Salon Da mata suke bi yanzu wajen neman mijin aure - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Salon Da mata suke bi yanzu wajen neman mijin aure

 


 ZAMANTAKEWAR RAYUWA A SOYAYYA:Mafiya yawan 'yan mata kai harma da zaurawa burinsu shine kawai suyi aure ba tare da la'akari da wanda suke so su auran ba ko zai dace da zama miji na gari. Hakan yasa da sunyi aure sai kawai su fito saboda rashin iya zaben namijin da zasu iya zaman aure na har abada dashi.Ga wasu hanyoyi da dabarun da wasu matan suke amfani dasu wajen gano ko wanda suke soyayya da shi ya dace da su aure shi.Haka suma maza da dama basu fahimtar irin wadannan dabarun da matan ke da su. Hakan yasa da zaran namiji yaje wajen wacce yake so sau daya ko sau biyu daga nan kuma sai yaga ta canza ko ta daina kula shi. Tana iya amfani da wadannan dabarun ne domin gano rashin dacewarka da ita. Don haka maza sai a kula.1: Addini: Mata masu dabara suna kula da yadda wanda suke so da aure yake daukar addinsa da kuma hanyar da yake tafiyar da shi. Da hakan ne zasu iya fahimtar ko ya dace da ya zama mijin nasu ko akasin hakan.2: Mu'amala sa: Mata suna kula da yadda wanda suke so yake mu'amala da mutane na kusa dashi dana nesa dashi kamin su amince da auren sa.3: Rashin Amsa Wayarka: Idan mace na son gwada dacewar namiji a rayuwar ta takan gwada shi ta hanyar kin daukar wayar sa akan lokaci har sai ya kira fiye da sau daya sannan idan ta dauka taji irin yadda zai fiskance cikin fushi ne ko kuma cikin bata uzuri.


Haka nan wasu matan idan ka tura musu text zasu ki baka amsa da wuri domin fahimtar irin mutumin da yake son su da aure.4: Kin Cika Alkawari: Mata suna gwada mazan da zasu aura ne da hanyar musu wani alkawari kuma su ki cika shi da gangar domin nazarin irin martanin da zaka dauka.5: Mace idan tana son gwada ka zata iya yi maka karyar batada lafiya domin ganin yadda zaka dauki rashin lafiyan nata. Matakin da zaka dauka yana da tasiri soyayya a cigaba ko dakatar da soyayyar ta da kai.6: Bijiro Maka Da Bukatu: Akwai wasu matan da hanyar da zasu gwada soyayyar da kake musu shine sun dankara maka wata bukatar da zasu yi tunanin bazaka iya yi ba ko kuma bazaka iya fitowa ka fadamusu gaskiyar gazawarka a cika wannan bukatar ba. Don haka idan ka gudu daga nan shi kenan. Idan kuma ka cika bukatar sai wani jarabwan. Idan kuma ka fito ka fadamata gaskiya nan ma kana da matsayi a wajen ta na daban.


7: Zuwa Maka Da Kawaye: Mata suna gwada maza da zuwa maka da kwayenra ko kannenta a lokacin da kayi sallama gidan su ko kuma ka gayyace ta zuwa wani wajen da kake tsammanin ita kadai zaka ganta.


Zuwa maka da wasu da baka tsammani wurin ka nan ma wata hance da zata iya fahimtar manufar ka a gareta.8: Yin Fushi Da Ganga: Mata suna gwanda masu son su ta hanyar kirkiro fushin haka nan kawai ba abunda aka musu ko kuma abunda aka musu bai kai matakin da suka dauka. Wannan shi ma yana cikin dabarun gwajin irin soyayyar da namiji ke mata.9: Yawan Son Jin Labarin Soyayyar Ka: Idan kaji mace na yawan yi maka zancen akan soyayyar data yi a baya ita ma tana son sanin wanda kayi a baya ne. Wasu kuma kai tsaye zasu tambaye ka labarin soyayyar da ka taba yi ko kuma labarin matarka ta gida. Cikin bayanin da zaka mata anan zata iya fahimtar irin wanda ya zo soyayya da ita.


10: Rashin Baka Muhimmancin: Zata rika kokarin nuna maka ba kada mahimmanci a rayuwar ta duk domin ganin hakurin ka ko rashin sa.

Drop Your Comment

0 Comments