Amfanin rake ajikin dan adam tanada matukar amfani sosai - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Amfanin rake ajikin dan adam tanada matukar amfani sosai

 

A wannan yanayin ne za ka ga ana tallan Rake a duk fadin garuruwan Arewa. Mutane kan kira ma su rake su saya don zaki. Amma amfanin Rake ya wuce nan.
Ga wasu daga cikin amfanin Rake nan:
1. Yana karfafa garkuwan Jiki Yana
taimakawa wajen kare cutar sanyi, mura da cutar daji.
2. Yana kara ruwan Jiki da karfi musamman ga masu aikin karfi ko aiki cikin rana.
3. Yana taimaka ma Hanta, Zuciya, Ciki, Ido, Kwakwalwa da Al'aura.
4. Yana taimakon Koda wajen hada fitsari da kyau.
Karanta wannan: Amfanin Dabino
5. Yana gyara Fata saboda sinadarin glycolic acid dake cikinsa.
6. Yana wanke Hakora (amma yana da kyau ka kuskure baki bayan kasha saboda kwayoyin cuta na iya samun zakin a matsayin abinci).
7. Gara ka sha Rake da ka sayi lemun
kwalba don ya fi su amfani.
8. Yana maganin yunwa kuma baya da illa ga masu cutar ciwon suga.
Turawa yan uwa don tunatarwa

Drop Your Comment

0 Comments