SANADIN LABARINA 16


  Page (16)

***Da yamma Isma'il yazo daukar su, cike da zumudin ganin jiddah, shi da Farouk suka zo yayi parking a chan gefen gidan sabo da motocin dake wajen sannan ya kira Mom a waya yana fatan su fito tare da jiddah, dan haka ma yazo da Farouk dan ya ganta a zahiri ya daina cewa ya haukace akan yar karamar yarinya. Fitowa sukayi suka tsaya a jikin motar Farouk ya kalle shi ya kwashe da dariya

"Wai duk zumudin ne haka?"

"Ba zaka gane ba, kwana biyu da ban ganta ba, ji nake kamar na shekara ban ga cute face din ta ba."

"Uhum umm, sannu Romeo"

"Ai nafi Romeo sai dai baban Romeo."

"Ah lallai, sannu."

"Yaww, idan ka ga babyn zaka tabbatar na iya kamu, ni zan raini kayata, ta tashi ta tsarin da nake so."

"Gaskiya ne kuma, amma fa ana iya samun matsala irin haka, sai kaga karshe yarinya tace bata so."

"Think positive dan Allah, in sha Allah babu abinda zai faru."

"Allah yasa."

Hango fitowar su Mom ya sakashi yin shiru, yana leken bayansu, ya hango su ita da Safeera a baya hannun su sarke da juna, ajiyar zuciya ya sauke da sauri Farouk ya kalli wajen da yake kalla. Har suka karaso idanun sa na kanta,shi kuma idanun Mom na kanshi tana nakaltar yanayin sa, Farouk ne ya zungure shi wanda saboda yadda yake kallon su yana murmushi har sai da Jiddan ta dan ji kunya, yayi saurin waskewa yana juyawa wajen su Mom

"Mom kun fito ashe."

"Ina zaka san mun fito?" Tace sai ya sosa kansa yana kallon Farouk, ya harare shi kawai ya budewa mom kofar suka shiga ita da kanwar Daddy, Safeera ta zagaya ta shiga suka sakata a  tsakiya, dan russunawa jiddah tayi 

"Mommy ku gaida gida, sis sai gobe a school mungode."

"Nifa jiddaaaa?"

"Hadda kai Ya Isma'il, ina wuni?"

Dadi na ya kamashi,yace

"Fine, bari mu tafi."

 Sannan ya rufe kofar motar Farouk yayi kamar ya daki kafadar sa amma ya kyale, kamar ma Isma'il din ya manta da su waye a cikin motar. Matsawa baya jidda tayi, tana rike da hannun Usman suka juya motar ta daga musu hannu sannn ta juya zuwa cikin gidan.
    
    Shiru ne ya biyo baya, fuskar Isma'il tamkar an masa bushara da aljanna, waka ya kunna a motar ya rage volume din sosai yadda ba zai damu na baya ba, ya rike wa motar wuta yana bin wakar a hankali a hankali. 

"Malam ka tafi damu a hankali kar soyayya ta kwashe ka, ka zubar damu a titi."

"Kyale ni." Yace yana dariya 
  

     Aunty Yagana ce ta kasa hakuri, tace.

"Gata yarinyar me hankali wallahi."

"Wa?" Suka hada baki dukka har Isma'il din

"Jidda."

"Auw, eh kuwa." Mom tace kawai tana murmushi

"Ai jiddah wallahi tayi, ga hankali da nutsuwa wallahi." Safeera ta dora

"Bata da damuwa kwata -kwata."

"Allah dai ya bar wannan kawancen naku har girman ku, har jikokin ku ma, duk da naga yayan naki ya rikice, Allah ya tabbatar mana da alkhairi Isma'il."

"Na'am?"

 Yace yana kokarin juyowa bayan dan be yi tunanin zaayi saurin gano shi ba

"Ka kula fa." Mom tace sannan ta dora

"Farouk kayi ma abokin ka fada, ya rage zafafawa, ita rayuwar nan komai a hankali ake binsa."

"In sha Allah Mom,ina fada masa ai."

"Munafuki." Yace yana hararar sa

"Wai Ya Isma'il ne...?" Sai tayi shiru tana yin murmushi

"Allah yasa hakan ya kasance,."

"Amin idan da alkhairi." 

