Dalilin da yasa muka Janye Yajin Aiki - NLC - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Dalilin da yasa muka Janye Yajin Aiki - NLC


Kungiyar kwadagon Najeriya da takawararta ta ‘yan kasuwa, sun janye yunkurin tafiya gagarumin yajin aiki a yau Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020. NLC ta TUC sun dakatar da maganar yajin aikin ne bayan sun yi yarjejeniya da gwamnatin tarayya a wani zama da su ka fara cikin daren ranar Lahadi.


Rahotanni sun ce an fara wannan taro ne tun da kimanin karfe 8:30 na daren jiya, an kuma kai ga cin ma yarjejeniya da karfe 2:50 na safiyar yau dinnan. Bayan tsawon lokaci ana tattaunawa kan batutuwan da kungiyoyin kwadagon su ka kawo, gwamnatin tarayya ta dakatar da karin kudin wuta na mako biyu.

Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige ya karanto takardar matsayar da aka cinma tsakanin wakilan ma’aikata da kuma gwamatin tarayya. Shugabannin TUC da kungiyar NLC; Quadri Olaleye da Ayuba Wabba su na cikin wadanda su ka sa hannu a madadin kungiyoyin ma’aikatan Najeriya. A bangaren gwamnati kuwa, wadanda su ka sa hannu sun hada da Ministocin kwadago, da yada labarai, Chris Ngige, Festus Keyamo da Lai Mohammed. Haka zalika karamin Ministan harkokin man fetur, Timipre Silva, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun rattaba hannu a wannan yarjejeniya.


Festus Keyamo ya tabbatar da cewa babu batun janye tsarin kudin man fetur, amma an dakatar da karin kudin wutar lantarki har sai nan da makonni biyu. A dalilin zaman na dazu, an kafa kwamitoci daga ma’aikatun gwamnati da kuma bangarorin ‘yan kwadago domin a cika wadannan alkawaru da aka dauka. A jiya kun ji cewa Gwamnatin tarayya za ta gana da kwadago da karfe 7:00 na yamma saboda yunÆ™urin shiga yajin aiki da ma'aikata ke yi a fadin Najeriya. 

Drop Your Comment

0 Comments