Malaman Tsubbu | Amfanin Su | Bambanchin Malaman Tsubbu da Malaman Gaskiya | Amfanin Zuwa gun su. - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Malaman Tsubbu | Amfanin Su | Bambanchin Malaman Tsubbu da Malaman Gaskiya | Amfanin Zuwa gun su.

 Malaman Tsubbu | Amfanin Su |   Bambanchin Malaman Tsubbu da Malaman Gaskiya | Amfanin Zuwa gun su.


    Ma'abotan mu barkan Ku da wannan lokachi barkan mu da arzikin sake saduwa da Ku a wannan gida mai Albarka.

     Yau ma dai kamar kullum, Sanin Ku ne ko wani lokachi muna iya 'ko'karin mu wajen ganin Mun kawo muku sahihin labari da kuma ingantattun rubutai domin ganin Mun fad'akar da Ku tare da nishadantar da Ku.

    yau ma dai na shiga na fita na sambado mana Rubutu Akan Malaman Tsubbu da Amfanin su da kuma Bambanchin Malaman Tsubbu da Malaman Gaskiya. Ku chi gaba da kasancewa tare da ni ako wani lokachi.

    Malaman Tsubbu: 
            Wasu Malamai  ne da suke fakewa da addini San nan suke aika ta abun da su ka ga dama a Rayuwar su, kama da ga kashe Mutum da tsafi ko kwacewa ko talauta mutum da sihiri. yawan chin su kuma malame ne na Musulunchi wadda suke koyar da 'Daliban su a zaure,to da ga nan ne fa wasun su wadda ba sa tsoron Allah sai su fara bokanchi a boye da bugun 'kasa.


    Amfanin Tsubbu:
         Samun biyan bukatan masu zuwa gurin su da bukatun su kuma suna sihiri suna samun biyan bukatan su. Musamman ga 'yan siyasa da bokaye.

     Hukunchin sa a Musulunchi:
            Kasancewar sihiri da tsafi ya ke yi ma mutane to haramunne, wani lokachi kuma istikara suke yi ma'ana Neman Sanin gaibu (ganin mai zai faru gobe), kuma duk munsan wannan haramunne a Musulunche.
       
   Bambanchin Malaman Tsubbu da na Gaskiya :
    Malaman Tsubbu suna sihiri ne su kuma Malaman Gaskiya koyar da 'Daliban su, suke yi karatun addini.
     Amma matsalar da ake samu Wasu malaman zauren (Gaskiya) su ke 'bata wasu. 
  Masu gaskiyar ma suna kaucewa wani lokachin, Allah ya shirya mana ya gyara mana zuri'ar mu.
    Zamani ya lalace yanzu, manya yara da mata da maza duk sun 'bachi da zuwa gun malaman Tsubbu, Ina fatan Allah ya shirya mu.

Drop Your Comment

0 Comments