Wasu Ne Suka Fusata Ni, Suna Yi Min Gorin Musulunta - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Wasu Ne Suka Fusata Ni, Suna Yi Min Gorin Musulunta


 

Wasu Ne Suka Fusata Ni, Suna Yi Min Gorin Musulunta, Shi Ya Sa Na Ce Na Bar Musulunci, Amma Har Yanzu Ni Musulma Ce, Cewar Muneerat Abdulsalam

Muneerat wadda ta bayyana hakan a wani sabon bidiyon da ta fitar cikin hawaye kan takaicin gorin musulunta da ake yi mata, ta kara da cewa "saboda soyayyata da Musulunci na yi hannun riga da mahaifina domin shi ba musulmi bane. Sannan kuma tunda na musulunta babu wanda ya ja ni a jiki, sai kyama ta da gori da ake yi min, kuma duk manyan da suke bibiyata babu wanda yake nema na da aure saidai su nemi na zo su yi zina da ni su biya ni".

Drop Your Comment

0 Comments