Shiru yayi be sake cewa komai ba, yasan dole Safeera ta gayawa jiddah, shi kuma be shirya hakan ba yanzu kar tayi rejecting dinsa tun kafin ya koya mata son sa. Dole ya hanata fada mata dan sai ya jira right time, yanzu da sauran su a fara musu maganar soyayya.
   A gida ya ajiye su be shiga ba suka juya shi da Farouk, suna fita suka hau fada shi Farouk a lallai sai ya nuna masa is too early saboda yana jiye masa karyewar zuciya musamman a hangen sa da yanzu Jiddan suka sake yin sama, da kuma yanayin kyawunta zata iya samun yayan manyan kasar suce suna son ta (tunda shi be san jiddah ba yar gidan bace) shi kuma Isma'il yaki yarda da duk wani point da zai kawo sam, ya riga yayi nisan da ba zai gane duk abinda za'a ce masa ba.
   Da daddare da ya dawo gida ya samu Safeera ya kwabe ta yace kar tace ma Jiddan komai, sukayi alkawarin ba zata fada ba, akan haka suka tafi, ya kasance ita ta sani amma jiddah bata taba hasashe ko kawowa ba.
    Tafiyar Baba da Mama ya saka gidan ya zama tamkar part din Yaya ne kawai, anan suke duk dabdalar su tunda yanzu sun rage daga Amira sai Maryam kawai, Safiyya da Umaima sun bi su tunda su dukka sun kammala karatun su ana shirin fara higher institution, rabon zaa yi haka ne admission din Safiyya ya dinga delay karshe dole sai dai su fara tare da Umaima a wata private university din a  Abujan. Da farko Mama cewa tayi ba zata bar yaranta a wajen aunty ba, sai da Baba ya bude mata wuta sosai yace toh sai ta zauna ya tafi da Auntyn dan shi ba zai katse musu karatu ba sannan ta hakura, duk da haka sai da ta kawo yar uwarta ta zauna a part dinta a zuwan ta dinga kula da su Amiran, sai gashi da ita da su Amiran duk sun maida part din Aunty da na Yaya wajen zaman su, idan akaje school aka dawo anan zaa baje har dare, daki daya yanzu Amira da Jidda suke kwana, hakan yakara karfin shakuwar su sosai. 
   

    Rayuwar ta cigaba da garawa cikin ikon Allah, Jidda ta shiga Ss2 Amira ss3,  anan ne Baba yace jiddan tayi waec a Ss2 din saboda yana so su taho gaba daya, jin haka ya saka Safeera tada hankalin ta, a dole itama aka kyaleta tayi a SS2 din dan ba zata iya bari jidda ta tafi, ta barta ba. Haka akayi suka zauna zaman yin waec sannan sukayi neco, bayan an gama ne jiddah ta shirya ta tafi garin su wajen Baffan ta, tayi sati uku sannan ta dawo lokacin ma Amira taje Abuja, sai ya rage sai ita kadai a gidan kamar mayya. Zaman ta da Yaya ne yake debe musu kewa dukkan su, dan idan kana tare da Yaya ba zaka taba yin hawan jini ba.
    Tana zaune tana kallon wata drama a wayar aunty rabin hankalin ya tattara ya koma kan kallon duk hirar da Yaya take mata bata ji ta ba, har tayi fushi ta tashi ta fito waje tana sababi

"Takwara ta koya miki wannan banzan kallon kayi ta magana ayi maka banza, mtsw kuma wai a haka ake so ka koma Habuja. Ni kawai a barni na koma kauyanmu."

"Ya hakuri Yaya, wallahi banji ki bane." Tace tana fitowa ta zauna a gefen Yayan

"Toh naga kema da muke zama muyi hirar mu kin bi hanyar yaran chan."

"Kallon da dadi Yaya."

"Duk dadinsa ya kai gidan badamasi ne?"

"A ah be kai ba." 

"Ah toh, ki daina bari na ina ta magana ni kadai"

"Na daina in sha Allah."

"Yawwa yar albarka, yanzu tunda an gama makaranta sai me?"

"Sai ta gaba, Baba yace cigaba zamuyi."

"Auw kema biya musu zakiyi ke da nake ganin ki me hankali, uban me ake tsinta ne a bokon da za'a ce sai an kure shi, shi kanshi wanchan sahoramin ina nan ina jiran dawowar shi sai na wanke shi tas, in banda shirme karatu ba na Allah da annabi ba, ace kaje kayi zaman ka ko kazo ma a kanka sai wani abu vidiyo, ta nan zaa ganka kana cika kana batsewa."

"Toh Yaya yanzu rayuwar ta zama sai kayi karatun ai."

"Namiji yayi mace ma sai ace dole sai tayi? Dakin mijinku be fi muku bane wai ni?"

"Yaya karatun yafi."

"Tafi chan, aure shine birgewar mace ba ta zauna gande-gande ba a gaban iyayen ta, yanzu ji Safiya da Umaimatu dan Allah, ga Maryama gaki ga takwara, wannan ai shirme ne."

"Zamuyi ai Yaya, daga baya idan mun fara jami'ar"

"Lallai ashe zaa yi fada dani kuwa, ko naji kauye wallahi na samo muku mazaje duk na hada ku dasu naga karyar bokon."

