Tarihin Riga mai Lamba 4 - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Tarihin Riga mai Lamba 4

Jerin ƴan wasan da suka goya riga mai lamba 4 waɗanda sukafi shahara sune: -Claude Makelele -Patrick Vieira -Sergio Ramos -Pep Guardiola -Frank De Boer -Frank Rijkaard. Sergio Ramos shine ɗan wasan da yafi kowanne shahara da taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa a jerin ƴan wasa da suke sanya riga mai lamba 4. Sergio Ramos ɗan wasan bayane a Real madrid. SHIN WACCE RAWA SERGIO RAMOS YA TAKA A ƘWALLON ƘAFA? Sergio Ramos shine kyaftin a Real madrid da ƙasar spain. Sergio Ramos yazo Real madrid daga sevilla a shekarar 2005, akan kudi €27m a matsayin ɗan wasan baya mafi tsada a ƙasar spain. Kuma shine ɗan wasa na farko da Florentino Pérez ya siya a matsayinsa na shugaban Real madrid. Yanzu haka Sergio Ramos ya shekara 15 a real madrid, ya jefa kwallaye 97 a Real madrid sannan guda 3 a sevilla, hakan ne yasa ya zama ɗan wasan baya na farko daya jefa kwallaye 100 a ƙungiyoyi a Tarihin laliga, sannan shine ɗan wasan baya na 2 da yafi kowanne jefa kwallaye a gasar Laliga , sannan ya lashe kofuna guda 22, wannan ne ya basa damar zama ɗan wasan baya da yafi kowanne ƙwazo a Real madrid, kuma ya shiga jerin ƴan wasa goma da babu kamar su a Real madrid da ƙasar spain, sannan an tabbatar da cewa yana daga cikin yan wasan baya da babu kamar su a duniya. Sergio Ramos ya shiga jerin ƴan wasa 11 na Fifa sau 10, hakan ne yasa ya zama ɗan wasan baya da yafi kowanne shiga wannan sahu, kuma shine yazo na uku a duniya inda yake biye da Messi da Ronaldo, sannan ya shiga jerin ƴan wasa 11 na nahiyar Turai sau 8, sannan ya lashe kyautar Gwarzon dan wasan baya na laliga sau 5. Yanzu haka shine ɗan wasan da yafi bugama ƙasar spain wasa. Sergio Ramos yana daga cikin yan wasan ƙwallon da sukafi Tarihi mai kyau a kwallon kafa da suka lashe kofuna mafi girma a duniya, ya lashe kofuna guda 22 da suka haɗa da Champions League guda 4, world cup guda 1, laliga guda 5. Ramos ya kusa ninka pele bugama ƙasa wasa inda ya bugama spain wasanni 172, hakan ne ya basa damar shiga jerin ƴan wasan da sukafi bugama ƙasarsu wasa a duniya. Har ila yau idan har Ramos ya buga gasar cin kofin duniya ta 2022 ya zarta pele zuwa gasar wanda a yanzu haka sun halarci gasar sau 4. Yanzu haka Sergio Ramos shine yazo na uku cikin jerin ƴan wasan da sukafi ɗaukar albashi a Real madrid bayan Hazard da Bale inda yake ɗaukar €200k a kowanne mako, a shekara kuma yana ɗaukar €10m. Yanzu haka Sergio Ramos shine ɗan wasan baya da yafi kowanne lashe lambar yabo inda ya lashe guda 52 a duniya.

Drop Your Comment

0 Comments