Yan sintiri sunyi nasaran kama barayin dare - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Yan sintiri sunyi nasaran kama barayin dare

Abinda ya kamata mutanen kowace unguwa su fara yi kenan a kowane gari... Matasa 'yan sintiri a Unguwar Shamaki dake cikin garin Gombe, sun samu nasaran kama wasu barayi biyu bayan gurmuzu da aka yi da barayin, 'barayin sun saba bin gidajen mutane da daddare suna sata da kwace kaya, ko ka basu ko maka illa da wuka, ko karfe. Jiya an kama su, kuma sun sha duka da dauri, sannan sun sha watsin ruwan sanyi kafin gari a waye aka mika su hannun 'yan sanda. . Jama'a abinda ya kamata kuyi kenan a unguwannin ku, ku saka matasa masu karfi masu kishi, su rika muku gadin unguwannin ku, idan su kama barayi su daka su, duka sosai, sannan a sako hotunan su a Facebook, a fallasa su sosai. Duniya ta gansu, wallahi hakan zai rage ta'addancin da ake yi a cikin garuruwan mu da unguwanni. Kar ku tsaya wai sai 'yan sanda sunzo kafin ku samu tsaro ma kan ku, ku fara kare Kan ku (Self Defence) wannan ko a constitution ya halatta.

Drop Your Comment

0 Comments