SANADIN LABARINA 42


  Page (42


Mota ya koma ya dauko bakin glass dinsa ya saka sannan ya shiga wajen Yayan, share shi tayi har ya zauna yana kallon ta, ta cikin glass din yana so yayi dariyar yadda ta turbune fuska ta kautar da kanta a dole ba zata kalle shi ba


"Ina kwana?"


Shiru


"Yaya ina kwana?"


Nan ma shiru kamar ba da ita yake ba, waka ta fara tana karkada kanta tana  habaici abinda ya bashi dariya yayi k'adan yana mikewa


"Tunda ba zaki kulani ba bari na tafi."


"Da uban me ya kawo ka? Ko ka nuna min ku tantirai ne kaida Jiddan?"


"Me mukayi?"


"Oho, duk abinda ma mutum yayi dan kansa."


"Kizo mu tafi ki bini toh."


"Idan na bika ba suna na Hadiza ba kenan, ni da gidanku ai har Abada, Allah ya taimaka ya bada sa'a."


"Toh kiyi hakuri kinji?"


"Ni kyale ni, sum-sum dakai kamar mutumin arziki, har ita Jiddan ashe itama munafuka ce, za tazo har in da nake ne."


"Kunfi kusa." Yace yana mikewa


"Sai kinzo Yaya."


 Ya zura hannayen sa cikin aljihu ya fice, ya nufi wajen masu gadi ya zauna yana sauraron hirar da suke duk da be saka musu baki ba, hakan ba karamin dadi yake musu ba, sam yaran gidan kaf basu da girman kai ko kadan haka ma fauwaz da yafi Tariq din magana yake zama dasu har suyi hira sosai. Ana haka shima Fauwaz ya dawo ya sameshi a wajen zai zauna yace su je ciki. Tashi yayi yabi bayan sa suka jera yana tambayar sa karfe nawa su Baba suka tashi. Suna shiga ciki ya kama hannun Fauwaz din ya murde shi ya baya, ya fara ihu


"Washhh!!! Da zafi fa."


"Me yasa mukayi magana kaje ka fadawa J..."


"J?"


"Jidda."


"Oh wacce magana?" 


"Maganar da mukayi ranar da na dawo, how comes ta sani idan ba fada mata kayi ba."


"Oh tab! Ai tana tsaye time din tazo kawo maka ruwa da juice taji komai."


"Shit." Ya sake shi yana dunkule hannun sa


"Me ya faru?"


"She's punishing me."


"Kamr yaaya?"


"Tace na kyale ta, naje na nemo type dina, and since then ta daina kulani."


"She's right, shine zaifi sauki."


"But ai da ba haka take acting ba, tana min magana ko da kadan ne, yanzu fa ko kallona batayi, kaamar ma ta tsane ni."


"Abun ya dameka sosai?"


"Sosai, yadda baka tunani, I'm thinking of not going again, bansan idan na tafi ko zata ce ta fasa ba."


"Then kayi mata bayani."


"Na me?"


"Kace mata mistake ne ba abinda kake nufi ba, ka fada mata you want her so bad baka so ka rasata, da dai irin wannan stuffs din, ka dai gane."


"Wa ni? Noo ba zan iya ba, kawai dai bana so ta daina min magana, amma ni ba zan iya karya ba."


"Karya?"


"Ehen, na fadi abinda nasan ba haka bane."


"Tirkashi, then ka kyaleta kawai, tana da every right da zatayi fushi ta daina kulaka, let her be, zan mata magana idan Baba yazo sai ta same shi nasan zai fahimce ta, kai kuma sai ka samo type dinka, a think hakan yayi."


"Idan ka fada mata haka wallahi zan iya fasa bakin ka, ni ba haka nace maka ba,I just need a solution ne kawai."


"Toh Ya Tariq ya za'a yi? Baka son ta, she's not your type, dan babu bukatar cigaba a zaman ku tare, free her Dan Allah, nasan zata samu..."


Ai be kai karshe ba yaji ya bige bakin sa, ransa a bace ya balbale shi da masifa, kar ya ya sake ya kuma sako maganar wani, sai da ya gama sannan Fauwaz din yace


"Kayi tunani dai, if not zaka rasa Jidda."


