Musha dariya:ya sambadi sirikarsa - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Musha dariya:ya sambadi sirikarsa

 

Wani mutum ne yatafi kasuwa, yana cikin  kasuwanci sai aka kirashi a waya, akace ga matarshi tana dukan mahaifiyarsa. Sai yayi shiru, daga nan ya kashe wayarsa. Da magariba tayi lokacin dawo gida, sai yaje yasayo bulalar dorina mai baki biyu kuma ya shafeta da man gyada. Kansa tsaye sai yatafi
gidansu matarsa. Da zuwanshi, ya iske baban matarsa a kofar gida, bayan sungama gaisuwa sai yace masa Baba Hajiya tana cikin gida? Uban ya amsa tananan. Sai yashiga ya sameta a daki, yasa
Sakata yacigaba da dukanta da wannan dorinar tanata faman ihuu. Maigida da makwafta suka shigo cikin gidan aguje amma daki a rufe. Bayan yayi mata jina-jina ya bude kofar yafito. Har zai wuce sai uban matar ya tambayeshi ko lafiya? Anan ya amsa masa.... Baba Matata ce ta Zane Mahaifiyata, Shine Nazo
Naramawa akan mahaifiyarta. Bayan yafita sai Uban yayi ajiyar zuciya, yace na godewa Allah ba Ubansa ta zaneba, dani za'ayiwa wannan dan banzan DUKA? A lokacin da ya koma gida sai ya taras da Abokin wasansa zaune a kofar gidasa, yayi masa barka da zuwa ya shige cikin gida. Yana shiga sai yaga matarsa tana kitso a mahaifiyarsa. Nan take ya fito don yayi shawara da bakonsa. Kafin yayi bayani sai bakon yace, don nayi maka wasan April fool sai ka kashe wayarka ko?
Idan kai ne yazakayi?

Drop Your Comment

0 Comments