mu tashi mu nemi na kanmu - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

mu tashi mu nemi na kanmu

Buri da Yan arewa musulmi suka hadu akai shine ya rabauta da kyakkyawan rayuwa anan duniya da gobe kiyama, anan duniya rayuwarsa ta kasance ya sami abin da zai ci a kullum, ya saka sutura mai kyau, ya shiga mota mai tsada, ya sami karatu kuma ya sami aikin yi, sannan ya yi aure. Wannan akan kankin kansa Kenan Amma abinda ya shafi yankin arewa gaskiya malam bahaushe baida wani buri ko mafarki akan arewa Amma kowa ka taba zaka samu cewa addu'arsa kullum itace " Rabbana aatina fid-duniya hassanatan wa fil-akirati hassanatan wa ƙina azabannar" Amma idan ka cire haka Mafi yawan mutanen Arewa basu da wani buri ko mafarki irin wanda ake kira (American Dreams) saboda da yawa bama su san kan su ba. Tun daga makarantar firamare dayawa daga cikin ɗalibai basu san me suke son zama ba anan gaba, idan an tambaye su sai su ce "ai duk abinda Allah ya ƙaddara kawai shine burin su", mutum ya tashi da safe bai san ina zai je ba, bai san me yakamata yayi ba a wannan ranar kawai shi burin sa " Allah ne ke azurtawa" wanda hakan rashin fahimtar tauhidi ne. Ƙalilan daga cikin mutanen Arewa suna da himma da kokarin ganin sun kawo gyara a Arewa amma basu da Yawa. Komai kagani yana da sila, zama bai kamace mu ba domin ba shine matakin da annabawa da Sahabbai sukabi ba, zama hakanan babu alkhairi acikinsa. Allah ubangiji kasa mu dace ameen 07/08/2020

Drop Your Comment

0 Comments