Amfanin jigida a kugun mace - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Amfanin jigida a kugun mace

 

Jigida kamar yadda akafi saninsa a hausance wata damarace da mata suke daurawa a kugunsu.
Shi dai jidiga a tun dori anayinsa ne da dutsai na sakiya ga masu hali, su kuma talakawa ana musu tasu jigidan ne da wani roba mai dauke da launuka daban daban domin karawa abun kyau da armashi a idanuwan mai kallo.
Larabawa da indiyawa sune sukafi amfani da jigida tun fil azal kamar yadda bincke ya nuna. Hakan kuwa baya rasa nasaba da yanayin yadda suke rawan al’adarsu inda suka kada da kuma girgiza kugunsu jigida na aman sauti yana hawa yana sauka.
Sai dai a baya kabilu da damar gaske na Africa suna amfani da jigida sosai fiye da yadda larabawa da Indiyawa suke yi ganin yadda su bakaken Afirka suka maida jigida cikin wasu jerin al’adunsu da kuma camfe camfe irin nasu.
Wasu daga camfin da akayiwa Jigida a Afirka shine, yana taimakawa mata masu ciki sauki wajen haihuwa, haka nan kuma macen da take sanya jigida tafi saurin sa’ar aure da wuri. Hakan kuma duk macen dake sanya jigida aljanu ko wasu abubuwa na sammu bazai kamata ba.
Shi dai jigida irin na da ba haka kawai ake sakata ba, domin shahararru kuma jarumai ne a wacan lokacin suke yinta don haka ne take da tasiri da kuma tsada ga masu saye.
Sai dai a baya akwai jigida na ‘yan mata akwai na Matan aure da kuma na tsoffofi, kuma a wannan lokacin babu matsala ko wani gani-gani da ake yiwa macen da aka ganta sanye da jigida saboda abune da aka dauka na al’ada maimakon ado ko kiran maza da wasu ke ganin matan yanzu suke yi da jigida ba.
Yanzu dai sanya jigida ga mata ya bunkasa ya fadada har cikin turai. Mata turawa kamar yadda bincike ya tabbatar kashi 60 cikin 100i suna sawa.
Sai dai a wannan zamanin da muke ciki sanyan jigida ga mata ya zama abun ado ne ba domin dalilai irin na chamfi da muka ambata a baya da mutanen baya suke yi ba, duk da yake ana samun kadan daga cikin mata kauyawa masu saka jigida da manuta na chamfi.
Shima dai kamar irin na da ne, wannan zamanin ana yin jigida ne da wasu duwatsu masu kyalli da kuma robobi masu sheki wadanda nauyinsu bai kai irin na zamanin baya ba.
Babban alfanun da jigida yake yiwa mata kamar yadda bincike ya tabbatar a wannan lokacin shine, yana karwa mace fadin kugunta ga irin matan nan da suke da karancisa.
Maza da dama da aka zanta dasu sun nuna sha’awarsu na ganin matansu na aure suna saka jigida domin yana karamusu kyau musamman idan mace tana sanye da kayan da zasu bayyanasu.
Har ilayau cikin alfanun da jigida ke dashi shine yakan motsa sha’awan maza a yayin da suka ji sautinsa ko suka hango shatinsa.
Kara ko sautin dake fitowa daga jigida a lokacin wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin gudanar da jima’i abune dake himmanta maza yake kuma kara musu kuzari da azama.
Sai dai duk da wadannan tasiri, mahimanci da alfanun da jigida ke dasu da duka mata bane suke sanyawa ba, haka ma maza da dama basu son ganin mace da jigida. Wasu mutane sun riga sun kudura cewa duk mace ko budurwar da aka ga tana sa jigida ko akaji sautinsa a tare da ita suna daukan irin wadannan matan mazinata ne.
Shi dai shan koko daukan rai . Abincin wani, gubar wani.

Drop Your Comment

0 Comments