Yau Sergio Ramos ya cika shekaru 15 a real madrid - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Yau Sergio Ramos ya cika shekaru 15 a real madrid

Acikin waɗannan shekaru Ramos yayi da ba za'a taɓa mantawa dasu ba, ga guda 13 daga cikin su : 1. Ƙwallonsa ta farko a Real madrid. Ramos yanuna matukar kwarewa a zuwansa madrid dukda karancin shekarunsa ramos yafara ciwa madrid kwallonsa ta farkone a gasar champions league yayinda madrid tadoke Olypiakos a group Stage. 2. Jan katinsa na farko a wasan Real Madrid da Espanyol 2005. A daidai lokacin da Real madrid take matuƙar neman nasara domin ta lashe gasar Laliga Ramos yayi sanadin samu red card na farko a madrid a ranar 18 sep 2005 yayinda madrid tayi rashin nasara a hannun espanyol daci 1-0. 3. Jefa kwallo a ragar Valencia a 2008. A ranar 24 aug 2008 ramos ya jefa kwallo a ragar valenci a spanish super cup hakan, yabaiwa madrid damar lashe kofin, a karshen season dai saboda kwazon da ramos yayi yasamu nasarar shiga FIFA dakuma UEFA team of the year sannan kuma yazo dan wasa na 11 dayafi kowa kokari a shekarar. 4. Ramos Acrobotic goal 2009. A ranar 11 jan 2009 ramos yaci kungiyar mallorca ACROBATIC goal irin kwallon da ronaldo yajefa a ragar juventus. 5. Jefa Real madrid a tsaka mai wuya a 2013. Ramos ya jefa Real madrid a tsaka mai wuya a ranar 9 ga watan jan 2013 ramos yakara kar6ar katin kora wato red card yayin karawa da celta vigo kuma andakarda dan wasan wasanni 4 saboda zaginda yayiwa alkalin wasa miguel angel ayza gamez. 6. Ɗan wasa na farko daya fara samun jan kati 18 a Real madrid. A ranar 14 dec 2013 ramos yazama dan wasa na farko a madrid daya samu red card 18 yayin karawa da osasuna sannan ya amshi red card na 19 a ranar a wasan da madrid tayi rashin nasara a hannun barcelona daci 4-3 7. Kakar wasanni ta 2013/2014. Shekarar 2014 tashiga kundin tarihin ramos dakuma madrid baki daya domin kuwa a shekarar ne madrid tasamu nasarar lashe gasar champion karona 10 kuma kwallon da ramos yajefa a ragar at. Madrid ana gabda tashi wasan ita tasauya akalar wasan har madrid tasamu nasarar lashe kofin, a shekarar dai ramos yasamu nasarar jefa kwallo a semi-final dakuma final din fifa club world cup wanda aka buga a morocco kuma madrid talshe kofin sannan an bayyana sunan ramos a matsayin dan wasan dayafi kowa kokari agasar. 8. Kakar wasanni ta 2015-16 Ramos yasamu red card na 20 a yayin da madrid kecin las palmas 2-1 a shekarar 2015-16, dan wasan yadawo daga dakatarwa a wasan el-clasico a ranar 2 apr 2016 wasanda madrid kecin barcelona 2-1 sannan ramos yakuma samun red card a wasan wanda yazama jan kati na 21 kuma na 4 a wasan El-clasico. 9. Ƙwallon da Ramos ya jefa against Atletico Madrid. Ƙwallon da Ramos yakara jefawa a ragar at madrid a final din champion na 2016 wanda ya bawa Real madrid damar lashe kofin, kuma yasamu nasarar zama (man of the match). 10. Ramos ya kuɓutar da Real madrid daga hannun Barcelona a 2016. A ranar 3 Dec 2016 ramos ya kuɓutar da Real madrid daga hannun Barcelona inda ya farke ƙwallon da barcelona sukaci Real madrid a el-clasico a mintin karshe wasanda ake tashi 1-1. Itace ƙwallo ta huɗu daya jefa a Elcasico. 11. Ramos own goal 2017. A ranar 15 jan 2017 ramos yayi own goal a wasanda madrid tasha kashi a gidan sevilla hakan takawo karshen wasa 40 da madrid tayi ba'a doke taba. 12. Cika Wasanni 500 da Ramos ya buga a Real madrid. . A ranar 11 feb 2017 ramos yabuga wasa 500 cif a madrid sannan a ranar 20 aug 2017 dan wasan yakuma ansar red card na 23 kuma na 18 a gasar laliga 13. Ramos yazama dan wasa na biyu a tarihin laliga bayan leo messi na barcelona daya jefa kwallo adukkan season 14 daya buga a gasar laliga.

Drop Your Comment

0 Comments