Anfitar Da Sabon Sarkin Zazzau - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Anfitar Da Sabon Sarkin Zazzau

An bukaci duk wandanda suka cancanci gadar Sarautar da su bayyana raayinsu bayan Adduar kwana Uku da rasuwar Marigayi mai martaban. Zuwa yanzu akwai mutane bakwai dasuka bayyana burikansu na gadar sarautar. A jerin mutum na farko shine yariman Bare-bari, da kuma Magajin Garin daga Kabilar Mallamawa. Sauran Biyar din sun fito ne daga Kabilar Katsinawa: wato Iya, Turaki, Uban Gari, Dan Galadima, da kuma Sarkin Kudu.


Masu Nadin sarautar su Biyar ne kuma zasu karasa zaben nasu kuma su mikawa Gwamna Sakamakon Kamin safiyar ranar Juma’a. Masu Nadin sarautar sune Waziri, Makama, Fagaci, Limamin Gari, da kuma Limamin Kona. Sun Jera Masu neman sarautar kamar haka; Magajin Gari, Yarima, Iya, da kuma Turaki, duba da wasu Ka’idojin zurfin ilimin masu neman, gogewarsu da Jagorantar Al’umma, Aikin Gwamnati, Mu’amalarsu da Al’umma, Lambobin Girmamawar da suka samu a kasa, Koshin Lafiyarsu, da kuma yanayin zamantakewar su da Al’ummar da suke Jagoranta.


A daren Alhamis, Masu nadin sarautar sun gudanat da zaben nasu kamar yadda Gwamna ya basu Shawara. Sun gudanar da zaben nasu a Gaban Sakataran Gwamna, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinan ‘Yan Sanda, da sauransu. Sun bi Ka’idoji Masu tarin yawa wajen Gudanar da zaben. Mutane Uku daga cikin masu zaben sun zabi Iyan Zazzau, Turakin Zazzau ya samu kuri’a daya haka shima yariman Zazzau ya samu kuri’a daya.


Masu Zaben sun rubuta sakamakon nasu kuma zasu mikawa Gwamna (Nasir Elrufai) Karfe 11 na safiyar Juma’a 25 ga watan September, 2020. Ana saka ran Gwamna zai bawa Al’umma Bayani bayan sun gama ganawa da masu nadin sarautar

Ga mai bukatar kallon videon abunda ke gudana kai tsaye danna wanna bluen rubutun dake kasa

Drop Your Comment

0 Comments