Gwamna-zulum yakai ziyarar bazata babban asibitin maiduguri - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Gwamna-zulum yakai ziyarar bazata babban asibitin maiduguri

Jiya da daddare da tsakiyar dare yayin da gwamna Zulum ya kai Ziyarar bazata ma babban Asibitin Maiduguri. Yace a kawo masa duty roster, ya duba sunan Likitocin da suka zo da wadanda basu zo ba, wadanda dama ya dace ace suna bakin aiki da daddaren, ya duba na Doctors, Nurses da masu karban haihuwa da sauran su. Wasu Likitocin kuma sun tafi wani 'daki suna bacci, yaje ya taso su, ya hau su da masifa, yana cewa idan aka kawo mara lafiya yanzu cikin gaggawa sai dai a jira ku gama baccin kenan ko yaya? . Yace "menene amfanin biyan ku kudaden a karshen wata? haka ake aiki da lalaci da son jiki da kasala?" Daga bisani ya dauki sunan wadanda suke bakin aiki a daren, ya kuma dauki na wadanda basu zo aiki ba, yace za'a yi maganin su. Ance wadanda basu so aiki a daren ba anyi ta kiran su a waya, cewa gwamna yazo wurin aikin su basa nan, ance galibin su basu yi bacci ba a daren. Wasu kuma a duhu suka taso suka je Asibitin, bayan gwamnan ya dauki bayanan ya tafi.

Drop Your Comment

0 Comments