 "Idan Mama ta dawo kace mata nazo, I'm going."


"Ok."


Juyawa yayi ya fita shi kuma Fauwaz ya zauna yana mamakin ace wai Ya Tariq din ba zai iya gane halin da yake ciki da kansa akan jidda ba, ko kuma dai ya gane kawai dai tsabar ki fadi ne be sani ba, shafa bakin sa yayi Allah yaso be fasa masa shi ba a garin kishi dan yau zai je wajen Hidaya da yamma.

    

Da hannu daya yake tuki dayan yana danna counter kansa a gaba yana kallon titin da yake dauke da tsirarin ababen hawa, gida ya nufa tunda ya baro gidan su yayi zaman sa a central mosque sai da akayi magriba sannan ya nufi gidan kansa cike taf da maganar Fauwaz da ya wuni yana bitar ta ya kasa gano in da ya kuskure, a tunanin sa baya bukatar ya bude baki ya fad'awa Jidda komai, ba kuma ya jin zai iya nan kusa amma kuma ya kamata ace ta masa uzuri ta gane yadda ya damu da ita sosai, sau wajn goma a yinin ranar yana gwada kiran wayarta sai tayi kamar zata shiga sai ya katse yana maimaitawa kansa babu amfanin kiran.

    Horn yayi Yahaya ya taso da gudu ya bud'e get din ya shigo yayi parking sannan ya fito ya jefawa Faisal key din, ya gaji da tuki ba zai sake ba har sai ya dawo, Kano zasu je jibi kuma a jirgi zasu duk abinda zai taso ma a cikin garin Faisal din ne kawai zai kaishi


"Akwai baki a gidan ne?"


"Eh Amira ce da wata."


"Ok." Yace yana yin gaba, sai kuma ya juyo


"Ka zama a kusa ko yaushe zan iya kiran ka, a wanke black car din chan da ita zan fita gobe in sha Allah."


"Ok sir, an gama."


Haurawa yayi zuwa kofar da zata sadaka da cikin gidan ya sa key ya bud'e, suna zaune su uku a falon Jidda da Amira na zaune a kujera daya sai Salma dake kwance tana danna waya, da sauri ta tashi zaune tana gyara zaman ta, riga da skirt ne a jikin ta da suka dan kamata babu ko mayafi, tunda tazo uffan bata cewa Jiddan ba, itama bata kulata ba suna ta hirar su da Amira har Ya Safiyya ta kira Amiran tace ta bawa Jiddan ta tashi daga wajen taje sukayi wayar ta dawo ba tare da sun ji me suka tattauna ba.

   Mikewa tayi tana fadada fara'ar fuskar ta, ta nufe shi daga in da yake tsaye yana zare takalmin kafarsa daga tsaye, kallon ta yake tana karasowa har tazo daf dashi, ta dan russuna kad'an tace


"Sannu da zuwa." Fuskarta dauke da murmushi, murmushiin ya maida mata yace 


"Thank you." Yana mika mata hannun shi, dan noke kafadar ta tayi ta mika masa hannun a kunyace duk nauyin shi da su Amira dake zaune a wajen na cikata, amma dole tayi bayan wayar sa sukayi da Ya Safiyya dan ba zata taba bari Salma ta samu galaba akanta ba. Idon sa akan lips dinta da yasha jan janbaki me kyau da sheki, kamshin turaren da tayi amfani ya cika ko ina ya sashi a wani yanayi. Hannun ta sarke da nasa suka karasa shigowa tsakiyar falon 


"Ya T... welcome." Salma tace haushin Jiddan da abinda ta aikata na tike ta


"Yawwa." Yace yana kallon Amira da kunyar zuwan musu gida duk ta cikata


"Welcome Yah."


"Kece munafuka ko?" Yace yana hararar ta


"Allah Ya ba ruwana wallahi."


"Naji." 


Yace suka wuce zuwa kofar da zata kaisu dayan falon, yasa hannu ya bud'e musu ska shiga, suna shiga tayi saurin janyewa tana kin kallon sa, tsayawa yayi saroro yana duban ta, dakin ta, ta shige ta barshi a tsaye a wajen cike da mamakin ta!


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links