Labarina_ Shirin (Arewa24) - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Labarina_ Shirin (Arewa24)

Gaskiya duk abunda aka tsarashi bisa ilimi da gogewa daban yake. Da yake Shirin ya sami tagomashin babban darakta kuma masani a kan harkar fina finan Hausa wato Mal. Aminu Saira, ba karamin kayatar da masu kallo yake ba matuka, ba abin da zan ce sai Allah ya kara basira. Sai kuma duba a kan danbarwa soyayya wacce take faruwa tsakanin Mahmood da Sumayya, yana da kyau a matakin farko shi Mahmood din ya fara shawo kan mahaifiyarsa ta yadda ya auri wata sabanin ajiyar da yake da ita a gidansu amma kawai ya zo sai bata mata lokaci yake domin bai gama da gaggarumin aikin da ke gabansa ba na samun yaddar ummansa. Duk abubuwan da kawarta take masa ina goyon baya bisa rashin tabbas da ita Ruqayyan ta hango ta fuskar rashin tabbas da yake da shi a gida na auren ita Sumayyan da kuma rashin nuna jurawa a cikin soyayyar tasu, juriya wani babban rukuni ne a soyayya domin itan bata taba yiwuwa ba tare da samun kalubale ba. A takaice Mahmud da sumayya dole su rabu. Saidai ita sumayya itace abun tausayi don zatafi shan wahala. Ta wata fuskar Mahaifiyar Mahmud dole ta tursasa shi kan auran wacce take so don itama zafi gareta kuma tadace da Mahmud kwarai. Zafin kishin shi zai kaishi yabaro tunda ga kawar sumayya tafara akansa. A ƙarshe ina jinjina ga Malam Aminu saira da sauran maikatan tashar arewa 24 musamman oga na Nura Ahmad Allah ya ƙara ɗaukaka ameen

Drop Your Comment

0 Comments