kamfanin sarrafa shinkafa tiamin ya kafa reshensa a jihar bauchi - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

kamfanin sarrafa shinkafa tiamin ya kafa reshensa a jihar bauchi

Wannan dama ce ga matasan Arewacin Nigeria, musamman ma 'yan jihar Bauchi. Babban kamfanin sarrafa shinkafa da samar da ita dake Nigeria wato TIAMIN RICE, kamfanin ya kammala gina babban cibiyar sa a jihar Bauchi, a garin Yuli, dake 'karamar hukumar Ganjuwa, (kusa da cikin garin Bauchi), bayan babban cibiyar sa dake Kano. Kamfanin ya sanar da zai fara 'daukan ma'aikata a gurabe har guda Arba'in (40), ga wanda yake bukatan samun aiki da kamfanin TIAMIN RICE ga hanyar da zaka bi: : 1. Ka shiga email din ka, ka aika da CV 'din ka, wato "Curriculum Vitae" zuwa ga adireshin kamfanin na email, wato: ( tiaminricebauchiemployment@gma il.com ) Amma zaka rubuta "JOB TITTLE" a matsayin subject of the email din da zaka tura. . 2. Ana bukatar masu Diploma, NCE, Degree da Sauran karbabbun takardun gwamnatin tarayya dana jiha, wadanda suka wuce Sakandare. 3. Za'a rufe ranar Talata 17- September- 2020, idan Allah ya kaimu. . Kamfanin ya samu hadin gwuiwa da gwamnatin tarayya da CBN da kuma Jaiz Bank da sauran su, yana da rijista da CAC, ya samu tallafi mai girma daga gwamnatin shugaba Buhari da goyon baya dan samar da kamfanin shinkafa, da Shinkafar kanta. Yanzu haka yana da branch a jihohi uku ne kadai a Nigeria, Bauchi, Kano da Lagos. . Kamfanin zai dauki ma'aikata tun daga: 1. Direbobi. 2. Masu sha'anin kudi da lissafi. 3. Masu walda. 4. Sarrafa injuna. 5. Sarrafa hatsi. 6. Masana ilimin Shari'a. 7. Masu ilimin hada hadar kasuwanci. 8. Masu daukan kaya. 9. Masu ilimin sinadarai (Chemicals). Da sauran su..... Allah ya bada sa'a.....

Drop Your Comment

0 Comments