munyi asarar fiye da rabin kudin shigarmu saboda corona-Buhari - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

munyi asarar fiye da rabin kudin shigarmu saboda corona-Buhari

Mun Yi Asarar Fiye Da Rabin Kudin Shigarmu Saboda Zuwan Cutar Corona Virus, Cewar Shugaba Buhari Daga Muhammad Kwairi Waziri Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta yi rashin kusan kaso 60 cikin 100 na kudin shigarta dalilin zuwan cutar Corona virus. Dan haka ne ma dole ta dauki matakai masu tsauri, lura da cewa za ta rika biyan albashi da sauran kashe kudi da ya zama na dole. Hakan ya fito ne daga bakin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a yayin taron bada rahotannin ayyukan ministocin gwamnati na farko. Mataimakin shugaban kasar ya karyata ikirarin da ake na cewa gwamnatinsu ba ta tausayin ‘yan Nijeriya, inda ya ce sun samar da tsare-tsare na tallafawa ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

Drop Your Comment

0 Comments