Mai kudin Duniya yayi rashi - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Mai kudin Duniya yayi rashiMahaifin Bill Gates, ɗaya daga cikin attajiran duniya wanda ya samar da kamfanin Microsoft ya mutu.
William Henry Gates II ya mutu a ranar Litinin ya na da shekara 94.
Cutar Alzheimer da ke shafar ƙwaƙalwa ce ta yi sanadi mutuwarsa, kamar yadda iyalansa suka tabbatar a wani labarin da jaridar New York ta wallafa.
Gates Babba tsohon soja ne kuma ya kafa kamfani da ke harkokin shari'a, kamar yadda tarihinsa ya nuna.
Bill Gates mai shekara 64, ya ce sun yi babban rashi kuma zai dauke su tsowon lokaci su na jimamin mutuwar mutumin da ya yi tasiri a rayuwar mutane da dama.

Drop Your Comment

0 Comments