tattalin arziki: dama can an dora najeriya a turbar shan wuya sunusi ll - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

tattalin arziki: dama can an dora najeriya a turbar shan wuya sunusi ll

Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya dora laifin matasalolin tattalin arzikin Najeriya a kan dogaro da man fetur lamarin da ya sa gwamnatocin baya su ka sakankance, ga shi yanzu hakan ya taba tattalin arzikin kasa. "Da ma can an dora Najeriya a turbar da za ta sha wuya, saboda fiye da kaso 90 na kudin shiga da gwamnati ke samu ya na fitowa ne daga cinikin man fetur, shi kuma farashinsa hawa yake yana sauka. "Mu danyen man fetur muke samarwa, amma kuma alhakinmu ne mu saka farashin man fetur da aka shigo da shi bayan an tace, ta yaya za ka tsayar da farashin kayan da ba kai kake sayowa ba?, danyen mai muke samarwa ba tataccen man fetur ba. "Mu ne kadai kasar keda arzikin man fetur amma ba ma cin moriyar hauhawar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya saboda ba ma tace danyen mai a cikin gida, sai an siyo daga kasar waje," a cewar Sanusi. Sanusi II Source: UGC Read more: Ba zai yiwu a iya farfado da arajar Naira ba sai mun rage dogaro da kuma mayatar son amfani da kayayyakin da ake shigowa dasu daga waje. "Domin tabbatar da hakan akwai bukatar samun hadin kai a tsakanin kasashen nahiyar Afrika a kan daina siyo duk wasu kayayyaki daga ketare matukar za a iya samarwa ko sarrafasu a gida. "Dole a samu wannan amincewa a tsakanin kasashen nahiyar Afrika ta yamma, saboda koda CBN ya hana a shigo da wasu da kayayyaki sai ma'aikatar kasuwanci ta yi nata aikin, musamman aiki tare da sauran makwabtan kasashe. "Hatta kayan da za mu iya samarwa a gida shigo dasu ake yi. Ba ina nufin cewa mu fara kera motoci, jiragen sama yanzu ba, abubuwan da zamu iya samarwa ya kamata mu mayar da hankali wajen samar dasu da sarrafasu. "Hakan zai taimaka wajen samar da aiyuka, gina tattalin arzikin kasa, da daga darajar takardar Naira," a cewarsa. Read more: 

Drop Your Comment

0 Comments