Nayi azumi shida don kawo karshen mulkin APC a najeriya- Musa sulaiman - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Nayi azumi shida don kawo karshen mulkin APC a najeriya- Musa sulaiman

Matashi Musa Suleiman Sarki da ya yi alwashin yin azumi guda bakwai da nufin Allah ya kawo karshen mulkin jam'iyyar APC a Nijeriya, ya fara azumin tun a ranar da ya yi alwashin, wanda a yau ya kai azumi na shida, cikin azumi bakwai da ya sha alwashi sauran guda daya wanda zai karasa a gobe Alhamis. Matashi Musa, wanda haifaffen dan Jihar Gombe ne, dake zaune a anguwan Bolari, ya yi alwashin yin azumin ne kan yadda gwamnatin Nigeria ke gallazawa talakawan kasar wajan tsadar kayan abinci, man fetur, wutar Lantarki, tare da kasa cika musu alkawuran da gwamnatin kasar ta dauka a lokutan yakin neman zabe. Idan baku manta ba, kwanan nan gwamnatin Nigeria ta kara kudin man fetur da wutar Lantarki duk da halin da al'ummar kasar ke ciki na tsadar kayan abincin da al'umma ke fama dashi, wanda hakan yasa al'umma da yawa suke cigaba da fadin munanan kalamai tare da kokawa ga gwamnatin kasar. Al'ummomi daga kowanne sassa a Nijeriya sun tuntubi matashin tare da kara masa karfin guiwa kan azumin da yake yi don ganin an kawo karshen mulkin jam'iyyar APC a Nigeria, wasu hadda bashi gudummuwa a lokutan da yake bude baki don su karfafa masa guiwa. 8 hrs · Facebook L

Drop Your Comment

0 Comments