Addu'ar Sallar Istihara

 


Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu).


Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ  حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.

Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.


Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka  kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".


Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;

(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)

(Washawirhum Fiyl Amri Fa'iza Azamta Fatawakkal Alallahi).


"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links