Me yake kawo yawan yin fyade ga 'kana nan Yara. - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Me yake kawo yawan yin fyade ga 'kana nan Yara.

  Me ya ke kawo Samun yawan yin fyade ga 'kana nan yara?


    Assalamu Alaikum Warahamatullah. 
Ma abota Wannan shafi barkan Ku da war haka da fatan duk kuna cikin 'koshin lafiya. Allah ya 'kara mana Lafiya da kuma kare mana Imanin mu.
   
    Gaskiya kullum Abubuwa sai 'kara ta'azzara ya ke yi, Fyade kullum 'kara yawa ta ke yi a tsakanin Al'umma abun ma har ya kai an fara Aikata Wannan babban sa'bo a Masallaci wa'iya zubillahi. 

  A kwanan ne ne fa aka kama wani Mutum 'kato dashi ya na aika ta Fyade ga wata Yarinya 'yar shekara hudu da haifuwa.  Bari mutafi kai tsaye zuwa ga darasin mu "Me ya ke kawo yawan samun yin Fyade a cikin Al'umma".

   Ta wani 'bangaren Zamu iya kiran sa da Rashin tsoron Allah, Mutane suna Manta wa da ce wa zasu mutu kuma za a tambaye su akan abubuwan da suke aika tawa.
   Ko Muce suna da Rashin tausayi , Yanzu Dan Allah yarinya 'yar shekara 4 kayi zina da ita mai mutum zai samu? ai sai de kawai ya halaka yarinya ya kuma chutar da iya yen ta.


   A cikin irin sune da ake kamawa wasun su ke bada labari cewa Ashe wai sasu ake saboda samun abun duniya, kuma fa abun Duniyar 'karewa zai yi.
    Wasun su Manyan 'yan siyasa ne ke sasu saboda suma bokayen su sun sa su saboda su samu mulki. Wa sun su kuma bokayen ke sasu kai tsaye saboda gudun talauci.
     Allah ya kiya ye, Wasu kuma son Zuciyar su ne kawai ke sasu,wani kuma mugunta da Sharrin Zuciya.
    Wasu kuma zuciyar su kawai ke raya musu su lalata yarinyar nan kawai sai su afaka mata.

  Shawarar mu ga iyaye da yayu da sauran Al'umma shine Ku kiya ye 'ya'yan Ku mata kai harma da mazan saboda yanzu zamani ya gama lalace wa kana chan kana tarbiya wani kuma ya na nan ya na batawa, Allah ya kiya she mu. Amin summa Amin.

Drop Your Comment

0 Comments