kada Ku kuskura Ku bawa dan arewa takaran shugaban kasa _ohanaeze ta fadawa PDP - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

kada Ku kuskura Ku bawa dan arewa takaran shugaban kasa _ohanaeze ta fadawa PDP

"Idan kuka kuskura kuka bayar da takaran shugaban kasa ma 'dan Arewa a jam'iyyar PDP, toh kada kuyi tsammanin Inyamurai zasu zabi jam'iyyar ku, tun 1999 shiyyar mu ta Inyamurai muke yin PDP amma ko Vice President ba'a taba bamu ba, PDP ta mayar damu Saniyar da ake tatsan Nonon ta har sai ta mutu, menene PDP ta mayar damu? a wannan karon ko a bamu takaran shugaban kasa ko mu kauracewa jam'iyyar har abada" - inji 'Kungiyar Matasan Inyamurai, wato Ohanaeze Youth Council. . "Sun kara da cewa, duk wani 'dan "kabilar Igbo da ya kuskura ya karbi Vice President a PDP toh kada yayi gan-gancin sake shiga yankin kasar Inyamurai, babu abinda muke bukata sai takaran shugaban kasa a PDP". Har wa yau sun yi korafi cewa, sun fara jin kishin-kishin din PDP zata tsayar da dan takara daga Arewa ta Yamma (Noth West) yankin da shugaba Buhari ya fito, toh gargadi na karshe kenan ga jam'iyyar PDP". - inji Ohanaeze Youth Council

Drop Your Comment

0 Comments