurin sadda kanta k'asa l"Ya Tariq sannu da zuwa, ina wuni? A kawo maka ruwa?


" Ko juice?" Maryam ta ce 


 Duk sun rikice musamman da suka san ya ji komai da dukkan alamu


"Munafukai." Yace a hankali, zamewa sukayi suka gudu ya zama daga shi sai Jidda sai Salma dake tsaye kaamar wanda aka dasa a wajen


"Come here baby." Yace yana nuna mata gefen sa da yake zaune, pretending kamar be san da zaman Salma a wajen ba, wanda yake ji zai iya tashi ya jata har waje sannan yace securities su yi mata shegen duka ita da uwar ta. Har ba zata taso ba saboda kar Mama ta fito sai kuma ta tuna da Salma dake falon, tashi tayi a nutse ta isa wajen nasa maimakon ya barta ta zauna a gefen sa sai kawai ya dora ta akan cinyar sa, wani irin waro ido tayi tayi kamar zata tashi ya zagaye ta da hannun sa ya hanata tashin yana kashe mata ido daya


"Maama?" 


Tayi kamar a hankali wanda shi kadai zai iya ji, yasan Mama ba zata shigo yanzu ba shiyasa ma yayi hakan.


"Nayi missing dinki, so much."


Yace yana saka hannun sa ya gyara mata lipstick din bakin ta yana kallon yadda lips din ta suke shining kamar yayi kissing dinsu.


Da sauri Salma ta juyo yaji sanda ta bud'e kofa ta shige ya saki murmushi yana gid'a kansa. Yunkurawa tayi zata tashi again ya sake hana ta


"Karki kara kokarin tashi idan bani nace ba." 


Kofar ce ta sake budewa sai kuma salati ya biyo baya da karfi, Aunty Nafi ce Salma na bin bayan ta


"Tariq menene haka? Wanne irin rayuwa ce wannan?"


Yi yayi kamar be ji ta ba, ya kusanto da bakin sa daf da na Jidda da kunya ta hanata ko da motsi ne, bata san dalilin sa nayiin hakan ba,ji tayi yayi mata peck a gefen kuncin ta, zuwa lips dinta na sama, yayi kamar zai hade bakin su waje daya da sauri Aunty Nafin ta tura Salma suka koma dakin ganin abin na Tariq yafi karfin tunanin ta. Cikata yayi ta tashi da sauri tana kin kallon sa,shi kuwa murmushii kawai yake idon sa a toshe da bakin glasses. 


"Kananan marasa mutunci." 


Yace a zuciyar sa yana relaxing sosai a saman kujera. Hanyar fita tayi ta dago ya kalle ta


"Baby ina zaki?"


"Wajen Yaya."


"Ok bari na zo muje." Ya mike tayi saurin cewa


"Dan Allah kar muje tare."


"Why? Ke da babyn ki?"


"Ni dai dan Allah."


"Me yasa toh?"


"Kunya zaka sa ni ji."


Dariya yayi k'adan ya koma ya zauna


"Shikenan sai kin dawo."


Juyawa tayi ta fita shi kuma ya cigaba da zaman jiran Mama wadda ya baro su suna fafatawa da Baba akan abinda ya faru.


**Kaamar munafuka haka ta shiga wajen Yayan tana labewa, Sarai Yaya ta ganta amma ta maze ta tsuke fuskar ta tana yin kamar bata ga Jidda ba


"Assalamu alaikum." Tayi sallamar tana shiga gaba daya


"Amin." Yaya tace a gajarce


Kusa da ita Jiddan ta zauna ta kauda kanta gefe ta koma dayan gefen ta sake dauke kanta, 


"Dan Allah Yaya kiyi hakuri."


"Da akayi me?" 


"Komai ma, dan Allah wallahi ba laifi na bane Allah Yaya, dan Allah."


"Ba dai kin zabi miji ba? Ke dadi miji ko? Har kike rawar kai ki shige dakin miji da tsakar rana kiki fitowa ko?"


"Na shiga uku."


"Kiyi hakuri dan Allah."


"A ah ai ba komai, ba komai kinji? Masu hali irin Malam ma kaza aji ya ka cika bare kana bin su, ni da zan siyar miki kima da darajar wajen sa shine kika watsan k'asa a ido kika shige daki kukayi mukus ko? Dadi aure "


"Na shiga dari ma ba uku ba." Ya furta a hankali, sai kuma a fili tace 


"Ba haka bane Yaya, kiyi hakuri ni dai dan Allah."


Noke kafardar ta, tayi


"Dan Allah Yayarmu, Hajiya Yaya ikon Allah, ki taimaka kiyi hakuri ko na zauna na fasa komawa.""Ki zauna a ina?


"Anan."


"Kaji mukafukar yarinya, ni zaki ma kinibibi?"


"Da gaske Yaya."


"Wasa kike ko?"


"Da gaske mana."


"Toh ma hakura,."


"Ni idan bakya so sai nayi zamana anan din kawai."


"Nace miki na hakura, ba in da zaki zauna da ya wuce dakin mijinki, na bar maganar ma kwata-kwata, shikenan?"


"Toh shikenan Yaya, amma da..."


"A bar maganar, samo min yoghurt a firij na dan sha."


"Hajiya Yaya da cin dadi."


"Arzikin d'a, ke ma ki zage jiki ki zazzago su baka san wanda zai jikan ka ba."


"Nawa ma kikayi Yaya?"


"Sha hudu nayi."


"Wai!"


