Dalilin mutuwar Aure na | In ji momi Gombe. - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Dalilin mutuwar Aure na | In ji momi Gombe.

   Dalilin mutuwar Aure na | In ji momi Gombe.


    Barakan mu da Wannan lokachi mai sauraro da fatan kana lafiya.


   Momi gombe ta bayyana wa BBC da sauran gidan jaridu dalilin da ya sa auren ta ya mutu.   A yadda jarumar ta bayyana ta ce ita de da mijin ta suna zaman lafiya babu abun da ya hadasu, ta na masa biyayya tsakanin ta da mijin ta yi na yi, bari na bari.

    Randa auren su ya chika kwana talatin da tara (39) sai mijin momi gombe ya fara mata wasu abubuwa gwale gwale wadda ita bata gane kan su ba amma sai ta yi haquri.

    To washe gari da safe Ranar da suka cika kwana arba'in da aure sai mijin momi gombe ya ce mata ta shirya ya kai ta ganin gida, ta ce masa to a yadda ta bamu labari.

    cikin girmamawa ta shirya suka tafi kawai ya na kai ta sai ya bata takardar ta na saki da rubutun ya sake ta saki uku.

    Ta shiga gida ta basu bayanin abun da ya faru sai iyayenta suka ne mai shi a waya amma baya dauka da ga baya ma ya sa su a blacklist in sun 'kira bata shiga to nan ne fa da tagama idda sai ta shigo masana'artan kannywood da ga bisani har suka fara waka da hamisu breaker.

Drop Your Comment

0 Comments