Alamomin 12 Da Zaka Iya Fahimtan Mace Bata Sonka - TrustPosts
Trustposts - Best Entertainment Gists Portal & Unlimited Music, Video Download For Free...

Alamomin 12 Da Zaka Iya Fahimtan Mace Bata Sonka

 A duk lokacin da ka samu kanka a soyayya kai ke son mace ita bata yinka to kana cikin hatsari.


Babu soyayya mai wahalarwa da cutarwa irin soyayyar da mace bata sonka taki fitowa fili ta fadamaka, amma kuma ta bijiro da wasu kora da hali amma ka kasa fahimta.


Ga wasu alamonin da duk namijin da yaga mace tana nuna masa su, ko tamta babu wannan macen bata yinsa. Alamomin sune kamar haka:


1:Bazaka tabajin ko abakin makusantanta tana maganarka ba.

2: Da zaku shekara bata ganka ba bazata nemeka ba ko tayi cigiyarka.

3: Ba ako yaushe take daukar wayarka ba.

4: Bazata damu idan taga kiranka data bata kusa da wayan ta kiraka ba.

5: Baza maka reply na sakon text ba, baza kuma ta tura maka ba.

6: A duk lokacin da kuka hadu zata nuna maka tana cikin uzuri.

7: Idan kazo inda take bazata baka lokaci ba a gidansu kuma kullum tayi barci ne idan akace kaine kazo wajenta.

8: Bazata damu da abun hannunka ba idan kuma ta damu zata rika daura maka nauyin da bazaka iya dauka ba.

9: Zata rika yawan maganar abunda tasan baka so ko labarin wani datasan baku jituwa.

10: Bata la'akarin da halin da kake ciki na farin ciki ne ta tayaka ko na bakin ciki ne ta maka jaje.

11: Bata zaban irin kalaman da zata fadamaka, zata rika sako maka magana kai tsaye ba tare da la'akari ba.

12: Bata ganin mutunci ko darajar duk wani makusancinka.


Wadannan sune kadan daga cikin alamun da mace zata iya nuna maka muddin bata yinka. Da fata maza zasu fahomta sunemi mace ma kaunarsu tana so yana so ba yana so tanaki ba.

Drop Your Comment

0 Comments