SANADIN LABARINA 41

 
                  Page (41)


***Ya dade a zaune a falon dan anan ya kusa cinye fiye da rabin daren sa hoping ko zata bud'e amma har ya gaji ya tashi ya shiga ciki ya gyara pillows din dake kan doguwar kujera dake dakin ya kwana dan baya jin hawa gadon. 

   Juye -juye ya dinga yi yana tunanin maganganun, ya fadi dukka kuma ko kad'an yasan be kyauta ba, ya yi kuma dana sanin furtasu duk da be yi tunanin Fauwaz zai fada mata ba, tunda shi dai ba a gabanta yayi waccar magaanar ta farko ba, ko shine dole yaji babu dadi ita ta ma yi hakuri sosai.   Kunya ce ta lullube shi tunawa da yadda ya gama cika baki kuma yazo yana kissing din yarinyar mutane bayan ta san duk abinda yace a kanta. Fauwaz ne ya cuce shi tunda dai da be fada mata ba fuskewa kawai zai yi duk da ya taba fada taji ya san kuma taji din amma maganar bata kai munin wannan din ba.

   Da wuri ya tashi bayan ya samu yayi baccin kad'an, ya fito falon ya zauna sanye da jallabiya me gajeran hannu yana jiran fitowar ta. Bayan kusan awa daya da zaman sa sannan yaji ana murd'a key din dakin, yayi saurin dauke kansa  daga kallon dakin ta fito fuskar ta a gaba bata ko kalli bangaren da yake ba, ta fice zuwa dayan falon na farko in da ta shiga kitchen ta duba abinda zata duba ta dora ruwan tea, falon ya dawo ya zauna idon sa na kan kitchen din yana jin motsin ta, ya kunna TV pretending kaamar yana kallo ne amma rabin hankalin sa yana wajenta. 

  Godiya taje ta kirawo tazo ta tayata ta soya musu doya da egg sauce ta dafa ruwan tea me kayan kamshi ta jera  akan saman Iceland din ta zuba ma Godiya nata tace taje taci sai tazo ta gyara kitchen din. Karba tayi ta fita daga kitchen din ita kuma ta d'aga cikin wajen oven din zata saka ragowar man da tayi amfani dashi ya shigo ya tsaya daga jikin island din yayi folding hannuwansa a kirjinsa yana kallon bayan ta. Dagowa tayi ta juyo ta ganshi tayi saurin dauke kanta ta dau plate din da ta zuba nata rike da cup tazo zata wuce shi.

   Saurin tare hanyar yayi ta dan ja baya da sauri


"Goodmorning tunda baki iya gaisuwa ba."


"Ina kwana?" Tace a gajarce ta nuna masa hanyar


"Zan wuce." 


"Fushi kike dani?"


Girgiza kanta tayi,


"Ni ba fushi nake ba."


"Toh menene, kika chanja all of a sudden."


"Ba komai, zan wuce."


"Ba in da zaki, sai kin fada min."


Ajiye abun hannun ta tayi a gefen Iceland din ta wuce gaban sink ta soma wanke kayan da suka bata da ta barwa Godiya ta wanke. Jan daya daga cikin kujerun dake jikin Iceland din yayi,ya zauna ya soma cin doyar daga cikin plate din da ta ajiye a gefen yana shan tea din yana kallon ta, sai da ta gama tatas ya goge hannun ta, ta fice daga kitchen din ba tare da ya sake tsaida ta ba, ya kuma cinye mata abincin da ta zuba duk dan tayi masa magana amma sai ta nuna kamar ma bata san me yayi.  A rayuwar sa ya tsani silent treatment duk da shi yafi kaurin suna a wannan bangaren amma ya tsani wani yayi masa sai yaji kamar kansa zai yi bursting, ta gwammace ta zauna bata ci komai ba akan ta yi masa magana kenan. Ransa ne ya dan sosu, a kalla yayi kokari har yake bin ta tana botsarewa bayan be taba hakan ba, zai gwada kyaleta yaga iya gudun ruwan ta.

   Wanka ya shiga ya shirya ya fito yana daura links a jikin hannun rigar sa Mama ta kirashi tace Amira zasu zo da Salma gidan su kwana biyu, wani banbarakwai yaji har ya kasa hakuri yace;


"Kwana Mama?"


"Eh kwana, ko kar suzo?"


" A'ah, amma..."


"Mahaifin ku shi kadai kake ma biyayya Tariq, ba zan ce kayi min ba, ba kuma zan hana ba, shikenan ba komai."


"A ah, i'm sorry, kiyi hakuri,sai sunzo."


"Shikenan, yaushe zaka tafi?"


"Nan da kwana hudu ko in sha Allah."


"Ok sai su zauna har sai ka dawo."


"Toh Mama." 


  Hula ya saka bayan ya gama wayar ya fice daga gidan a tunanin sa hakan sai sa ya manta da ita da tunanin abinda ya addabi zuciyar sa. Kai tsaye gidansu ya nufa dan so yake ya samu Fauwaz yaji yadda akayi ya fada mata maganar da sukayi sannan ya samu Hajiya Yaya. 

Sabani sukayi da Fauwaz din yana fita shi kuma ya na shiga gidan. Wajen aunty ya fara zuwa ya gaishe ta sannan yace yana so ayi Jidda lefe kamar yadda akayi wa kowa, mamaki ya bawa Aunty amma a k'asan zuciyar ta dadi take ji, ya soma siyan wasu kayan online amma wasu dai zai bar Auntyn ta siyo. A haka suka rabu ya nufi wajen Mama, bata nan ta fita sai Aunty Nafi da su Amira dake shirin tafiya gidansa wanda ba asan ran Amira zaa baka dan dai tana shakkar Mama ne sannan kuma ba zata bar Salma taje ita kadai ba dan tasan dalilin zuwan ba na Allah da annabi bane, so take ma ta fadawa Ya Fauwaz yasan yadda zai sanar da Ya Tariq din ko Mama ta kirashi kar ya yarda amma sai ji tayi suna waya da Maman kamar ma kuma har ya amince.

   A tsaitsaye ya gaida Aunty Nafin da wasu mata su biyu ya fice yana jin tana maganar ya tsaya Salma ta kawo masa breakfast amma yayi biris ya ja dan siririn tsaki dan baya son yadda matar take masa sam, ya kuma lura ita ke zuga Mama dan dazu ya jiyo sautin muryar ta,tana cewa Maman kar ta raga masa idan yaki amincewa kawai sharewa yayi amma ya jita, baya son munafukan mata kuma sai yasan yadda yayi yasa ta tarkata inata tayi gaba dan ba zai iya tolerating dinta ba.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links