"Biyar ne suke raye a yanzu."


"Masha Allah."


"Haka mukayi haihuwar nan da wahala ma ba irin ta yanzu da gata yayi muku yawa ba, wai tsabar lalacewa wai da miji ake jego, mu zamanin mu ka isa? Ai kai da miji sai kayi arba'in har ba irin Malam masu bakin hali ba."


"Zamanin ne ya chanja Yaya."


"Ai na gani, sai a shige daka da miji a bar me zaman dabaro tana hamma da zare ido, yaran yanzu sam basu da ta ido wallahi."


"Zamanin ne fa Yaya."


"Ai sai ku karata ga ku nan gasu, shiyasa ni ba gidan wadda zanje zaman dabaro kin ganni nan, kowa ya karata chan."


"Uhum." Jidda tace tana hasaso yadda zata kaya idan akace wai itace da ciki ko zata haihu.


***Fada sosai Baban yake ya dauki waya ya kira Tariq yace ya dawo, dama cewa yayi ya basu waje zai kirashi, sai gashi nan ya shigo ya kalli Mama da take cikin tsananin tashin hankali, ta so ita ta fara sanar da Baba maganar tayi masa bayani yadda zai gane amma sai akaci rashin sa'a ya sani wanda bata san ta wajen wa ba, amma kuma yace text akayi masa shiyasa tayi tunanin Nafi ce ta tura masa text din, bata san haka zata mata ba, gashi ta kara sata a matsala dan Baba yace babu ruwan sa tunda har ta iya tura Yara gidan Tariq din duk da tasan rashin dacewar hakan shima kuma ba zai iya komai ba illa ya tursasawa Tariq din auren Salmar kamar yadda yace Maman na so tunda da bata so ba zata fara tura su ba, babu irin bayanin da batayi masa ba akan Nafi karya take amma fafur yaki yace dama ai ya gaya mata tun ba yau ba, ta fita daga harkar gidan Tariq amma taki, shikenan tunda har ta zabi hakan dama kuma bata son jidda sai ya auri Salman dan ya gaji da halin ta.

  Gefen Baban Tariq ya zauna Baba ya kalle shi ya nuna sa da hannu sannan ya nuna Maman


"Ga uwar ka nan, tasan duk abinda yake faruwa saboda son zuciyar ta, ta jawo maka matsala da kanta, bani da abinda kuma zan yi akan wannan maganar dan ko zuwa sukayi suka fadawa duniya sun bata min suna, babu kuma wanda zai yarda da mu, duk da su kansu illa zasuyi wa kansu babba amma mutane basa gane hakan idan har suka rasa abun da suka kwalla fa rai akai basu samu ba, toh sai su yi kokarin shafa maka bakin penti, yanzu zamani ne na social media kuma duk abinda aka ce siyasa ta shigo zakayi kokarin kare mutuncin ka da martabar iyalin ka dan abu kad'an sunan ka zai karade ko ina, bani da niyyar tursasa maka aure a wannan lokacin, amma tunda har ban isa na saka ko na hana mahaifiyar ka ba, shikenan gata nan,kaje ka fara shirye-shiryen auren Salmar, idan yaso sai ka ajiye Hauwa'u a gida kaamar yadda take so, ka dauki matar da ta zaba maka ku tafi"


Da sauri Tariq ya dago kansa da yake duke, ya kalli Baban


"Sai ka fara shirye-shirye dan babu lokaci, abinda mahaifiyar ka take so ne, tunda ita Hauwa'u ba 'ya bace a wajen ta,amma ta sani, tana da 'yaya mata duk abinda kayi wa dan wani kaima sai anyi wa naka."


Kan Tariq a k'asa ya kasa motsawa dan be yi tunanin abinda Baban zai ce kenan ba, bayan yayi masa duk bayanin da zai masa kuma ya gamsu ya amince, amma kuma sai yaga Baban ya chanja baki daya kamar bashi ba, tashi Mama tayi dan tasan ko me zatayi ba zai saurare ta a lokacin ba, shiyasa kawai taga gwara ta fita zuwa sanda zai huce, sannan taje ta samu Nafi suyi duk wacce zasuyi dan wallahi da Tariq ya auri Salma gwara ta hakura da Jidda duk da bata son ta.

  

Yunkurawa Tariq yayi zai bi bayan Maman bayan yayi godiya a ciki ciki Baban ya dakatar dashi yace ya zauna, zama yayi ya tankwashe kafarsa


"Na kira wani a embassy, yace ku shiga gobe da safe, idan yaso daga chan sai ku wuce kanon."


"Na'am?"


"Eh, sannan akan maganar da mukayi yanzu..."


"Baba dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya auren yarinyar nan ba."


"Na sani, kuma nima ba zan bari ka aure ta ba ,inaso mahaifiyar ku tayi hankali ne, ta ajiye duk makaman yakin ta,ta rungumi Jiddah dan idan aka tafi a haka ko 'yaya kukayi zata iya kin su, tunda tana kin uwarsu."


Ajiyar zuciya ya sauke me karfi wadda har sai da ya bawa Baban dariy


"Jairi, kannen ka mata ne suka sanar dani duk abinda yake faruwa tun ranar da uwata suka zo gidan, nayi shiru ne ina bibiyar komai,."


_"Ashe yaran nan suna da rana."_ yace a cikin zuciyar sa, godiya ya sake yiwa Baban yayi masa sallama ya fito ya wuce kai tsaye wajen aunty dan yasan anan zai tarar da ita


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links