Rufe bakin ta, tayi taba dariya, sannan tace

"Ya hakuri Yaya, zamuyi fa."

"Ko fa mashinshini baku dashi fa, wannan wanne irin abu ne? Ko wannan gattin banzan da aka zuba a waje ne yake bawa mazan tsoron zuwa su kulaku ne ni Hajara?"

Sai ta hau tafa hannu tana salallami,

"Ba zai yiwu ba wallahi, dole a sake sabon zama,ko za'a yi karatun dole kowacce ta kama miji a hannu, ba zan lamunci wannan sakarcin ba."

"Toh Yayah." 

Tace tana cigaba da dariya dan ita bata ga abin ta da hankali ba, bama ta wannan tunanin ita sam wallahi, shiyasa ma bata dauki maganganun Yayan da wani muhimmanci ba.

Kiran ta Usman yazo yayi yace tazo Safeera tazo,ta tashi da sauri dan bata yi tsammanin zuwan ta ba, Yaya na mata magana bata ji ba tayi gaba kawai. Da saurin ta, ta shiga falon tana kiran sunan ta, sai ta tsaya chak ganin mutum a zaune a falon jikin sa sanye da shadda fara kal, yayi kyau sai taga baki daya ya sauya mata kamar bashi ba, fuskar sa ta kalla sai taga kamar ta kara haske akan dah, 

"Ya Isma'il?" Tace tana karasowa dan bata ga Safeeran ba, ta bayan ta tayi tsalle ta dane ta, wanda ta kusa kaita kasa, suka kwashe da dariya gaba daya

"Na zata fa ba dake akazo ba."

Tace bayan ta saketa

"Ni da Ya Isma'il ne, suprise visit mukayi miki tunda aka gama examz shiru."

"Wallahi, duk ba dadi zaman."

"Ina wuni ya Isma'il."

"Lafiya lou, kina lafiya?" Yace yana dan zamowa daga jikin kujerar zuwa gaba

"Ina aunty? Tasan kunzo?"

"Eh ta shiga ciki, magana ce ta kawo mu Jidda ni da yayana."

"Toh... Zauna bari na kawo muku ruwa."

"Kyale shi, ki zauna bari naje na dauko."

Tace tana zamewa ta barsu su biyu. Shafa kansa yayi jidda ta kalle shi sai tayi saurin dauke idanun ta ganin yadda yake kallon ta, ta dade da sanin yana mata irin wannan kallon amma bata taba kawo wani abu ba, amma a yau sai taga kallon nasa yayi mata nauyin da taji duk ta takura.

"Jiddaaa."

 Ya kira sunan ta cikin jan sunan wanda ya sakata dagowa ta dan kalle shi sannan ta yi saurin dauke idonta ta amsa a chan ciki kirjin ta na bugawa kamar wadda tayi tsere, tana tsoron duk abinda zai fito daga bakin sa

"Kiyi hakuri da abinda zan fada miki jiddah, ban zo ba sai da na nemi izinin Aunty, ta bani damar zuwa na fada miki abinda yake Raina.."

"Jidda na jima ina sonki, so me karfin gaske, tun ranar da na dora idona akanki ban kara samun nutsuwa ba, komai nake kece Jiddah, ina sonki fiye da yadda nake son kaina, ke din nake so Jidda, ba wani abu da kike dashi ko kika mallaka ba."

Wani gingirim taji a kanta, taji yayi mata nauyin da taji tamkar an dora mata gaba daya nauyin Nigeria akan ta, wani irin yanayi ta riski kanta wanda bata taba tunani ko hasashe ba, me zata ce masa? Ba zata iya cewa bata son shi ba ko dan Safeera, ko dan kaunar da suke nuna mata, sai dai bata jin ko digon sansa a ranta, bata jin zata so shi, ba kuma dan bashi da qualities din ba, ba kuma dan be hadu ba, bata taba kawo saurayi me jini a jiki da hutu kamar Isma'il zai sota ba ma, ba ajin sa bace ita, yafi ta komai da komai amma ya sauke kansa yake fada mata kalmar soyayya."

"Dan Allah Jidda karki ce min a ah, zuciya ta ba zata iya dauka ba, dan Allah."

Bakin ta ne ya sarke, ta shiga tari babu kakkautawa, duk ya rikice ya shiga kiran Safeera, da sauri ta fito ganin jidda na tari ta koma ta kawo ruwa ta bata tasha sannan tarin ya tsaya. Kallon ta yake yana daga tsaye yaki zama saboda yadda ya rikice,sai da ya tabbatar ta dawo daidai sannan ya zauna yana jan ajiyar zuciya.

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links