Muhimmanci motsa jiki ga mata - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Muhimmanci motsa jiki ga mata

 

ZAMANTAKEWAR RAYUWA:Motsa jiki yana da matukar mahimmanci a rayuwar dan adam, sai dai kuma mafiya yawan mutane musamman ma mata basu cikin daukar motsa jiki da wani mahmamcin ba duk kuwa da sune ma yafi dacewa da rayuwrsu.


Ko kin taba zama kika yi tunani a lokacin da kika ziyarci asibiti domin tambayar kanki shi mai yake jawowa mata suka fi maza lalurar zuwa asibiti? Amsar dai ita ce baya ga lalurori irin na mata na halitta, rashin motsa jiki yana daya daga cikin dalilan da suka addabi mata musamman na cikin biranenmu ganin basu damu da mosta jikunansu kuma basu yin wasu aiyukan da zasu jigata don haka ne da zaran karamar cuta ta shigesu sai asibiti.Akasarin matan masu hannu da shuni musamman na Arewacin kasannan su akafi samunsu da rashin motsa jikunansu, duk da yake ana samun wasu daga cikinsu da suke da kayakin motsa jiki a cikin gidajensu ko dakunansu suna yi a kullum ko kuma jifa-jifa. Wasu kuwa suna kokarin fita filayen motsa jiki ne da sassafe ko da yammaci domin warware jikunansu ta hanyar motsa su.Ga matan da suka dan yawata cikin kasan nan, zasu fahimci cewa matan yammaci da kudancin kasan nan sufi lafiya da kuma tsofa da kyau jikinsu saboda yadda suke ware wani lokaci cikin lokatansu suna motsa jiki. Haka kuma da zaki yi nazari sosai zaki ga cewa matan Fulanin daji da suke tafiyar kilomita masu dama da kafafuwansu da kuma yin surfe da daka da hannuwansu sunfi matan da sue zauni cikin gari lafiya da kuma jimawa a duniya. Haka kuma da kin taba zuwa wuraren jihohin Benuwai Adamawa, Nasarawa da jihohin Kebbi kiga ga mata yadda suke noma fasa duwatsu da kuma daukar kayayyaki masu nauyin akansu zaki tambatar da cewa matan ciki biranai basu da wani lokacin na yin wani aikin da zamu kirashi na motsa jiki koda kuwa aiyukan gidan ne garama matan da suke yini aiyukan cikin gida da zasu iya fakwa da shi a matsayin motsa jiki ne shi ma.


Akwai mata da damar gaske da suka yi ki…ďa da har ya soma zame masu matsalar da majansu, irin wadannan matan masu girman jiki data addabaisu suna matukar kokawa wajen rashin samun kulawa ga Mazajen su irin na lokacin kamin su yi girman jikin. Baya ga hakan kuwa, akasarin matan da suke fama da cuwa ce cuwace irinsu hawan jinni cutar shugari da makamantasu hakan yana faruwa ne saboda sakaci da suke yi wajen motsa jikunansu a lokaci zuwa lokaci, wanda yin hakan yana matukar rage kaifin cututuka irin wadannan.Mahimmancin motsa jiki ga mata yana da matukar yawan da ba zasu fadu ko su lissafu ba. Sai dai abun nufi shine duk wata macen da take neman tsufa da lafiyar ta da kuma soyayyar mijin ta, dole ne ta kula da nauyi da kuma girman jikin ta.

Drop Your Comment

0 Comments